Jerin Mutanen Da Buhari Ke Bukata Don Takarar 2019 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Jerin Mutanen Da Buhari Ke Bukata Don Takarar 2019

Published

on


Shugaban kasa a yanzu Muhammadu Buhari a yanzu ya shirya don tunkarar zaben kakar shekarar 2019, duk da cewar ya raba hanya da abokan sa tsofaffin janar-janar na soji kamar Cif Olusegun Obasanjo da TY Danjuma da sauran su da suka nuna adawar su karara akan sake takarar ta hana tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan dawo kan karagar sa.

Mafi yawancin wadanda suka taimakwa Buhari sun rabu da shi, sai dai APC ta samu nasarar samun wasu jigajigan ‘yan siya dake kasar nan akwai kuma wasu ‘yan hana ruwa gudu a yanzu a cikin APC, mafi yawancin su gwamnoni ne dake rike da madafun iko sai dai kuma dukkan ministoci kashi da yawa daga cikin su an sake nada su wakilai a (NWC) na jam’iyyar kuma har da wasu ‘ya yan PDP za su tsaya masa.

Bugu da kari, watakila Buhari abin da zai chazawa shi ne yadda zai janyo ra’ayi da kuma ci gaba da goyon bayan da yake samu daga wasumasu jan wuya dake cikin jam’iyyar APC maici ganin mahimmancin da suke dashi a wurin sa don ya samu kaiwa ga nasara. Irin wadannan mutanen sun san yadda ake shige da fice na siyasa kuma suna da kima a idonalumumomin dake yanku nan su, saboda haka za su jajirce don suga ya

koma kan karagar shi. Idan kuwa suka yake shi, a cikin sauki zai canza taku ta wajen komawa salon zaben 2011 a lokacin da ya samu zunzurutun kuri’u har miliya sha biyu, wanda ya cancanci ace ya yi namijin kokari amma da sauran aiki.

 

Bola Tinubu

Buhari da Tinubu sun dinke barakar su da ta auku ta lokacin yin hadakar jamiyyu a zaben 2015, inda hakan ya nuna a zahiri yadda Tinubu ya dinga yabawa Buhari a lokacin da Buhari ya kai ziyara jihar Legas a kwanan baya. Kafin nan, Buhari ya yi shelar neman kawo yafewa juna a lokacin da ya fifita Tinibu, inda yace Shugaban jam’iyyar na kasa Cif John Odigie-Oyegun wanda kuma shi ne yake jagorantar majalisar zartarwa ta APC dasu hakura da sake mai-maita mukaman su, inda Buhari ya umarci a gudanar da taro donsake zabar sababbin shugabannin jam’iyyar.

Ga dukkan alamuTinubu ya yi barci, inda ya bar ya yi sakacin da nauyin da Buhari ya dora masa na sasanta ‘yayan APC da suke ganin jam’iyyar bata yi masu daidai ba.

Dalilin da yasa Tinibu bai goyon bayan tazarce na shugabannin jam’iyyar kuma yana son shugabannin Oyegun ya sauka. Sai dai Buhari da mukarraban sa sun hango matsala na tafe, inda suka yi tunani akan nasarar zaben 2015 wanda a lokacin bai zo da sauki ba.

Fadar shugaban kasa ta shigo ciki ganin Tinubu ya amince zai kawo yanbkin Kudu maso Yamma don yin hadaka. Amma idan har tarihi ya mai-maita kansa, kuri’un yankin Kudu maso Yamma suka fada a cikin akwatin Buhari, cin zaben ba karamin aiki bane.

Masu fashin baki a harkar siyasa sun bayyana cewar dole ne Buhari yaci gaba da hadakar da aka yi, amma abinda ake jin tsoro shi ne, wasu daga cikin jigajigai har da wani sashe na gwamnonin APC suna ta kai gauro da mari don suga Oyegun ya sake yin tazarce da sauran a lokacin taron kasa na jamaiyyar da za’a gudanar. Haka idan taron bai yiwu ba, Gwamnan jihar Filato Simon Lalong wanda kuma shi ne yake jagorantar jagorantar wani kwamiti na APC a ranar 27 ga watan Fabirairu ya dauki matsa a karawa wakilan kwamitin gudanarwa na kasa na APC wa’adin shekara daya.

