Matar Alkalin Wasan Da Ya Busa Wasan Real Madrid Da Jubentus Tana Fuskantar Barazana — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Matar Alkalin Wasan Da Ya Busa Wasan Real Madrid Da Jubentus Tana Fuskantar Barazana

Published

on


‘Yan sanda a Ingila suna gudanar da bicike kan sakonnin waya na barazana da cin zarafi da ake aika wa matar alkalin wasan gasar firimiya wanda ya yi alkalancin wasan kofin Zakarun Turai tsakanin Real Madrid da Jubentus Michael Oliber.

Oliber ya ba wa Real Madrid fanareti ana dab da tashi daga wasan, abin da ya ba ta damar fitar da Jubentus daga gasar ranar Larabar data gabata.

Hukuncin ya sa mai tsaron ragar Jubentus kuma kyaftin Gianluigi Buffon ya soki alkalin wasan, lamarin da ya sa ya bawa golan jan kati a lokacin.

Haka kuma wasu kafafen watsa labarai na kasar Italiya su ma sun yi ta suka ga alkalin wasan inda suka bayyana shi a matsayin wanda bai san aikinsa ba.

An sanya lambar wayar matar Oliber mai suna Lucy wadda take alkalancin wasa a babbar gasar kwallon kafa ta mata ta Ingila, (Women’s Super League), wadda kuma take alkalancin a wasannin maza wadanda ba na gasar lig ba, a shafukan sada zumunta da muhawara (zumhawara), bayan wasan na Real Madrid da Jubentus, abin da ya sa aka yi ta aika mata da sakonnin zagi.

Kungiyar manyan alkalan wasa, PGMOL, ta ce tana bayar da goyon bayanta ga lafirin da matarsa, ta kuma yi alla-wadai da cin zarafin da ake wa Lucy a shafukan sada zumunta da muhawara.

A wasan na Bernabeu a birnin Madrid alkalin wasa Oliber ya kori kyaftin din Jubentus kuma mai tsaron raga Buffon saboda sukar da ya yi masa a kan fanaretin da ya bayar a minti na 93.

Bayan wasan ya gaya wa manema labarai cewa alkalin wasan dan kasar Ingila yana da jakar shara ne a matsayin zuciya; ma’ana ba shi da kan gado, bai san abin da yake yi ba, sakarai ne.

A ranar Asabar Buffon ya ce yana nan a kan bakansa na wadannan kalamai da ya yi gaba daya kuma baya nadamar hakan.

Golan mai shekara 40 ya yarda cewa wasu daga cikin kalmomin da ya yi amfani da su, sun yi tsauri, amma duk da haka ya ce lafirin mai shekara 33 ya yi kankanta a ce ya yi alkalancin wasa mai wannan muhimmanci.

A wata hira da gidan talabijin na Italiya, Buffon ya ce: ‘’Dole ne na kare abokan wasana da magoya bayan kungiyarmu, ko da ta cikin fushi ne. Dole ne na yi haka, ko da kuwa hakan zai bata min suna.’’

Haka kuma ‘yan sanda na gudanar da bincike a kan rahotannin da ke cewa wasu mutanen ma suna zuwa suna buga kofar gidan lafirin da matar tasa, suna kwarara musu zagi ta akwatin sanya wasikarsu.

Yanzu dai ‘yan sanda sun tsayar da lambar wayar matar, ko da yake wasu magoya bayan wasan kwallon kafar suna zagin ta cin mutunci ta shafukanta na sada zumunta da muhawara.

Advertisement
Click to comment

labarai