An Bar Taiki Ana Dukan Jaki — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MAKALAR YAU

An Bar Taiki Ana Dukan Jaki

Published

on


idrisdaudawaaliyu@gmail.com 08065683849

Sauda yawa haka abubuwa suke tafiya idan kuma ba farga aka yi ba da sauri shi ‘’Jakin Da Ake Duka Saboda Baida Sauri’’ ana yin wasu kura kurai na rashin tsayawa koma a samu lokacin yin hakan, kawai abinda mutane da yawa suke ta gani shine, idan irin hakan ta faru sai laifin wasu ko kuma wani, bayan kuwa ga mai laifi ana ganin shi kiri kiri, amma kamar ya gagara ne ayi ma shi magana, kodai kai tsaye, ko kuma asa wasu suyi ma shi. An dora ma shi kayan fa  da suka fi karfinshi, saboda ya kasa tafiya kamar yadda kowa yake tsammanin zai yi hakan, kowa dai  gani yake jaki shi ne ke da laifi, ba tare da an yi la’akari da yawan kayan da aka dora ma shi ba, ba kuma a tambayar shin ko zai iya daukar kayan, wannan duk ba a yin hakan saboda rainin da ake yi ma shi, da kuma wani kallom masheka aya.

Al’amarin tabarbarewar tsaro akan halin da ake ciki kowa ya san shi ke cima mutane tuwo a kwarya, kamar an rasa wane irin mataki ne ya kamata a dauka. Duk wadanda ya dace ace suna kan gaba wajen bada shawarar, babban matakin da ya dace a dauka, yanzu gasu can an barsu a baya.

Kamar dai yadda kowa ya sani doka daga gida ne take farawa, ’’Idan kuma ana Dara fidda uwa ake’’ duk wani sakarcin da za a ce ‘’ya’’ya sun tashi dasu ai sai an barsu, saboda kuwa, ai gida wurin da kullun za a rinka ganin Iyaye can ne babbar makaranta ta farko wadda za a tashi da tarbiyya, tun ana ‘yan kanana. Sai makaranta ta biyu al’umma wadanda suka kunshi mutanen unguwar da ake, da kuma daukacin  su mutanen garin suma suna taka muhimmiyar rawa wajen bayar da tarbiyya ta gari. Makarantu duk suma wurin da ake bayar da tarbiyya ta gari ce, baya ga shi ilmin, abin ba tsaiya akan ilmi ba, saboda kuwa ita tarbiyya idan ba tare da ilmin ba, ai tamkar wani fankon ashanar da babu komai ne. Duk wadansu laifukan da ake aikatawa suna da nasabar rashin ba ‘ya’ya tarbiyya da ilmi tun suna yara kanana, lokacin ne zasu fi dadin juyawa, amma idan ka bari har yawo da hankali suka fara shigarsu, to abin zai yi wuya a samu damar sa su koyi wani abin da su a lokacin suna ganin al’amarin duk ya daure masu kai, kuma hadin kai zai yi wuya su bada shi dari bisa dari, kamar yadda ake son su yi.

Idan aka dan nutsa aka tuna da wasu ‘yan shekarun da suka wuce ai kowa ya san masu sarautun gargajiya sun taka muhimmiyar rawa, wajen aza tubulin  kulawa da tsaro, wannan kuwa ya fara ne tun daga unguwa inda mai unguwa wanda shi wannan mai unguwa, shine mai babbar fada aji ta bangaren tsaro, da kuma yadda za a bi doka, sai garin Dagaci wanda shi ne masu Unguwanni suke karkashin sa, ana kara yin dan tattaki sai kuma Hakimi shi kuma shi ne mai lura da Dagatai, da yake tafiya tayi tafiya, ai sai Sarki wanda shi ne oga kwatakwata wanda su kuma Hakimai daga wurin sa, suke amsar umarni.

