Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Garkuwa: Rashin Zuwan Alkali Ya Hana Sauraron Karar Evans

Published

on

Daga Idris Aliyu Daudawa

A ci gaba da ake yi da shari’ar shahararren wanda ya kare da aikata laifin garkuwa da jama’a, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda ka fi sani da Evans, shari’ar da ke gaban mai shari’a Oluwatoyin Taiwo , wadda kuma kotun kan zauna ne a Ikeja. Jiya ba a ci gaba da ita shari’ar ba, saboda rashin zuwan shi Alkalin.

Kamar yadda wani jami’in kotun wanda bai so a ambaci sunan shi ba, ya ce ita mai shari’ar, tana  halartar wani taro ne da, babbanmai shari’a na jihar Lagos mai shari’a Opeyemi Oke.

An dage sauraren shri’ar har sai zuwa ranar 16 ga watan Yuni.

Gamnatin jihar Lagos tana son a yanke hukunci ne ma Evans, shi da Bictor Aduba, saboda aikata laifuka hudu, na aikata laifin garkuwa da mutane, da kuma mallakar makamai.

Ana kuma zargin su da garkuwa da Mr Sylvanus Ahamonu, suka tsare shi har na sati tarra, suka kuma amshi kudaden da suka kai dala 420,000 daga iyalan shi.

Zaman karshe wanda aka yi ranar 14 ga atan 14 ga watan Maris, faifan bidiyo ya nuna shi Evans din , ya amsa aikata laifuka da suka kunshi, garkuwa da jama’a, fashi da makami, ciki da kuma wajen Lagos, da aka nuna a kotu.

An dai nuna su faya fayen bidiwo da aka nuna lokacin da ake bada sheda, wanda Insifekta Idowu Haruna, wanda shi mamba ne na wata rundunar ‘yansandan ciki, masu kawo dauki.

Faya fayen bidiyon an nuna su a dakin zama na kotun yana saye da jar riga, ya zauna bisa wata kujera,yana bayani akan laifukan da ya aikata, yana tare ne da Haruna.

Za a iya ganin shi yana dariya yana fadawa ‘yansanda abubuwan da yake yi da rana, wadnda suka hada da, fashi da makami, tare da karguwa da mutane, inda yake amsar kudin fansa, da suka fara daga dala 250,000 zuwa milyan daya, da yake amsa, daga wurin wadanda suka fada komar shi.

An saurare shi yana bada cikakkun bayanai dangane da yadda iyalanshi suke, yadda ya gudu daga gida, ya fara aikata ayyukan ashsha a rayuwar shi.

Ebans yana fuskantar wasu shari’u biyu wadanda suma sun shafi, al’amarin daya shafi yin garkuwa da jama’a, a babbar kotun Lagos da ke Ikeja.

Ana dai zargin sune da aikata laifukan da suka shafi, kokarin yin garkuwa da Vincent Obianodo, wanda shi wani jami’i ne na, Kamfanonin motocin sufuri, na Young Shall Grow, ita ma  shari’ar tana gaban mai shari’a Oluwatoyin Taiwo. Yayin da ita kuma ita shari’ar aikata laifin kokarin kamawa da yin garkuwa da Mr Donatus Dunu, wani babban jami’i na Maydom Pharmacetucals tana gaban mai shari’a Hakeem Oshodi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: