Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Damke Mutumin Da Ake Zargi Da Yi Wa Diyarsa Ciki

Published

on

Daga Idris Aliyu Daudawa

Rundunar ‘yansandan jihar Lagos ta kama wani mutumi mai shekaru 50,mai suna Taiwo Oyelabi, saboda zargin shi da ake yi da yi ma ‘yarsa mai shekaru 21 ciki.

Kwamishinan ‘yansanda Mr Edgal Imohimi shi ne wanda ya bayyana haka, ga al’umma ranar 16 gawatan Afrilu lokacin da ya fito da Oyelabi, da sauran adanda suka aikata laifuka daban daban, a Hedikatar ‘yansanda ta jihar dake Ikeja.

Imohimi ya ce an bayyanaa rundunar ‘yansanda al’amarin, wadanda wasu mutane suka yi, ranar 16 ga watan Afrilu, cewar shi laifin anaikata shi ne a gida mai lamba 15 hanyar al’umma a Iyana- Iba cikin Igando.

‘’An fara shi al’amarin ne cikin watan Nuwamba 2017 lokacin da wata yarinyar dake zaune da kawunta, da koma gidan mahaifinta saboda ya nemi hakan.

‘’Tun daga wancan lokacin ne ya fara saduwa da ita, wanda a karshe a sakamakon al’amarin tsakanin, mahaifi da ‘yarsa, shi ne ciki ya fito.

‘’Bincike ya dangane da shi al’amarin ya nuna cewar shi wanda ake zargi da aikata laifin ,maigadi ne, amma kuma duk lokacin da zai tafi aiki sai ya je da ‘yarsa.’’

‘’Wannan bakon al’amari sai ya ja hankalin mutane, na unguwar wadanda suka kai ma ‘yansanda kukan nasu’’.

‘’Wannan al’amarin da shi mahaifin yarinyar ya aikata ba karamin laifi bane, kamar yadda Kamishinan ‘yansandan ya ce.

Shi ma da yake magana Oyelabi ya masa aikata laifin na saduwa da’yarsa, ya kuma shi ba halin shi bane, an jara’ayin shi ne.

Ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewar ‘yarsa tana da wasu Aljanu.

Ya kara jaddada cewar ‘’Ina zaune cikin daki lokacin da tazo ta rungume ni, ta fara sumbata ta’’.

‘’Na bugeta na kuma kai ta wata majami’a masu sa fararen kaya, can ne aka fada mani cewar tana da Aljanu’’.

‘’Abin ya faru wajen sau biyar ne, amma kafinin san abin da ake ciki, ashe tanada ciki wata uku.’’

‘’Wannan aikin Shedan ne saboda ni ban san yadda zan yi da abin da zata Haifa ba, bayan ta haihu’’.

Daga karshe Imohimi ya ce za a kai mutumin kotu, da zarar an kammala bincike.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: