An Koya Wa Marayu 50 Gyaran Babur A Zariya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Koya Wa Marayu 50 Gyaran Babur A Zariya

Published

on


A ranar Lahadin da ta gabata, kungiyar ma su gyaran babur na karamar hukumar Zariya,’’ZAZZAU MOTORCYLE MECHANIC ASSOCIATION’’ wanda ake kira [ZAMMA], ta jagoranci yaye wasu matasa su hamsin da wannan kungiya ta zakulo su, ta kuma koya ma su sana’ar gyaran babur, domin su sami sana’ar da za su dogara da ita, mai-makon watan-gaririya a tituna.

A sakonsa wajen taron, mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, ya nuna matukar jin dadinsa na yadda shugabannin wannan kungiya suka yi hangen-nesa, inda suka tattara marayu guda hamsin suka koya ma su sana’ar gyaran Babura.

Mai martaba Sarkin Zazzau, da Ji-Sambon Zazzau Alhaji Sani Sambo ya wakilta, ya kuma tabbatarwa shugabannin wannan kungiya, zai ci gaba da ba su duk gudunmuwar da suke bukata, domin su sami saukin aiwatar da ayyukan da suka saw a gaba, na samar da sana’o’in dogaro da kai ga matasa, musamman ma dai marayu da wannan kungiya ta tallafa wa rayuwarsu a wannan rana.

Farofesa Muhammad Shafi’u Abdullahi, Wakilin Makarantan Zazzau, wanda kuma ya kasance shugaban wannan taro, ya nanata furucin da mai martaba sarkin Zazzau ya yi, na yaba wa shugabannin wannan kungiya,na yadda suke bakin kokarinsu, na ganin sun tallafa wa rayuwar matasa da suke karamar hukumar Zariya.

Da kuma wakilin makarantan Zazzau ya juya ga matasan da aka koyar da su wannan sana’a, sai ya bukace su da su tabbatr sun rungumi wannan sana’a da hannu biyu, domin rayuwarsu ta inganta fiye da yadda ta ke a yau.

Shi ko Sarkin Ayyukan Zazzau, Malam Abbas Muhammad Fagaci, bayan shi ma ya yaba wa shugabannin kungiya na yadda suke tallafa wa rayuwar matasa a karamar hukumar Zariya, sai Sarkin Ayyukan Zazzau, ya nuna matukar damuwarsa na yadda daukacin ‘yan siyasa da suke madafun iko da aka ba su goron gayyar wannan taro, babu wanda ya je wajen wannan taro.

Kamar yadda Sarkin Ayyukan Zazzau ya ce, wannan hali da ‘yan siyasa ke yi, babban kuskure ne, musamman in sun tuna, al’ummar da suka yi amfani da lokacinsu ne suka zabe su, suka kai ga biyan bukata, amma sai suka kasa mayar da zanen goyon da aka yi ma su.

Kazalika Garkuwan kudun Zazzau, Dokta Muhammad Sani Uwaisu, kira ya yi ga gwamnatin jihar Kaduna da kuma sauran gwamnatoci da su kara tashi tsaye, na ganin sun rubanya tallafin da suke ba kungiyoyin da al’umma suka kafa domin tallafa wa junansu da kuma matasan da ya  kamata  a ce gwamnatoci ne aiwatar da tsare-tsare domin inganta rayuwaru a bangaren ilimi da kuma sana’ar dogaro da kai.

Da kuma ya juya ga iyayen yara, sai Garkuwan kudun Zazzau ya nuna matukar damuwarsa na yadda iyaye maza ba su damu su kai yaransu wuraren koyon sana’o’I ba, sai dai iyayensu mata, ya ce, lokaci ya yi da iyaye maza za su canza daga tunanin sauke nauyin da Allah ya dora ma sun a kula da tarbiyya da kuma ilimin yaransu.

Tun farko a jawabinsa, shugaban kungiyar, Alhaji Jibrin Kasim (OZEEZ) wanda mataimakinsa Malam Ibrahim Jibrin ya wakilce shi, y ace sun kafa wannan kungiya a shekara ta 2016, wanda zuwa yanzu, sun koya wa yara fiye da 160 wannan sana’a ta gyaran babur, daukacin yaran a cewar shugaban, sun fito ne daga sasan karamar  hukumar Zariya. Sauran wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da Garkuwan Ayyukan Zazzau, Injiniya Balarabe Musa da Dokta Muhammad Sani Hassan da dai al’umma da yawan gaske da suka fi mayar da hankalinsu, wajen nuna jin dadinsu na yadda wannan kungiya ta tashi tsaye na ganin sun inganta rayuwar matasa da suke karamar hukumar Zariya, sai suka yi alkawarin ci gaba dab a wannan kungiya duk goyon bayan da suka kamata, domin su cimma burinsu na tallafa wa matasa da kuma marayu da suke karamar hukumar Zariya.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!