An Tsinci Sandar Majalisar Dattawa A Hanyar Maraba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Tsinci Sandar Majalisar Dattawa A Hanyar Maraba

Published

on


Daga  Khalid Idris Doya, Abuja

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta samu nasarar kubuto da sandar iko ta Majalisar Dattaban Nijeriya wacce wasu da ba a san ko suwaye ba suka kutsa majalisar gami da sacewa a sa’ilin da majalisar take tsaka da gudanar da zamanta a ranar Laraba, wadanda ake zargin da sace sandar ikon sun kai mutane biyar.

Mukaddashin babban jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Nijeiya Sifiritanda Aremu Adeniran shi ne ya shaida hakan a cikin sanarwar manema labaru da ya aiko mana da sanyin safiyar jiya Alhamis, ya ce sun samu nasarar kobutar da sandar ikon ce a karkashin wata gada da ke mashigar Abuja.

SP Aremu ya bayyana cewar, aukuwar satar sandar ikon ke da wuya ne kuma shugaban rundunar ‘yan sandan kasar nan, (IGP) Ibrahim Idris ya bayar da dukkanin umurni gami da karfin iko ga sashin kwararru na rundunar da ke karkashin sashin bibiya na IGP, domin su samu nasarar kwato sandar cikin gaggaawa.

Aremu Adeniran ya kuma shaida wa manema labarai cewa, shi shugabansu na ‘yan sandan Idris ya kuma bayar da umurnin a tsaurara dukkanin tsaro a lunguna da sakon cikin Abuja gami da sanya shingayen bincike ta kowane yanki na cikin babban birnin tarayya Abuja, domin tabbatar da bincikar kowace mota hade da tabbatar da dawo da sandar ikon majalisar da kuma taso keyyar wadanda suka sace sandar, idan halin hakan ya bayar (sai dai hakan bai samu ba har lokacin kammala rahotan nan).

Ya ci gaba da cewar sashin rundunar na musamman masu aikin bibiya, sun himmatu ka’in-da-na’in wajen tabbatar da tsaurara tsaro da kuma binciken dukkanin abun da suka gani ko suke tsammanin sandar tana wajen domin a samu nasarar kwatota daga hanun wadanda suka yi awon gaba da ita.

Ya bayyana cewar sandar sun samo ta ne a gefen hanya gabanin karasawa zuwa ga kofar mashigar Abuja, inda wasu masu wucewa suka hangota hade da sanar wa rundunar ‘yan sandan.

Ya kuma shaida cewar har zuwa yanzu bincikensu kan wannan lamarin na ci gaba da gudanuwa domin tabbatar da cewar an sankamo masu laifi kan lamarin domin kai su ga zuwa gaban shari’a domin fuskantar laifukansu.

Mai magana da yawun rundunar ya nuna matukar godiyar rundunar ‘yan sandan ga jama’a da suka yi ta taimaka masu da bayanai da kuma sanar musu da dukkanin motsin da suka gano domin a samu nasarar.

Ya nuna gayar farin cikinsu ga masu motocin haya da na hawa da suke Abuja a bisa taimako da hadin kai da suka bayar wajen binciken wannan sandar wacce har aka kai ga samun nasarar dawo da ita hanu mai kyau.

Ya bayyana cewar har a gobe dai aikin ‘yan sanda ne tabbatar da kare lafiya da dukiyar ‘yan kasa, yana mai bayyana cewar za su kuma ci gaba da kara himma a wannan fannin domin ci gaba da bayar da tsaro a gasar nan.

Wakilinmu ya labarto cewar sai dai rundunar ta ‘yan sanda har zuwa yanzu ba su sanar da cewar sun kama ko da mutum guda daga cikin wadanda ake zargi da sace sandar ba, ba a kuma bayyana wa duniya dalilinsu na wannan satar ba.

Advertisement
Click to comment

labarai