Sharhin Fim Din ‘Bayan Fage’ — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Bayan Fage’

Published

on


09097438402 habibsaddika@gmail.com

Suna: Bayan Fage

Tsara labari: Jamil Nafsin

Producer: Mukhtar SS

Director: Nasiru Ali Koki

Kamfani: Habiba My Enterprises

Jarumai: Sadik Sani Sadik, Rabi’u Rikadawa, Ladidi Tubless, Mukhtar SS, Fati Kaduna, Lawal Ahmad da Sulaiman Bosho

Sharhi: Saddika Habib Abba

A farkon fim din an nuna ana soyyaya tsakanin Anas(Lawal Ahmad) tare da Hassana (Fati Shu’uma) suna matukar son junansu shi Anas ba shida karfi sana’ar sai da shayi yake yi yana zaune tare mahaifiyarsa cikin rufin asiri kwatsam sai wani abokin Anas yazo Nura (Sadik S Sadik)daga wari an yi masa canjin aiki ya dawo Kano da zama shi yana da rufin asirinsa sai Anas ya daukeshi suka tafi gidansu Hassana domin su gaisa suna zuwa sai ya ga Usaina kanwar Hassana domin dama ita Hassana ‘yan biyu ce da Usainar ta sai yace yana sonta sai ita Usaina ta amashi soyyayarsa hannu bibiyu, ana cikin haka sai kanin mahaifin Anas ya kirawo shi zuwa Garin Kaduna saboda zai yi tafiya yana so Anas din ya jire masa shagunansa na tsahon sati biyu, Anas suka yi sallama da Hassana ya tafi garin Kaduna. watarana Hassana ta fito bakin titi sai ta hadu da Nura acikin mota tare da uban gidansa a gurin aiki Alhaji Afarasima(Sulaiman Bosho) suka rage mata hanya suka kai ta gurin da zata je tun a lokacin sai Alhaji Afarasima yaji ya fara son Hassana Nura ya yi masa jagora zuwa gidansu yaje suka fara siye mahaifin su Hassana da abin duniya domin dama tun farkon fim din an nuna mahaifin su Hassanar mai son abin duniya ne har mahaifiyarsu, anan labari yasha bam-bam iyayen su ka juya akalarsu zuwa kan Alhaji Afarasima domin har kyautar mota da kudi masu yawa ya yi wa mahaifinsu, ita kuma Hassanar ta tsaya kai da fata akan cewar ita batason Alhaji Afarasima sai Anas din ta takeso ana cikin haka sai Anas ya dawo daga tafiya sai ta fadamasa halin da ake ciki akan mahaifinta yana son hadata da wani sai Anas ya yi zuciya ya gani tamkar itama Hassanar tana sonsa Hassana ta yi ta bibiyarsa tana bashi hakuri sai daga baya ya tsaya tayi masa bayanin abokinsa ne fa Nura ya kawo mutumin Anas ya yi matukar mamaki sannan ya fuskanci ita Hassana tana tare da shi sannan suka fara neman mafita, a bangaren mahaifinta kuma magana tayi karfi tare da Alhaji Afarasima da a lokacin da mahaifin Hassana yaga Anas ya matsanta sai ya kafa masa wani sharadi akan yaje ya shiryo nan da kwana biyar yazo a daura musu aure idan har zai iya a lokacin Anas ya shiga cikin damuwa ya buga ya buga bai sami kudin auren ba sai hakura ya yi, aka saka ranar daurin auren Alhaji Afarasima da Hassana kafin ranar tazo sai wani mai sai da gwalagwalai ya ganta mai tarin dukiya wadda tafi ta Alhaji Afarasima labari ya sha bam-bam ranar daurin aure sai Alhaji Afarasima yaji an daura da wannan mutumin ba da shi ba shi kuma Nura an daura masa da tasa budurwar Usaina, hankalin Alhaji Afarasima ya tashi kuma tabbatar wa da mahaifin Hassana sai an dawo masa da duk abinda ya mallaka musu, nan fa rigima ta kacame musu.

 

Abubuwan Birgewa:

1- An nuna muhimmancin rikon amana a fannin soyyaya.

2- An nuna muhimancin yin soyyaya tsakani da Allah.

3- Kyamara ta daukar hoto ta fita babu laifi a fim din.

 

Kura-kurai

1-An ga Hassana ta shigo gidansu Anas tazo nemansa bisa tsari na al’ada da addini bai dace ace tazo gidansu nemansa ba sai dai shi yaje, sannan an nuna mahaifiyar Anas mutuniyar kirki ce amma irin shigar da Hassana tayi ta rashin tarbiyya ta shiga gidan ya dace ace ko yaya tayi wa Anas korafin rashin kamun kan budurwar ta sa ko kuma tace ma ya canja wata.

2-Sana’ar Anas an nuna sai da shayi ce bayan ita ba’a nuna yana wata sana’ar ba amma sai maikallo yaga keken dinki acikin dakin Anas shin wannan keken dinkin menene matsayinsa? idan ma na mahaifiyarsa ne bai dace ace an ganshi a dakin matashi kamar Anas ba, ballanta ita ma mahaifiyar tasa ba’a nuna tela bace.

3-Yanda aka nuna katafaren gida irin na mahaifin su Hassana bai dace ace yana nuna tsananin kwadayin abin duniya haka ba don gidansa ya nuna shima yana da shi, idan wannan kwadayin za’a nuna sai a nuna girman gidansa da arzikinsa bai kai yadda aka nuna a fim din ba.

4-kawai an nuna ana daurin auren Hassana da wani mai kallo bai ga duk yanda abubuwan suka kasance ba ambarshi a duhu sannan ba’a nuna makomar soyyayarta da Anas ba ko kuma fim din akwai cigaba?

5- Alhaji Afarasima yana furta wasu kalamai wanda basu dace ba a fim din wanda zasu iya kasancewa sun bata tarbiyya kamar wurin da yazo tare da mahaifin Hassana ya sameta acikin harabar gidansu suna zance tare da Anas. sannan wanene shi? shin saurayine ko kuma yana da aure? ba’a taba zancen iyalinsa ba a matsayinsa na babban mutum kamar hakan

6-Menene makomar cin amanar da Nura ya yi? don an nuna riba ma yaci tunda shi ya samu ya auri Usaina. yakamata a nuna karshansa saboda darasi.

7-Akwai wurin da aka nuno wasu garda gardan samari sun danno kai sun shigo falon gidansu Hassana sun shigo da sakon kayan abinci wanda Alhaji Afarasima ya aiko su an ga sun sami mahaifiyar su Hassana sun bata, shigowarsu kai tsaye cikin gidan ba tare da iso ba a matsayinsu na baligai bai dace ba domin gida ne na matar aure.

8- An ga Alhaji Afarasima ya yi wa mahaifin Hassana kyautar mota mai tsada amma shi Alhaji Afarasima har fim din ya kare acikin motocin da yake hawa ba’aga wacce tafi wadda ya bayar tsada ba, tunda har yana iya kyauta da wannan ya dace ace wacce yake hawa tafi wannan tsada.

9- An ga Anas yana tafiya yabar gurin sana’ar shayinsa babu kowa kamar lokacin da Nura yazo ya daukeshi, kuma anji Anas yace ba shida yaro shin wa Anas yake barwa gurin nasa ya tafi? ko costormer’s dinsa yake bawa su jire masa? to idan ma hakane ai ba’aji ya fada ba.

 

Karkarewa:

An nuna illar kwadayi amma zaren labarin bai dire ba sannan babu cikkaken jigo a labarin.

 

Advertisement
Click to comment

labarai