A Ko’ina Akwai Zalunci..! — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

A Ko’ina Akwai Zalunci..!

Published

on


Kalaman mafi yawan mutane a Nijeriya ya fi nuna cewa, an fi aikata zalunci a matakai na gwamnati; kama daga ma’aikatan gwamnati na farar hula, jami’an tsaro zuwa kan masu rike da mukaman siyasa, kamar kansila, shugaban karamar hukuma, ’yan majalisa, sanatoci, gwamnoni da ma kujerar shugaban kasa. To, amma ya wajaba mu sani cewa, a ko’ina a na iya samun zalunci. Kuma duka zalunci, zalunci ne, sannan kuma haramun ne a wajen Allah, kazalika haramun ne a dokokin kowacce kasa, la’alla mutane ne su ka aikata zaluncin a dai-daikunsu ko a kungiyance ko kuma a gwamnatance. Sammakal!

Zalunci ya na iya faruwa a cikin gida tsakanin mata da miji, iyaye da ’ya’ya, uwargida da amarya ko tsakanin masu gida da barori. Duk wanda ya tauye wa wani hakkinsa a tsakan-kanin wadannan mutane masu mabambantan dangantaka, to fa sunan wannan abin zalunci. Idan mace ta ha’inci miji ko ya tauye ma ta hakkinta, zalunci ya faru. Idan iyaye su ka ki sauke hakkinsu a kan ’ya’ya ko ’ya’ya su ka ki yin biyayya da kyautata wa iyaye, zalunci ya wanzu. Idan kishiyoyi su ka kulla sharri a tsakaninsu, zalunci ya tabbata. Haka nan idan masu gida su ka azabtar da barori ko barori su ka aikata almundahana kan masu gida, shi ma zalunci ya afku kenan.

Bugu da kari, zalunci ya na iya faruwa a kamfanoni tsakanin masu kamfani da ma’aikatan kamfanin, tsakanin manyan ma’aikata da kananan ma’aikata ko tsakanin masu binciken kudi daga waje da ma’aikatan kamfanin na cikin gida. Duk lokacin da masu kamfani su ka tauye hakkin gumin ma’aikaci ko shi ma’aikacin ya yi zagon kasa yayin gudanar da aikin da a ka dora ma sa, to zalunci ya faru kenan. Idan manyan ma’aikata su ka shiga hana wa kananan ma’aikata damarsu ko kananan ma’aikata su ka nuna bijirewa umarnin na gaba, to an aikata zalunci. Duk san da masu binciken kudi su ka aikata cin hanci da rashawa ko ma’aikatan cikin gida su ka tafka ha’inci da rufa-rufa, to zalunci ya wanzu kenan a nan.

A matakai na aikin gwamnati kuma zalunci na iya afkuwa tsakanin ma’akata da sauran al’umma. Duk lokacin da wani ma’aikacin gwamnati ya saka ha’inci da almundahana a cikin aikinsa ko al’umma ta dakile ma’aikaci har ya gaza cimma aikata aikinsa, to an aikata zalunci kenan.

Yayin da jami’an tsaro su ka halasta cin hanci da rashawa ko su ka fifita rashawa a yayin gudanar da ayyukansu ko kuma mutanen gari su ka goyi da bayan kama-karya ko amfani da kusanci ba bisa ka’ida ba, to fa babu shakka an tafka zalunci a nan kenan.

Idan masu rike da mukaman su ka siyasa su ka yaudari al’umma ko su ka aikata cin amana ko su ka yi nade-nade bisa son zuciya ko kuma mabiya su ka goyi da bayansu ko masu zabe su ka zabe su ba bisa cancanta ko kuma masoya su ka goya wa masu rike da mukaman siyasa baya a kan son rai, to zalunci ya wanzu kenan.

Ba komai wadannan misalai ke nufi ba face nuni da cewa, a kowane irin mataki ko dangantaka a na iya samun abinda a ke kira da zalunci, ba sai shugabannin da a ka dora wa alhakin tafiyar da ragamar gwamnati ne kawai su ke iya aikata zalunci ba; kowanne a cikinmu zai iya tsintar kansa a inda a ke bukatar ya  kauce wa aikata zalunci, ya kuma guje shi, domin sai kowa ya yi gyara kan damar da ke hannunsa sannan ne gyaran zai kai kowane mataki na kasa da a ke muradin a ga an cimma tun daga ainihin tushen jijiyar tsiron matsalar har zuwa kan ainihin hudar furen.

Tabbas wannan kalubale ne da ke kan kowa! Allah Ya ba mu ikon farkawa yanzu-yanzun nan, don tsamo Najeriya daga sarkakiyar koma-bayan da ta ke ciki. Amin!

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!