Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Budurwa Ta Kashe Mahaifinta Saboda Ya Hana Ta Auri Masoyinta

Published

on

Wata ‘yar shekara sha shida mai suna Emani Kure ta aikata aika-aika sakamakon hallaka mahaifinta har lahira.

Emani Kure wadda take da zama da iyayen a kauyen  Karaban dake yankin Bwari a garin  Abuja ta kashe mahaifin nata dan shekara 40 mai suna Kusha Kure,inda ‘yan sanda suka tabbatar da cewar, lamarin ya auku ne a ranar Lahadin data gabata da misalin karfe uku na dare.

Yarinyar ta hallaka mahaifin nata ne saboda yaki amincewa bukatar ta na auren wani saurayin ta mai suna  Nasiru Musa.

Emani da masoyin nata Nasiru Musa, sun shafe kimanin shekaru biyu suna soyayayya sun bayyana ra’ayin su na son yin aure.

Kwamishinan rundunar ‘yan sanda na Abuja  Sadik Bello ya bayyana cewar, an kawo  rahoton lamarin  ga ofishin ‘yan sanda na gudumar Bwari.

Ya ci gaba da cewa, jami’an sa masu na sashen binciken kisan kai, sun cafko  Emanu tare da mahaifiyar ta mai suna Asabe Kure, wadda ake zargin ta taka muhimmiyar rawa wajen kashe mijin nata.

Ya kara da cewa daga baya an mayar da binciken ga sashen binciken kisan kai dake rundunar.

A hirar da manema labarai suka yi da wadda ake zargi  Emani, ta yi bayani mai girgizarwa akan yadda ta sheka da mahaifin nata barzahu.

Emani ta ce, “na kashe mahaifi na saboda yaki amincewa in auri masoyi na Nasiru Musa.”

Acewar ta, “ mun sahfe shekaru biyu muna soyayya, kuma mahaifi na ya sha jibga ta a lokuta da yawa akan in janye ra’ayi na son auren Nasiru”.

Emani ta kara da cewa, na kashe shine da misalain karfe uku na dare kuma mahaifiya ta ce ta bani wannan shawarar a lokacin da muke kwance a harabar gidan mu, cewar in shiga daki, inda mahaifi na ke yin barci in kashe shi.

Ta umarce in yi amfani da adda don in hallaka shi, inda naje inda yake ajiya addar sa na dauko naje dakin sa na kashe shi.

Ta ce, “na sassare shi a wuyan sa,bayan da mahaifiya ta rike mini kafar sa.”

A cewar ta, “bayan na kashe shi, na gudu daga gidan mu zuwa gidan kawa ta mai suna Regina.

Ta ce, Nasiru bai da masaniyyar ina son in kashe mahaifin nawa, kuma shi ma ya kidime a lokacin da ya samu labarain abinda na aikata.”

A na ta bangaren, mahaifiyar ‘yar shekara talatin da biyar ta karya zargin da ‘yarta ta dora mata.

Asabe ta ce,”nida majina marigayi bama goyon bayan  Emani akan son da take na auren Nasiru Musa, amma tayi biris da jan kunnen da muka yi mata” .

A cewar ta, a lokacin mijina yana barci a daki kuma ‘yar karamar yata da nake goyo ta tashi ta fara kuka na tashi don in bata Nono tasha, sai kawai naji mijina yana ihu a cikin dakin sa, inda nayi gaggawa na kirawo siriki na mahaifin mijina.

Shi da sauran jama’a suka shigo gidan mu suka iske mijina a cikin jini, kuma yata bata wurin, domin ta gudu.

Acewar ta, na fara zargin ta da Nasiru Musa a zaman wadanda suka aikata ta’asar.

Ta ce, munje ofishin “yan sanda na gudunduma dake  Bwari don kai rahoton akuwar lamarin, inda na sheda masu cewar, ina zargin ‘yata da saurin ta akan aikata ta’asar, inda daga baya ‘yan sanda suka cafko Nasiru da ‘yata kuma ta amsa laifin ta, amma ta ce wai nice na umarce ta kashe mijin nawa.

Nasiru dan shekara ashirin da biyu, ana zaegin sa da hkda baki don kashe Kure.

Nasiru ya ce bai san cewar Emani ta kitsa son kashe mahaifin ta ba.

Har yanzu wadanda ake zargin Emani da mahaifiyar ta da kuma Nasiru suna tsare ana gudanar da bincike akan lamarain.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: