’Yan Sanda Sun Kama Motoci Shake Da Makamai Za Su Taraba — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda Sun Kama Motoci Shake Da Makamai Za Su Taraba

Published

on


Daga Umar A Hunkuyi

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Ebonyi ta kama wasu motocin bas biyu shake da mutane masu dauke da bindigogi da harsasai.

‘Yan sandan sun kama motocin ne kusa da gadar Onu-Ebonyi da ke kan titin Abakaliki zuwa Ogoja, ta Karamar Hukumar Izzi, ta Jihar.

Sun kuma sami tufafin Sojoji a tare da su, wani wanda ya ga faruwar lamarin ya ce, ana tsammanin mutanan da aka kaman makiyaya ne.

Bayan kama sun ne, sai suke cewa, su masu shirya wasan kwakwayo ne na, ‘Nollywood,’ za su je Taraba ne domin daukan wani wasan Fim.

Tuni ‘yan sandan suka kai su shalkwatar ‘yan sandan Jihar a Abakaliki, domin ci gaba da yi masu tambayoyi. Sai dai ‘yan sandan sun bayar da rahotannin da suka saba da juna kan kamun.

Cikin sakon da Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Titus Lamorde, ya aika wa manema labarai ya musanta faruwar lamarin, amma Kakakin rundunar Jihar, Lobeth Odah, shi kuma ya tabbatar da kamun.

“Tabbas mun kama wasu mutane dauke da bindigogi da alabarusai za su Taraba, amma ba Fulani Makiyaya ne ba, masu wasan kwakwayo ne na Nollywood.

“Suna sanye da rigunan Sojoji, amma muna ci gaba da binciken lamarin. Da zaran mun kammala bincike zan sanar da ku abin da muka gano,” in ji ta.

Amma a sakon na Kwamishinan cewa ya yi, “Kai sam ba gaskiya ne ba.”

Babban mai baiwa Gwamna Dabe Umahi, shawara kan harkokin tsaron cikin gida, Kenneth Ugballa, cewa ya yi, yana nan yana bin diddigin maganar don ya san ainihin abin da ya faru.

“Tabbas na ji labarin, amma a yanzun haka ba ma ni a cikin Jihar, amma ina gab da shiga Jihar, da na isa Shalkwatar ‘yan sanda zan nufa kai tsaye don na ji gaskiyan abin da ya faru,” in ji shi.

Advertisement
Click to comment

labarai