Sai dai dai wasu dakarun APC sun nuna damuwa akan hakan, domin in har suka dawo da waccan matsayar da aka cimma ta ranar 27 ga watan Fabirairu, Tinubu zai kara shiga cikin rudu, inda hakan zai zama babbar barazana ga APC a yankin Kudu maso Yamma. Yace, Tinubu ba wata makawa zai dakele dukkan wata barzana da Obasanjo zai kulla a yankin na Kudu maso Yamma, kuma indan aka yi dubi da karfin da ministocin da suka fito daga yankin suke dashi, ba zai yi daidai dana Tinibu ba wajen samarwa da Buhari kuri’u ba.

 

Bukola Saraki

Har yanzu Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki shi ne ke jan akalar siyasar jihar sa ta kuma yana samun goyon baya daga wasu jihohin dake Arewa ta tsakiya haka yana da dinbin magoya baya a Majalisar Dattawa kuma yana da magoya baya a tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP. Tabbas Saraki yana daya daga cikin mutanen da Buhari yake bukata don samu nasara yin gangamin a 2019.

A lokacin zaben 2015, Saraki ya zuba dukiyar sa don APC ta kaiga nasara da kuma yadda ya taka rawa wajen bizne tsohowar jam’iyyar sa PDP, musamman yadda ‘yayan PDP suka fice daga cikin ta har da Saraki suka kuma shinfida kinshikin samarwa da Buhari nasarar lashe zabe.

Saraki wanda tshon gwamanan jihar Kwara ne ya shigo gari ne a lokacin da ya dora gwamman jihar mai ci a yanzu Abdulfatah Ahmad akan karagar gwamanan jihar da kuma sauran jama’ar sa akan madafan iko.

Tunda daga ranar tara ga watan Yuni 2015, Bukola magajin siyar giudan mahaifin sa bai yi kasa a gwaiwa ba wajen yada karfin siyasar sa a jihar tta Kwara ba. Saraki dan kasa na uku yana kara samun baza komar sa duk da tuhumar da yake fuskanta a gaban kutun da’ar ma’aikata kuma yana da dimbin magoya baya a Majalisar Dattawa. Koda yake anyi ta yawo da sunan sa a matsayin wanda yake son shiga takarar kujerara shugaban kasa, sakamakon rikcin dake tsakanin Majalisar Dattwa da bangaren zartarwa kuma akwai rahotanni da suke cewa yana shirin fiewa daga APC.

Matukar har Saraki ya shiga yakin neman zaben Buhari, zai yi amfani da takwarorin sa da Majalisar da kuma goyon bayan da yake dashi a cikin APC da PDP don yiwa Buhari aiki.Kasar nan tana da guddumomi yanki guda109.

 

Dakta Rabiu Kwankwaso

Shi ne tsohon gwamnan jihar Kano kuma bai taba boye aniyar sa ta nemn shugabancin kasar nan ba, domin a zaben fidda gwani na jam’iyyar sa ta APC na 2014,yazo na biyu bayab Buhari sai stohon Mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yazo na uku da sauran su.

A yanzu haka, Kwankwaso yana da magoya baya a daukacin jihohi talatin da shida na kasar nan har da Abuja.

Yana ta shiga sako da lungu na kasar nan ta hanyar yin amfani da gidauniyar sa wajen yin kamfen, musamman kai ziyara a ida aka samu barkewar wata annoba da zuwa kai ziyara ga wadanda suke a tsare a gidajen kurku na kasar nan, inda yake ta sanya wa ana sako masu kanan laifuka.

Masu nazari akan harkar siyasa sun bayyana cewar Kwankwaso yana ci gaba da tattunawa da Obasanjo.