Idan an yi bako a unguwar Malam Saisaye, shi da kan shi zai tambayi shi wannan bakon nan, na shi da maganar kwana nawa zaka yi, zai yi, ko kuma zai kai har wata, kai maganar gaskiya duk bakin da aka yi, duk gidan da suka sauka sais hi maigidan ya je, ya sanar da Mai unguwa yana da baki wane da wane zasu yi, kwanaki, ko kuma makonni, kai har ma da maganar ko zai yi wata ne wata,da kuma sana ‘oin da suke yi. Haka shi ma mai unguwar zai sanar da Dagaci, shi kima Dagaci ya sanar da Hakimi, da haka abin zai kai har  sai ya kai ga kunnuwan sarki, ga yawan jimillar bakin da suka zo kasarshi, sana’oin da suke yi, da kuma iyakar lokacin da  zasu dauka, suna zaune a wurin.  Duk wannan fa ta hanyar da ake aikawa da irin wadannan sakonnin ana tashin wani mutum ne ya tafi zuwa wajen Dagaci saboda ya sanar da shi irin halin da ke ciki, dangane da tsaro, ana hawan Dawakai ne  alokacin, ba wata maganar waya, ko mota ma ba suyi yawa ba, ba a da wasu sauran hanyoyin sadarwa na zamani wadanda ake dasu yanzu, amma abin wannan ya nuna da akwai matukar kishin kasa dangane da hakan, ba wai ina nufin yanzu babu sauran maganar kishin kasar bane, amma dai Hausawa sun yi wata karin magana inda suke cewa ‘’Idan kana da kyau to ya dai kamata ka kara da wanka. Wancan lokacin ana biyan su masu sarautun gargajiya albashi tun daga mukamin mai unguwa har ya zuwa Sarki, sanin muhimmancin kowa ya sani, su a al’amuran da suka shafi harkar tsaro.Yanzu masu sarautun gargajiya ba duka ake basu albashi ba, wanda ba wai ya taka kara ya karya bane, idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da suke badawa. Saboda idan ka dubi masu unguwanni sune suke zaune wasu ma tun Iyayen yaran suna suma a lokacin kanana, sun san halayyar kowa, nan da nan cikin sauri, da zarar an ga mutuma ya kauce hanya, za a maido shi kan hanyar da zata kai shi gida, ba yayi ta kara shiga cikin kungurmin daji ba. Halin da ake ciki yanzu irin wannan yayi matukar wuya, domin zan iya cewa dukan yayi yawa, abin da yasa koma na kan, ba a iya karewa, musamman su masu unguwannin wadanda sune ke yin yawancin dukkan ayyukan.

Da akwai dai bukatar a sake lale dole ne  sai an kulawa da masu sarautun gargajiya, ta hanyar basu  martabarsu  da kuma hakkinsu , wadanda suka kamata, a koma baya yadda ake na lura da duk bakon da ya shigo gari, an san ko wane ne shi, gidan wa ya sauka, kwana nawa zai yi, da kuma sana’ar da yake yi.  Sabanin yanzu sai dai kawai ayi ta ganin hakanan kamar tururuwa, sun dai zo amma ba a san halinsu ba, ko kuma su wanene su, sannu a hankali irin su ne haka watarana ba abin mamaki bane aji sun tada wata husuma.

Wani abinda kuma ya dace ita gwamnati tayi shine bincikar wasu daga cikin jami’an tsaron ta, kamar su masu kula da shige da ficin al’umma, masu barin Nijeriya da kuma shigowa cikinta, wato Immigration ke nan . Ta yaya har baki zasu shigo, a ina kuma suke samun makaman da suke amfani dasu idan sun tashi attukansu na basu dace ba, ya kuma ko su wanene suke samar masu da makaman,muddin dai ba za abi diddiki ba a gano bara gurbi ma’aikata ayi gaba dasu, daga dukkan bangarorin tsaro , to za kuwa a dade ana cikin yin karatun Dankama. Idan an gano wadanda suke da laifi na yadda bakin haure suke shigo Nijeriya da kuma wadanda ke daure taimaka masu, a hukunta ko wanene mutum, wato a tauna tsakuwa domin ita aya ko taji tsoro.

Yana da kyau dangane da jiragen yakin da aka sayo dagawa kasar Amurka, wannan mataki ne da yasa shugaba mawa saboda murkushe masu tada zaune tsaye. To amma babban abin da za a kula dasu shine,  a koma irin yadda aka yi ba a samu matsalar tsaro ba sai yanzu, a gano me yasa ba a samu matsalar baa da can, me kuma yasa ake samun matsalar tsaro yanzu. Iyaye kuma ya dace su kara kulawa da tarbiyyar ‘ya’yansu, saboda tun daga gida ake fara yin saka amma  fa kuma da bakin zare.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!