Ya Kamata A Rufe Gidajen Man Da Ke Kan Iyakokinmu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Ya Kamata A Rufe Gidajen Man Da Ke Kan Iyakokinmu

Published

on


A

daidai lokacin da karancin man Fetur ya addabi kasarnan da kuma fitintunun da hakan ya haifar, mutane kadan ne suka yi kyashin mukamin Shugabancin kamfanin mai na kasa, NNPC,  wanda aka baiwa, Dakta Maikanti Baru, duk kuwa da morewar da ake tunanin akwai ta a cikin wannan mukamin. ‘Yan Nijeriya fatan su ita ce, su sami hanya mai sauki ta samun man na Fetur, don haka suke tsammanin wannan sabon shugaban da aka nadawa kamfanin man zai yi wata akara-dabara ne kawai, sai a ga komai ya yalwata. Don haka sai matsi ya yi yawa a kansa, kowa na jiran sa da ya fito ya yi bayanin inda matsalar take.

Ba wanda yake sha’awar jin wahalar da kamfanin ke sha wajen ganin ya wadatar da man a cikin kasa. Milyoyin lita ne na man ake sayowa daga waje a kullum, amma duk da hakan wahalar man ake yi, mafi yawa ta hanyar zagon kasa, ga wadanda suke son tsiyata tattalin arzikinmu domin biyan bukatun kansu. A kodayaushe, kamfanin na mai kokari yake na fahimtar da al’umma kan ainihin yadda matsalar take, kamar ta yadda wasu ke karkatar da man da kuma munanan ayyukan masu yin fasakwarin man.

Amma akwai matsala guda babba wacce take yin tarnaki a kan kokarin da kamfanin man ke yi na wadata kasa da albarkatun man na Fetur. Wannan matsala kuwa ita ce, ta yawaitan gidajen sayar da man na fetur a kan iyakokin kasarmu, wanda hakan ke kara taimakawa masu fasa kwarin man wajen karkatar da man namu zuwa kasashen makwabta, da nufin samun riba mai gwabi. Wasu na iya cewa, ai gina gidajen man a kan iyakoki hanya ce ta kasuwanci wanda kuma kila a ce ba ta da wata matsala.

Idan har da a ce, ana yin hakan da nufi ne na kwarai ba da manufar karya tattalin arzikinmu ba ta hanyar karkatar da albarkatun man namu zuwa kasashen makwabta, to da sai mu ce lallai hakan ba laifi ne ba, hanya ce ta neman abinci. To tabbas, mafiya yawa ba hakan ne manufar su ba, suna gina su ne kawai da nufin yin fasakwarin man zuwa kasashen ketare. Ma’anar fasakwari shi ne, shigarwa ko shigowa da duk wani kaya zuwa cikin wata kasa a asirce kasantuwar kasar da ake shiga ko fita da kayan ba ta halasta hakan ba, ko kuma ana yin hakan ne da nufin kaucewa biyan harajin da aka dorawa kayan. A dukkanin al’ummu na kwarai kamar Nijeriya, masu aikata hakan ana masu lakabi ne da munafukai masu laifin karya tattalin arzikin kasa.

Wadanda ma suka fi su hadarin sune, wadanda a kan baiwa albarkatun man da nufin su kai su wurare na musamman, amma sai su kauce su bi ta barauniyar hanya su karkatar da su zuwa iren wadannan gidajen man na kan iyakokinmu, daga nan kuma sai a fice da kayan wajen kasarnan. Suna cin haramtacciyar riba, kamfanin NNPC kuma na karban zargi. Gaskiyan lamarin shine, kusan dukkanin iren wadannan gidajen man, duk ‘yan Nijeriya ne ke mallakan su. Abin haushin ma shi ne, ba wahalar su a wajen samar da man nan na fetur da aka yi.

Suna zaune, NNPC, na yi masu aiki. A kullum kamfanin na cikin shan suka da zargi, yana ta fadi tashin ganin ya fita kunya, amma su barayin na man, suna gefe suna ta dariyar su. Kullum suna kan hanyar zuwa Banki domin ajiyar makudan kudaden da suka tara ta hanyar haram.

Wannan shi ya sanya a namu fahimtar muke ganin jami’an tsaro su na da mahimmiyar rawar da za su taka a bisa kokarin da kamfanin na NNPC ke yi na ganin ya wadata kasarmu da albarkatun man, ya kuma toshe wadancan hanyoyin da barayin man ke bi suna karkatar da man namu. Kamfanin yana yin aikin shi, wajen baiwa ‘yan kasuwa albarkatun man domin su sayarwa al’umma. Sai dai abin takaicin shi ne, da yawan ‘yan kasuwan suna cikin ‘yan ta’addan da ke sayarwa da gidajen man na kan iyakokinmu da man da ake ba su

Kamfanin na NNPC, ya san ire-iren su, sai dai a irin wannan lokacin ba yanda shi a kan kansa zai iya yi da su. Cikin halin rashin kunya kuma, iren wadannan ma su aikata hakan ne za ka ji sun fito suna kururuwar sam su ba sa cikin masu aikata hakan. Su za ka ji su na kukan janye tallafi da kuma tsadan canjin dala da makamantan hakan, da nufin kara tsawwalawa kamfanin na NNPC, da kuma al’umman Nijeriya, domin biyan bukatan kansu. Mu a wannan jaridar muna ganin sam bai kamata a ce iren wadannan marasa imanin sun fi karfin doka ba. Akwai bukatar da mu yi nu ni da cewa, mafiya yawan hanyoyin da ake bi wajen karkatar da albarkatun man namu, duk ta hanyar mota ne.

Wanda hakan ke nufin za a iya lura da su, a kuma iya yin maganin su, mun tabbata jami’an tsaro da ke aiki da kamfanin na NNPC za su iya gano su tare da yin maganin su. Sai dai kuma idan akwai wani abin ne na daban, ko kuma akwai wasu bayanan da al’umma ba su sani ba, muna bayar da shawarar ya kamata gwamnati ta fara kulle ire-iren wadannan gidajen sayar da man na bogi da ke kan iyakokinmu. Muna ganin hakan zai taimaka wajen hana yawaitar fasakwarin man namu da ake yi zuwa kasashen ketare. Wanda hakan zai saukaka mana wahalar man namu da kuma muke fama da ita.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!