Daga Littattafan Hausa: Asadulmuluk (5) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADABI

Daga Littattafan Hausa: Asadulmuluk (5)

Published

on


08069824895

Hakan ya sa Gimbiya ta aminta da a ba ta ita ta zama ita ce mai kawo mata abinci da wadansu kananan hidimomi don ta samu saukin bauta. matsaya

Ana wannan hali Gimbiya ta dube ta ta ce; “Bintu ko kin san abinda yake faruwa kuwa,?” Bintu ta girgiza kai ta ce; “Ranki ya dade ban sani ba.” Gimbiya ta ce; “Yan’uwanki sun dauko ki a sume, wai yaya aka yi ne?” Sai kowacce cikinsu ta kunshe bakin ta, don sun san in har ta yi magana to kowa sai ya yi dariya. Bintu ta dan daga kanta sama tana tunani, daga baya ta ce; “Ranki ya dade samarin aljanu sun fara yawo a cikin gidan nan.”

Sai kuwa aka kwashe da dariya gaba daya har Gimbiyar. Gimbiya ta ce; “A yi kawai,” sai da kowa ya nutsu sannan ta ce; “Haba Bintu shin ba ki sani ba ne cewa iyayenmu sun riki alkawari tsakaninsu da aljanun gidan nan akan ba za su dinga yawo ana ganinsu ba?” Bintu ta ce; “Haka ne, amma fa ranki ya dade kin san fa su ma suna saba alkawari kamar mu.”

“Gimbiya ta ce; “Yalla kun taba kulla alkawari da aljani na aure ya saba miki ko?”

Bintu ta girgiza kai, “Amma dai ranki ya dade ni dai na tabbata jiya na ga namiji acikin wannan wurin, kuma suffarsa ba ta yi kama da irin ta bayin gidan nan ba, haka nan launin jikinsa ba irin na jama’ar kasar nan ba ne, sannan in ba aljani ba ta yaya za a yi wani namji ya shigo nan bayan an hana.

Ita kuwa wannan baiwar tana zaune ta na jin abin da ake yi, amma tana tsoron ta fadi yadda aka yi a kamata da laifin shigo da wani namiji a yi mata hukunci mai tsanani, daga nan Gimbiya ta yi umarnin aka kawo mata wani abincin. Ummu Nazifah ita ce baiwar da ta yi wa Asadulmuluuk rakiya zuwa cikin gida, kuma ita ce mafi girman bayin da ke gaban gimbiya a shekaru da hankali, don ko da a wasu lokutan ma idan gimbiya za ta yi wata muhimmiyar shawara to ita ce kan gaba. Bayan da Asadulmuluuk ya koma masaukinsa, sai ya sa aka kirawo masa bawan nan da ya yi masa rakiya, da ya zo ya ga kamar ba a hayyacinsa yake ba.

“Ranka ya dade na ga yanzu ka dawo, amma kuma gashi kamar wani abu yana damunka, lafiya?” in ji bawan. Asadulmuluuk ya ce; “Babu shakka ina cikin dimuwa. Wai shin dama ku a nan masarautar a hade kuke da jama’ar aljanu, yanzu kusancinku har ya kai ku dinga tarayya da aljanu a mazaunanku?”

Bawa ya ce; “Ranka ya dade ai ban fahimci abin da ka ke son fada min ba aljanu fa ka ce!.”

“Aljanu mana, saboda yanzu a kan hanyata ta dawowa daga inda ka yi min rakiya, na yi batan hanya, ina cikin tafiya na kai ga wani daki da na ga wata yarinya wadda kyanta ya wuce ace bin adama ce da wannan kyan, kai lallai wannan aljana ce ta rikide ta zama suffar mutane, ka ba ni labari yaya abin ya ke ne?”

Bawa ya yi murmushi sannan ya ce; “Ai ko kusa babu aljanu a gidan nan, kuma babu wani abu da ya yi kama da su, hasali ma muna da alkawri da aljanun gidan nan kan cewa ba za su dinga bayyana a fili ana ganinsu ba, ko dare ko rana.

Ranka ya dade ina kyautata zaton Gimbiya Badee’atulkhairi ka gani don ita kadai ce kyakkyawa wadda mutum kamar ka zai gani ya yaba da ita, ita ‘ya ce ga Sarkinmu wadda ita kadai ya haifa.”

Asadulmuluuk ya ce; “Wannan labarin cewa yana da ‘ya guda daya ai ina da shi, har ma da na shiga sun ce ba ta kusa da an hada mu mun gaisa da ita, amma ban san kuma wani abu bayan hakan ba.”

Bawa ya ce; “Yadda lamarin da sha’aninta yake, ita dai yarinya ce wadda a duk shekara sau daya tak take fita, wato ranar bikin Sallah babba.” Cikin mamaki ya tambayi bawa cewa, “To mecece hikimar tsare ta a gida haka?” in ji Asadulmuluuk. Bawa ya ce; “A cewar mahaifiyar ta, an yi mata katanga ne daga duk wata hanya da za ta iya sada ta da shiga lamari na shedana, misalin yadda ‘ya’yan Sarakuna da na attajirai ke gasar tafiya wurare na shakatawa, a duk ranekun Alhamis da Juma’a, da kuma yi mata iyaka don dauke hankalin ta ga barin kamuwa son hawa doki kamar yadda yake da tushe a fannin Uruusiyyah, wanda a yanzu ya mamaye Daular Larabawa da sauran kasashen duniya masu arziki. Sai dai kuma bisa al’ada ka san akan baiwa ‘ya’yan Sarakuna horo a fannin dabarun yaki, yadda za su kare kansu kafin hari, ni na ba ta horon kuma na gamsu da horon da na ba ta, za ta iya kare kanta idan yiwuwar hakan ta taso, ko da ta wuce lokacinta kuma za ta iya koyon abinda ya fi hakan ma. ”

Duk da cewar ban kare mata kallo ba, to ina maganar yin aure wanda kuma ya wajaba a kanta?” in ji Asadulmuluuk. “Yanzu ita ce a kan gaba, domin da fari dan Wazirin garin nan ya fito neman aurenta, ita kuwa ta juya baya ga barin maganarsa, wanda hakan ya jawo maganganu marasa fa’ida, daga wazirin zuwa Sarki.” In ji bawan.  Cikin mamakin jin haka Asadulmuluuk ya ce; “A’ah ka bani labari, ta yaya har Waziri ya kan iya fadar kalma maras fa’ida ga Sarki, kuma akan sha’anin auren ‘yar Sarkin?” Bawa ya ce; “Kamar yadda ka sani a al’ada da Shari’ah dole Waziri ya zama mai ilmi da hankali, amma wannan wazirin namu ba haka yake ba, don ko a wajen nadin sarautar sabon waziri bayan wancan ya rasu ma ba shi ya cancanta ba, cikin dare ya aika aka kashe wancan shi kuma ya zo aka yi masa nadin saboda ana tsoron mugun kaidinsa. To tun daga wannan lokaci da ta ce ba ta kaunarsa, ba mu sake jin wani ya fito neman auren ta ba.” Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah ya kai mu.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!