Matsalar Cin Hanci Da Lalata ‘Yan Mata Kan Cin Jarabawa A Makarantu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Matsalar Cin Hanci Da Lalata ‘Yan Mata Kan Cin Jarabawa A Makarantu

Published

on


Sati biyu da suka gabata, kafafen yada labarai na yanar gizo sun cika da batutuwa kan wani abin assha na magana da kuma na faifan bidiyo da ya bayyana, inda aka ji aka kuma ga wani Farfesa na Jami’ar, Obafemi Awolowo, (OAU), da ke Ile-Ife, yana bukatar wata daliba da ta amince ma shi ya yi lalata da ita, domin ya taimaka mata ta cinye jarabawarta. Kamar dai yadda aka zata ne, wannan abin asshan da ya bayyana tabbas zai janyo cece-kuce mai yawa da kuma fusata da nu na kin yarda gami da yin tir daga al’umman Nijeriya.

Wasu daga cikin mutanan da suka mayar da martani, sun yi suka ne kan yadda sau da yawa ake cin mutuncin matan ta hanyar neman yin lalata da su. Amma wannan lamarin da ya bayyana na kwanan nan ba shi ne farau ba. A watan Oktoba da ya shige, wani malamin na Jami’a mai karantarwa a Kwalejin Fasaha ta Ogoja, da ke Jihar Kros Riba, wanda yake kuma magidanci ne, hoton sa ya bayyana a faifan bidiyo inda yake neman yin lalata da dalibarsa da yake duba mata takardun ta na kammala karatun ta. Jami’an tsaro ne suka kama shi.

Hakanan an ma kama wani malamin na Jami’a, a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Auchi, tsirara tare da wata dalibarsa. Malamin sai ya yi zargin wai daman cinne ne aka yi ma shi. A wasu lokutan, lalaci da rashin mayar da himma gami da son cin banza na wasu dalibai matan ne ke sabbaba masu hakan. A shekarar 2005, Jami’ar Jihar Legas da ke Ojo, ta kori wani malaminta wanda aka kama daga shi sai dan kamfai, yana kokarin yin lalata da wata dalibar shi ‘yar aji biyu, a dakin Otel.

Batun yin lalata da dalibai mata a makarantu babu shakka abin kunya ne, kuma abin damuwa ne sosai, hakan kuma yakan saka shakku a takardun shaidar gama karatun da Jami’o’i ke bayarwa.

Muna tsoron wannan abin kunyan na zargin yin lalata da daliba mace domin ba ta nasarar cin jarabawa, wanda ya shafi Farfesa Richard Akindele, na sashen kididdiga da ke Jami’ar ta, OAU, da wata daliba wacce ba a ambaci sunanta ba, wanda tabbas ba shi ne na farko ba, wanda kuma bisa ga dukkanin alamu ba shi zai zama na karke ba. Domin gane dalilin hakan abu ne mai sauki.

Hakan na faruwa ne kasantuwan su kansu Jami’o’in ba wani abin a zo a gani da suke yi na ganin sun hana aukuwan hakan. Duk da cewa, a dokokin Jami’o’in aikata hakan babban laifi ne wanda ke da hukuncin sa na musamman, amma sam ba wasu matakan kirki da suka dauka kan shigen aikata hakan da aka yi a baya, da har zai tsoratar ga sake aikata hakan a gaba.

Kasantuwar rashin daukan wasu matakan hana aikata hakan ne da Jami’o’in ke yi, ga malaman Jami’o’in da suka aikata ko suka nemi su aikata yin lalata da dalibai matan, ko ma sun aikata din sun kuma ciyar da su nasarar jarabawowin. Hakan ya janyo rashin dogaro da mahukuntan na Jami’ao’in, inda ta kai wasu daliban sukan dauki doka a hannun su. Wasu malaman tabbas daliban sun yi masu cinne ko sun shirya masu shigo-shigo ba zurfi, daga baya suka kama su bayan sun yi masu tsirara suka kuma rika lakada masu dan Karen kashi.

Duk da shike ana iya cewa, yawanci hakan na faruwa ne bisa yadda zamani ya canza,inda ake ma matan kallon abin da za a yi lalata da su ne kawai aji dadi. Amma kuma a wasu lokutan yanda su kansu matan ke bayyanar da kansu yakan taimaka a nemi yin lalatan da su. Hakan shi ma abin Allah wadai ne. A nan LEADERSHIP JUMA’A, tana yaki da duk wata manufa ko aiki na cin mutuncin mata ta hanyar yin lalata da su, a ko’ina ne kuwa, kan tituna ne, a kasuwa ne, a makarantu ne ko a wuraren aiki ne.

Duk da yawanci an fi jin batun cin mutuncin matan ta hanyar neman da malamai maza ne ke yi wa dalibai mata a Jami’o’in, amma da wuya ka ji ana maganan dalibai matan da kan kokarin jan hankulan malamai mazan domin su yi lalata da su da gangan. Akwai kuma matsalar da dalibai maza kan baiwa malaman cin hanci domin su sami cin jarabawowin na su. Duk wadannan matsaloli ne da ya wajaba a lura da su a kuma nemo hanyar magance aukuwan su.

A ra’ayinmu, muna ganin da yawa ko ma duk wadannan matsalolin sun samo asali ne daga irin tarbiyan da mutum ya taso da ita. Wasu lokutan ma sam tarbiyan ce babu. Tarbiya mai kyau takan shirya ta kuma daidaita rayuwar mutane zuwa aikata abu mai kyau ne kadai.

Ya wajaba, iyaye su kula da irin tarbiyan da suke baiwa ‘ya’yayensu wacce ta dace da al’ada da kuma addinin su, su nu na ma ‘ya’yansu maza su daina ganin mata a matsayin ababen debe sha’awa idan sun girma.

Gazawan magance duk wadannan ababen asshan da ke yi mana kisan mummuke abin takaici ne. hakan yana nu ni da a sake duba tsarin makarantun namu ne, a kuma gyara da kore dukkanin halayen banza daga cibiyoyin ilimin namu.

Akwai dai gazawa wajen jagorancin makarantun namu. Malamai da yawa suna karantarwa ne ba tare da an duba cancantar su yadda ya kamata ba. Har sai gwamnati ta dauki matakai kan hakan na musamman, matukar ana son ganin magance matsalar da sauri.

Kwararru sun yi gargadin cewa, yin musayar bayar da cin hanci ko kuma amincewa da yin lalata domin cin jarabawa,aikin tir ne. Ya kuma wajaba dalibai su kara mayar da hankulansu wajen abin da suke karantawa, domin su gujewa malaman da kan yi amfani da gajiyawan na su, har su nemi yin lalatan da su.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!