Ana kuma ta yada cewar Kwankwaso zai canza sheka zuwa sabuwar SDP da ta yi hadaka da jam’iyyar PRP, sai dai mukarraban sa sun karyata hakan. In ya marawa kudurin Buhari na sake tsayawa takara abin zai yi armashi sosai, musamman ganin irin karfin da yake dashi a jihar Kano.

 

Aisha Buhari

Don Buhari ya lashe zaben 2019, ba zai yi sake ya kunshe matar sa a dakin girki ko a dakin ta na aure ba. Ana sa ran Aisha zata yi dukkan mai yuwa wajen janyo ra’ayin mata sake zabar mijin ta kamart yadda ta yi a lokacin yakin neman zaben sa a 2015. Ga dukkan alamu tana da kyakwar alaka da matan gwamnoni, inda ta hanyar su zata samu damar janyo dimbin mata da za su sake zabar mijin nata karo na biyu. In har bata yi hakan ba kuwa, Buhari zai iya fuskantar tirniki akan sake takarar sa.

Idan aka yi la’akari da hirar kwanan baya da kafar BBC sashen ta yi da ida a cikin watan Okutobar 2016, ta yi barazanar cewar baza ta goyi bayan mijin nata ba a zaben 2019 ba in har bai yi canje-canje a majalisar zartarwar sa.

A cewar ta, “ har yanzu bai shaida mini ba cewar yana son ya sake tsawa takara ba, amma a matsayi na matar sa in har abubuwa basu daidaita ba har zuwa 2019 ba, ba zan sake rokon mata su zabe shi ba kamar yadda nayi a baya.

Sai dai, a wasu lokuta a baya Aisaha ana ganin kamar ta fara saukowa akan furucin nata na baya, inda a wasu tarurrukan dat ahalarta take yiwa majin nata yakin neman zabe a kai-kaice musamman mata.

 

Aminu Waziri

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yana daya daga cikin mutanen da Buharike bukata a kusa dashi, ganin cewar ya yi dan majalisa wakilai daga 2003 zuwa 2011, ya kuma zama kakakin majalisar inda ya shafe shekaru hudu a cikin nasara yana kan kujerara.

A lokacin da yake kan kujerar, ya yi amfani da damar yaja takwarorin sa a jiki, inda hakan ya samar masa sauki wajen yankar tikitin APC na tsayawa takarar gwamnan jihar Sokoto ya kuma lashe zaben a 2015.saboda karfin da yake dashi a tsakanin takwarorin sa ‘yan Majalisar.

Tambuwal samu jan ra’ayin su don Yakubu Dogara ya gaje shi. Kafin ya yanki tikitin nema zama gwamna, ya so ya tsaya nean takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar sa ta APC. Wata majiya kusa da Tambuwal ta bayyana cewar ga alamun sa har zuwa yau, yana da burin shugabantar kasar nan inda wasu suke kira don cewar zai iya fcewa daga APC zuwa wata jam’iyyar mai yuwa PDP don ya cimma burin sa.

Sai dai, har yanzu Tambuwal bai bayyna marawa sake tsayawa takarar Buhari baya ba, musamman saboda dimbin goyon bayan da yake dashi a wurin ‘yan Majalisar Wakilai da kuma sauran gwamnoni takwarorin sa. Amma ana da yakinin cewar Buhari yana mutukar bukatar Tambuwa don ya lashe zaben a 2019, bugu da kari Tambuwal yana ta kokarin kare dangantar dake tsakanin sa da wanda ya gaji tsohon gwamanan jihar kuma Sanata mai ci Aliyu Wammako.

Wata majiya ta bayyana cewar, karfin su zai iya kawo Buhari nakasa in har suka share shi.

 

Dabe Umahi

Umahi dan shekara 54 ya taba rike mukamin Mataimakin gwamna na tsohon gwaman Martin Elechi daga 2011 zuwa 2015, kafin ya kuma zama gwamanan jihar Ebonyi duk da uban gidan na sa bai so hakan ba a karkashin jam’iyyar PDP. Tun lokacin da ya dare karagar ta gwamna, Umahi bai boye son da yake yiwa Buhari ba duk da cewar yana cikin jam’iyyar adawa ne.

A bisa maganar gaskiya, a shekarar data wuce, Umahi ya nuna goyon bayan sag a Buhari in har Buharin zai sake tsayawa takara a 2019. Samun mutum kamar Umahi a yankin Kudu Gabas takarar sake tsayawar takarar Buhari zata bayar da mamaki sosai.

Masu fashin baki sun bayyana cewar ministoci da suka fito daga yankin suma suna goyon bayan Buhari kuma abinda Buhari yake bukata shi ne ya kara nuna soyayyar sa ga wadan da suke tare dashi daga yankin.

A jawabin sa a lokacin da wata tawaga da suka suka fito daga yankin Ohaozara da suka fito daga mazabun Onicha da Ibo ta tarayya suyka kai masa ziyarar shiga sabuwar shekara a karamar hukumar Ohaozara,a shekarar data wuce, Umahi ya bayyana cewar, tuni Buhari ya riga ya samu goyon baya a jihar da PDP ke shugabanta.

 

Yakubu Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya saboda wannan kujerer da yake rike da ita, shima wani jigo ne da baza’a yi sakaci dashi ba, idan anamaganar shige da fice irin ta siyasa.

Duk da adawar da yake fuskanta daga wurin ‘yayan jam’iyyar sa APC, Dogara saida ya zama Shugaban Majalisar a ranar tara ga watan Yunin 2015, inda aka yi matukar fafatawa a lokacin da aka gudanar da zaben kujerar.

Amma tun daga wancan lokacin, yana ta tafiyar da kansa kamar wanda ake nuna masa wariya a cikin APC duk da cewar kamar yana daya daga na kusan Buhari.

Kamar wanda Dogara ya gada a matsayin shuganban Majalisar shima tsohon dan jamiyar PDP ne kuma saboda wayiyar da ake nuna masa a APC, ana rade radin yana jiran lokaci ne kawai don canza sheka zuwa wata jam’iyyar kilan PDP.

Dogara har yanzu dai bai nuna alkiblar inda ya dosa ba kuma bai nuna yana goyon bayan sake takarar Buhari ba. Baya ga juya akalar siyar mazabar sa ta Bogoro, Dass, Tafawa Balewa dake cikin jiharBauchi, yana kuma da karfi sosai wajen jan hankalin sauran takwarorin sa su 259 dasuka fito daga mazabun dake kasar nan ganin cewar shi ne yake jan ragamar daukacin ‘yan Majalisar su 360. A kasancewar Dogara dan kasa na hudu yana daya daga cikin wadan da shugaba Buhari yake bukata.

 

Timipre Sylba:

Har yanzu shi ne shugaban APC a jihar sa Bayelsa, duk da ban-bancin ra’ayin siyasa dake tsakanin sa da tsohon gwamna, yana fuskantarbarazanar wajen zama wakili a kwamitin zartarwa na kasa na APC. Tabbas Buhari yana neman gayon bayan daga jihar ta Bayelsa mai arzikin mai.

Sai dai, Sylba mai yuwa ba zai kai labari ba akan bukatar sa ta son sake komawa kan kujerar sa ba ganin cewar Gwamna Seriake Dickson shi neyake rike da madafun ikon jihar. A zaben gwamna da aka gudanar a jihar mai dauke da rikitarwa, har yanzu Sylba yana da dimbin magoya baya a daukacin fadin jihar. Amma shirn sa da ya yi a kwanan baya akan gudanar da ayyukan jam’iyyar da maganar shuganacin ta ba wani abu bane.

Buhari ba zai iya kawar da kai akan Sylba ba domin yana matukar bukatar shi don samun kuri’u daga jihar Bayelsa wadda ta kasance jihar haiwa ta tsohon shugaban kasaJonathan.

Sylba siyasar sa tana da karfi a jihar Bayelsa a waje daya kuma akwai takun saka a tsakanin sa da Gwannan jihar Dickson, wanda Dickson yakeganin Sylba ba karamin barazana bane ga PDP a jihar ba. A watan Nuwamba shekarar data gabata, Sylba da sun yi chachar baki

wajen dora laifi akan rikicin siyasar da barke a tsakanin magoya bayan APC da PDP a cikin karamar hukumar Brass.

Koma dai menene ya faru, dole ne Buhari ya tabbatar da ya yi aiki da Sylba da sauran magoya bayan APC da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar dake Bayelsa in har Buhari yana son ya taka wata rawa a jihar da har yanzu ‘yan jihar suke girmama Goodluck Jonathan.

 

Cibiyar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Ta APC

An kafa ta ne kafin gudanar da zaben 2015, inda aka dauko dubban ‘yan sa kai. Mafi yawancin su sun sanya rai za’a yi tafiya dasu bayan an lashe zaben na 2015. Amma bayan shekaru uku, mafi yawancin suna jiran a tuna dasu.

A cewar wani daya daga cikin cibiyar Ibrahim Jirgi abin zata canza zani a zabeb 2019. Acewar sa, “bana jin cewar ko za su sake samun wani dan sa kai kamar yadda suka samu a 2015. Yace, koda yake wasu ‘yan sa kan an nada su a mukamai, amma gudunmawar da zaruwan ‘yan sa kan suka bayar a baya bamu gamzu ba. Mafi yawanci suna da korafe-korafe kuma wasu sun mutu kuma har zuwa yanzu sama da kashi sittin bisa dari da suka yiwa Buhari aiki har ya zama shugaban kasa, ba’a ja su ajiki ba.

 

Sanata Mohammed Danjuma Goje

Takwarorin na majalisar dattawa da magoya bayan sa suna yi masa lakabi da Sarkin Yakin Gombe. Goje mutum ne wanda ba wuya ya tara jama’a Goje wanda babban jigo ne a harkar siyar Gombe yada daya daga cikin ‘yan siyar da Buhari ke bukata don sake darewa karagar shugabancin kasar nan a 2019. Saraki kamar Goje ya taba yin gwamna a jihar Gombe na tsawon shekara takwas, inda kuma a yanzu yake zagayen sa na biyu a matsayin Sanata kuma ya taka rawa sosai a kungiyar tsofaffin gwamnoni.

An yi amannar cewar a zageyen shugabancin Goje na gwamnan Gobe, shi kadai tilo ya dora gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo wanda ya gaji kojerar ta gwamna da Goe ya sauka.

Ba kamar Saraki ba, Goje ba zai iya janyo Dankwambo zuwa APC ba domin a lojacin da Goje ya fice daga PDP ya fara takun saka daDankwambo, kuma anyi amanar cewar Dankwambo yana neman kujerar Buhari.

Goje yana da dimbin magoya baya a Gombe kuma yana samun goyon bayan alummar jihohin dake makwabtaka da Arewa maso Gabas. A ranar alhamis da ta gabata ya yi shelar cewar ‘yayan PDP da ke jihar Gombe sune kawai suka amfana daga shirin gwamnatin tarayya na kawo dauki akan fatara.

Goje ya shaida wa Maryam Uwais mai bai wa shugaban kasa shawara a shirin SIP, cewar, “kuna basu kudade don su yi karfi su yake mu.” Goje a matsayin sa shugaba na yankin Arewa masu Gabas dake majalisar dattawa kuma wakili na kungiyar tsofaffin gwamnoni zai karawa Buhari babban tagomshi a yankin Arewa masu Gabas in har Buhari yaja shi a jiki.

Yana da haibar da zai iya janyo ra’ayin takwarorin sa ‘yan majalisar a jiki don su yi wa Buhari aiki. Sai dai, a yanzu jita-jitar da ake yadawa itace, mafi yawancin wakilan kungiyar ta tsofaffin gwamnoni za su buge ne zaman gidan Yari in har Buhari ya lashe zaben karo na biyu. Dole ne Buhari ya ja su a jiki akan cewar su daina wannan tunanin.

Advertisement
Click to comment

labarai