Sanata Hunkuyi Ya Kai Tallafin Tiransifoma Kauyen Sabon Birnin Bomo — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Sanata Hunkuyi Ya Kai Tallafin Tiransifoma Kauyen Sabon Birnin Bomo

Published

on


A cikin makon daya gabata ne kungiyar ci gaban anguwar Sabon Garin Bomo dake a karamar hukumar Sabin Garia jihar Kaduna suka samu tallafin Tiransifoma daga Sanata Sulaiman Hunkuyi, sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar datijjai.

Alhaji Isa Sa’eed Madaki shi ne shugaban kungiyar ci gaban wannan unguwa ya kuma bayyana wa wakilinmu irin dadin da suka ji har ya kara da cewa, kungiyar tasu ta jima tana neman gudummawa wajan manyan ‘yan siyasan da suke dasu amma basu yi nasara ba amma gashi sun mun shaida da kokarin Sanata Suleiman Hunkuyi domin shi ya yi mana alkawari kuma gashi ya cika don haka muna fatan Allah yasa sauran ‘yan siyasan zasu yi koyi da halinsa. wajen taimakon jama’ar su , kuma shuganan ya nuna farin cikin sa a madadin sauran jama’ar unguwar Sabon Garin Bomo ya ce, da fatan za a samu wasu da zasu dauke sauran aikin daya rage daya hada da sayan turakun wutar da fatan Allah ya bashi Sanata sa’an abin daya sanya a gabansa na taimakon mutanen sa.

Isma’il A. Bashir shi ne shugaban matasan unguwar na Sabon Garin Bomo a nasa bayanin cewa ya yi wajibin sune su godewa mai girma Sanata Suleiman Hunkuyi don ya cancanci yabo domin ya yi mana Alkawari kuma ya cika don haka suma zasu saka masa da yardan Allah in lokaci ya yi, shugaban matasan ya kara ne da kara kira ga sauran wakilansu da suma suyi musu irin wancan gudummawar da su taimaka masu da sauran kayan da suka rage ba a sayoba kamar turakun da za a dauko wutar zuwa cikin anguwar ya yi godiya ga Sanata tare da fatan Allah ya saka masa da alkairi mai yawa.

Malam Yusuf Adam shi ne mai Anguwar na Sabon Garin Bomo shi ma ya yi godiya ne ga sanata Suleman Hunkuyi  da kama kungiyar ci gaban unguwar bisa yadda suka nuna kauna da tsare mutunci da tunanin kawo ci gaban wannanuanguwa ya ce, da ’yan siyasa zasu rika cika alkawari kamar yadda Sanata  Suleiman, ya cika to da an sami canjin rayuwa a aasarmu baki daya.

Shin ko menene ya janyo wannan hangen nesa da Sanata Suleiman ya yi na mika tallafin taransifoma ga wacan anguwar? Tambayar da wakilinmu ya yi wa babban sakataren  a ofishin Sanatan dake MTD Zariya wato Malam Suleman inda ya ce “A gaskiya Sanata Suleiman Hunkuyi burinsa shi ne  duk inda ya yi alkawari fatansa ya cika kuma in Allah ya so dukk inda suka san Sanata ya yi musu alkawari to suci gaba da addu’a da yardar Allah zai cika shi kuma shi ma Sanata ya nuna godiya bisa godiya da addu’ar da jama’ar shiyya ta daya ke masa a duk rana.

Ya zuwa hada wannan labari tuni mazuna wannan unguwa suka shirya walima ta musamman bisa sa rai da sukayi na sun kusa fita daga wahalar zama a cikin duhu da komowa cikin haske kamar yadda sauran jama’ar wasu unguwanni ke zama a cikin haske da shan ruwan sanyi da nika da surfe cikin sauki.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!