Connect with us

MANYAN LABARAI

Tsaro Ne Ke Gabana Ba Zaben 2019 Ba –Buhari

Published

on

A wata ganawar aiki da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi da Firayiministar Birtaniya, Theresa May jiya a Birnin Landan, Shugaban ya bayyana abubuwan da ke gabansa fiye da zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Abubuwa biyu ne shugaban ya zayyana a matsayin wadanda su ne a gabansa; harkar inganta tsaro da kuma batun tattalin arzikin kasa.

Shugaba Buhari ya ce; “Mun yi yakin zabe ne da zimmar tabbatar da muhimman abubuwa uku, tabbatar da tsaro a kasar, habbakawa da farfado da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

“Za a gudanar da wani babban zaben kasa a shekara mai zuwa, tuni ‘yan siyasa sun wasa wukakensu kan wannan zaben, ni kuma babban abin da ke gabana shi ne tabbatar da tsaro da farfado da tattalin arzikin kasa.” Inji Shugaban

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shaidawa Firayiministar cewa, Nijeriya da Birtaniya sun jima da kyakkyawar alaka a tsakanin kasashen biyu.

Sannan kuma Shugaban ya yaba wa kamfanonin Kasar Birtaniya irinsu Unileber, Cadbury, da dai sauransu wadanda suke matukar taimakawa Nijeriya hatta a lokutan yakin basasa.

Daga karshe Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Firayiminista Theresa May karin haske dangane da irin nasarorin da aka samu a fannin noma, lamarin da ya tseratar da Nijeriya daga annobar yunwa.

A yayin da take tofa albarkacin bakinta, Firayiministar Birtaniya, Theresa May ta jaddada cewa, za su ci gaba da yin aiki kafada da kafada da Nijeriya, musamman wurin horaswa da bayar da kayan aiki ga sojojin Nijeriya.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!