NIPR Reshen Bauchi Ta Yi Sabbi Shugabanninta — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

NIPR Reshen Bauchi Ta Yi Sabbi Shugabanninta

Published

on


A ranar Asabar din nan ne, Cibiyar hulda da jama’a ta kasa reshen jihar Bauchi wato (Nigerian Institute of Public Relations), NIPR a takaice reshen jihar Bauchi ta gudanar da zaben sabin shugabanni da za su ci gaba da jan ragamar shugabancin kungiyar na tsawon wa’adin da kungiyar ke tafiya a kai.

Bayan fafata zaben, wakilinmu ya labarto mana cewar Alhaji Kabiru Ali Kobi, MNIPR shi ne aka zaba a matsayin sabon shugaban NIPR wanda kuma a da can baya shi ne mataimakin shugaban kungiyar, Alhaji Muhammad Rabiu Wada, MNIPR shi ne kuma aka zaba a matsayin mataimakin shugaba, wanda a da baya shi ne babban sakataren kungiyar.

Sauran zababbun su ne, Mr. John Ogbole, ANIPR a matsayin Sakataren NIPR, Alhaji Aminu Yusuf Ibrahim Bambiyo, ANPR mukaddashin sakataren kungiya, ita kuma Hajiya Aisha Idris Bamai, ANIPR aka zabeta a matsayin ma’aji.

Hajiya Adama Ibrahim, ANIPR ita kuma aka zabeta a matsayin sakatariyar kudi, a yayin da kuma Mal. Bashir Sambo, ANIPR mai binciken kudade, kama daga shigowarsu, kashesu, fitar da su da kuma me aka yi da su na kungiyar.

A yayin da kuma Malam Hassan Alhaji Hassan, MNIPR ya kasance a matsayin (Ed-Officio).

Da yake jawabi a wajen amsar sabon shugabancin NIPR, sabon shugaban Alhaji Kabiru Ali Kobi, ya sha alwashin yin duk mai iyuwa domin ciyar da kungiyar gaba, ya kuma bayyana aniyarsa ta daurawa daga inda tsoffin shugabanni suka tsaya.

Kobi ya bukaci goyon bayan mambobi da sauran tsoffin shugabanni kungiyar domin gudanar da aiyuka kafa-kafa domin ciyar da wannan kungiyar ta cibiyar hulda da jama’a ta kasa gaba.

Sannan kuma ya nemi kawo wasu hanyoyin da za su daukaka cibiyar da samar da sabbin hanyoyin da za su kai ga taimaka wa jama’an jiha, kasa da sauransu ta wannan cibiyar wanda mafiya yawa kwararrun kuma gogaggun ‘yan jarida ne ke mata kawanya.

NIPR dai mafiya yawan mambobinta kwararru ne a sashin aikin jarida da kuma hulda da jama’a a bangarori daban-daban. Tuni sabbin shugabanni suka kama aikinsu gadan-gadan domin kai cibiyar mataki na gaba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!