Marubuta Ba Makaryata Ba Ne –Bashir Sa’ad Dambatta — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

ADABI

Marubuta Ba Makaryata Ba Ne –Bashir Sa’ad Dambatta

Published

on


07038339244  ay1indabo@gmail.com

Matashin marubucin wanda yana cikin marubutan da suke tasowa, ya furta hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin ADABI A YAU, ADAMU YUSUF INDABO. Furucin dai na Malam Bashir ya zama tamkar martani ne ga furucin tozarcin da aka yi wa Marubuta a taron Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya da aka yi a jahar Katsina dake Arewacin Najeriya, a watan Maris din da ya gabata. Furucin da ya kai ga yamutsa hazo har ta kai ga wasu marubutan sun kauracewa taron. Bashir Sa’ad dai shi ne sakataren kungiyar marubuta ta Aminchi Writers Association Dambatta, kuma marubucin littafi, Matar Dana, Mace Haja, Zumuncin Boye da dai sauransu. Ga cikakkiyar hirar tasu kamar haka:

Wane ne Bashir Sa’ad Dambatta?

Sunana Bashir Sa’ad Dambatta, amma ana kirana da Money ko M-Life. An haife ni a jahar Kano cikin karamar hukumar Dambatta a shekarar 1994, na yi karatun boko da na addini duk a cikin garin Dambatta. A shekarar 2014 na wuce school of basic mass communication na yi certificate. A shekarar 2015 na yi saukar Al-Kur’ani Mai gifma. Yanzu kuma ina school of management Kano, ina diploma a kan Media and public relations.

 

To ya maganar iyali?

Hmn, iyali kuma ai da sauran lokaci.

 

To wanne tsani Malam Bashir ya taka ya sada shi da dunjyar rubutu da marubuta?

Ai Malam Adamu tsanuka ne ba tsani ba. Amma dai tsani na farko shi ne sha’awar yin rubutun da kuma karatun littattafan Hausa da na taso da shi tunda kuruciyata. Bayan haka ina son tsayawa gaban mutane ina magan suna sauraro na,su kuma yi amfani da abun dana ce. Hakan ya sa tun ina secondary nake a cikin kungiyar FRESH CLUB duk sati muna gabatar da labarin abun daya faru a maakaranta da ma cikin gari, a lokacin ma ni ne jagoran kungiyar. Ina jin dadi idan na fito gaban assembly ina karanta labarai, na ga an nutsu ana saurarona. Kwatsam sai kuma na ji ina sha’awar fara rubutu. Ai ko sai na fara rubuta Matar Dana, a lokacin ina da shekaru 16 da haihuwa.

 

A wacce shekara ka fara rubutu ke nan?

2009 a lokacin ina aji 2 na karamar sakandare.

 

Zuwa yanzu ka rubuta littattafai sun kai nawa?

A yanzu haka na rubuta littattafai guda bakwai.

 

A cikinsu wanne ne bakandamiyarka?

Littafin MACE HAJA shi ne bakandamiyata, saboda yadda lsbarin ya zo da wani sabon salo da yake taka muhimmiyar rawa a wannan zamanin namu, kuma ya samu karbuwa sosai a wajen makaranta.

 

To kasancewarka makaranci tun kafin ka fara rubutu, to a cikin marubutan waye gwaninka?

Shafi’u Dauda Giwa ne gwanina, littafinsa KAFIN SAFIYA ya matukar burge ni.

 

Ko kana da ubangida a cikin marubuta?

Kwarai kuwa, ina da uwardaki a cikin marubuta, ita ce Aisha Ali Dambatta, marubuciyar Nacin Zuciya da kuma Mata Hudu.

 

To ya batun kungiya?

Ina cikin kungiyar marubuta ta Aminchi Writers Association Dambatta ni ne ma sakataren kungiyar, sannan ina halartar tarukan kungiyar HAF da Tsintsiya don sada zumunci da karin ilimi a harkar rubutuna.

 

Zuwa yanzu wacce nasara ka samu a duniyar rubutu?

Ai nasarori za ka ce Malam Indabo, domin suna da yawa. Amma kadan daga ciki: na samu nasarar yin mu’amala da manyan marubutan da duniyar rubutu ke alfahari da su. Na ziyarci manyan tarukan marubuta irinsu taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya na Daya da aka yi a jahar Kano a shekarar 2016, dana Biyu da aka yi a jahar Katsina kwanakin baya, kuma ina ma cikin ‘yan kwamiti na wannan taron. Ka gako hakan babbar nasara ce gare ni da masoyana baki daya.

 

To kalubale fa?

Kalubale kam akwai su, amma ni ba sa gabana, saboda kullum mahaifiyata addu’ar Allah Ya tsare Ya kuma taimakatake yi mini, kuma ga shi Allah Ya karbi addu’rta, saboda ina ganin nasarori ta bangarori da dama.

 

Ka ambaci Taron Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya Karo Na Biyu da aka yi kwanakin baya, taron da wasu ke yabawa wasu kuma suna suka, saboda ayyana marubuta da makaryata da aka yi a gun taron. To ko me Malam Bashir zai ce game da haka?

Tabbas akwai wanda ya kira mu marubuta da makaryata, hakan bai mana dadi ba har abun ya haifar da matsaloli da dama, saboda marubuta ba makaryata ba ne, fasihai ne da Allah Ya yi mana baiwar kirkira, don fadakarwa da nishadantarwa.

 

Game da matsalolin da aka samu, wanne kira za ka yi ga ‘yan uwa marubuta domin kaucewa hakan a gaba?

Tabbas an samu matsaloli masu tarin yawa a taron da ya gudana, tun kafin taron aka fara samun matsaloli, da dadi babu dadi aka ganganda a ka yi. Saboda kusan kullum ka leka group din kwamitin shirya taron sai ka samu ana ta cece-kuce wanda har a ranakun taron an samu irin haka. So kirana dai ba zai wuce na mu dinga hakuri mina kai zuciya nesa ba, sannan mu hade kanmu, mu kaunaci juna da zuciya daya. Hakan shi ne zai sa mu kai ga nasara a dukkan al’amuranmu, in ko ba haka ba, za mu yi ta tsalle ne a waje daya.

 

A karshe wanne sako kake da shi ga masoyanka?

Ina alfahari da masoyana a duk inda suke a fadin duniya, ina jin dadin yadda kuke yaba  rubutuna tare da ba ni shawarwari, fatan ni da ku Allah ya ba mu tsawon rai mai amfani don mu ci gaba da amfanar juna.

 

To Malam Bashir mun gode.

Ni ma na gode.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!