Sabuwar Takaddama Ta Barke Kan Janye Sojoji A Jihar Taraba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sabuwar Takaddama Ta Barke Kan Janye Sojoji A Jihar Taraba

Published

on


Gwamnatin jihar Taraba ta bayyana kaduwa a kan gaggawar janye sojoji da ke aikin samar da zaman lafiya a jihar da aka yi a fadin jihar.

A sanarwa da jami’in watsa labaran gwamnan jihar Darius Ishaku, Bala Dan-Abu, ya rabawa maneman labarai rana Asabar, ya yi korafin janye sojojin ba tare da wani sanarwa ba daga fage da suke gudanar da aiyukan samar da zaman lafiya..

“Abin mamakin shi ne har yanzu babu wani dalilin da aka bayar na janye sojojin kuma a gwamnatante har yanzu bamu da wani labarin yin haka”

“A halin yanzu bamu da wani dalilin day a sa aka janye sojojin” inji sanarwar.

Haka kuma shugabankaramar hukumar Donga, Nashuka Ipeyen ya bayyana wa maneman labarai a wata tataunawa da suka yi das hi ranar Asabar cewa, an fara janye sojojin ne daga wuraren dake fama da rikice rikice tun misalign karfe10 nasafen ranar Asabar.

Mista Ipeyen ya kara da cewa, lokacin daya samu wannan labarin nan take ya tuntunbi Kwamandan sojojin na 93 Battalion  dake Takum,  Ibrahim Gambari inda ya yi bayanin cewar shi ne da kansa ya bayar da umurnin janye sojojin.

“Na yi masa kukan janye sojojijn da a ka yi saboda mun samu bayanin lalai za a kawo wa wasu kauyaku hari, sai y ace, shi ba zai iya daukar kasada da rayuwar sojojinsa ba”

“Kwamdan y ace ba zasu mayar da sojojin ba har sai gwamnatin jiar ta dauki alkawarin daular nauyin duk wani soja da a ka kashe ko a ka ji wa ciwo a fadin jihar”

“Ban san dalilin da gwamnatin zata dauki wanna alkawarin bat un da a kullum fare ren huka ake kashe wa”.

“Amma tuni muka yi wani shiri na gagawa da kwamishinan ‘yan sanda in da ya turo mota 3 na ‘yansanda domin bayar da tsaro”

Jami’in watsa labarai na rundunar sojoji na Yola, Kamarudeen Adegoke, ya karyata zargin an janye sojojin ya ce ba a janye wani soja ba daga kananan hukumomin. “Dukkan mutane mu na wuraren aikinsu, ban san daga inda gwamnatin ta samu labarin janye sojojin ba, amma ina mai tabbatar muku da cewa, mutanenmu na nan a wuraren aikinsu ba gudu ba ja da baya” inji shi.

Advertisement
Click to comment

labarai