Babu Al’mundahana Kan Adadin Kudin Giratuti A Bauchi —Habu Gar — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Babu Al’mundahana Kan Adadin Kudin Giratuti A Bauchi —Habu Gar

Published

on


ALHAJI HABU GAR Shi ne shugaban kungiyar masu karbar fansho na jihar Bauchi, ya yi karin haske dalla-dalla dangane da batun da gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya yi, na cewar a shekara ta 2015 an gabatar masa da Naira biliyan 15.5 a matsayin kudin da ake bin gwamnati na giratuti, inda kuma a shekara ta 2017 sai aka sake gabatar masa da Naira biliyan 26.3 a matsayin kudin giratutin da ake binsa. wannan dalilin ne ya sanya gwamnan ya yi shakkun biya. To sai dai, shugaban Habu Gar ya bayyana cewar babu wata cuwa-cuwa ko kuma neman cutar gwamnan kan wannan adadin, yana mai bayyana cewar dole ne gwamnan ya fahimci cewar a kowane wata ana samun masu yin ritaya kuma kudin karuwa suke yi, don haka ne ya bayyana komai filla-filla. Ya kuma shaida hakan ne a hirarsa da wakinmu KHALID IDRIS DOYA. Ga hirar:

Ka gabatar mana da kanka?

Sunana Alhaji Habu Gar shugaban kungiyar masu karbar fansho  na jihar Bauchi, sannan kuma ni ne Shatiman Gar.

 

Me za ka ce kan jawabin gwamnan Bauchi a ranar ma’aikata wanda ke bayani kan dalilansa na rashin biyan kudin giratutin tsoffin ma’aikata?

Mun ji jawabin gwamnan Bauchi, mun kuma karbe shi, mun kuma fahimci me yake cewa. Wato, kowa da fahimtarsa a rayuwar duniyar nan. domin duk yadda ka ji an ce maka kungiyar masu amsar fansho ka sani mutane ne masu ilimi da kwarewa, akwai likitoci, farfesoshi, gwamnoni, mataimakin gwamna, manyan sakatarori da sauran manyan bangarori duk za a ka samesu a karkashin wannan kungiyar; hatta shi kansa gwamnan mai magana mamba ne a wannan kungiyar.

Dole ne mu sanya hankali da lura kan wannan batun, abin da nake son kowa ya sani shi ne, wannan batun tantance masu bin bashin giratuti wasu tantancewar ma da mu aka yi, an yi aikin nan har kusan sau uku da ni. Abin da kuma muka yi shi ne, fayel-fayel muka bi daya bayan daya muka yi ta bi muna tantancewa. Abin da muke kuma son kowa ya sani shi ne, aikin gwamnati gadarsa ake yi, idan ka ga ka zo ka zama gwamna dole ne za ka samu wasu nakasu da ake son kai ka cike, wanda shi wanda ka amshi gwamnan nan a hanunsa ya barsu. Don haka ba wani abu ba ne idan wannan gwamnan ya zo ya samu bashin giratuti.

 

Kamar Naira biliyan nawa ne wannan gwamnan ya gada daga gwamnatin da ta shude na giratutin?

Naira biliyan goma sha daya ne, gwamna mai ci ya gada daga gwamnatin baya. Mun sani, lokacin da ya amshi gwamnatin asusun gwamnatin jihar Bauchi babu ko sisi a ciki, don haka a wancan lokacin mun yi masa uzuri.

 

Jihar ta samu tallafin Paris Club da Bailout, amma har zuwa yanzu gwamnatin ba ta biya ko sisi ba, kuma kana cewa babu kudi?

Eh, gwamna bai biya ko sisi na kudin giratuti ba; amma lokacin da aka kira ni daga gidan gwamnati, an shaida min cewar gwamnan na son biyan kudin nan, ko kuma ya rage. Domin mun tattauna da wasu manyan daraktoci suna nan suna kuma kan shawo kan gwamna domin ganin ya biya wannan kudi. A don haka ina bukatar ‘yan uwana masu amsar fansho ina masu ba su hakuri, domin ba wai zan fito a matsayina ina zagin gwamna ba ne, a’a ba zan yi hakan ba. A kan bayanin gwamna kuma, lallai ne bayani yakan yi kama da bayani. Abu daya kawai kuma wanda ya kamata shi ne gwamna ya rufe ido kawai ya biya wannan kudaden na giratuti domin masu shi su amshi hakkinsu.

 

Gwamnan jihar nan ya bayyana cewa kudin nan ya yi masa yawa ne ya sanya bai biya ba; domin daga shekara ta 2015 zuwa 2017 kudin ya karu sosai ta ina kudin suka yi tashin gwarron zabi?

Kan wannan kudin, dole ne gwamna ya duba baya. Ina son ya tuna cewar akwai manyan sakatarori da daraktocin da suka shekara takwas wadanda ya ce a yi musu ritayar dole. Wadannan wanda aka yi musu ritayar dole nan su kadai kudadensu ya kai biliyan biyu su kadai ma, wanda kuma shi gwamnan da kansa ya yi musu ritayar nan bayan da ya zo kan mulki, ka ga kudi ya yi mene ne? ya karu. Sannan kuma, shekaru uku daga lokacin da aka ba shi wancan kidayar ai shekaru ukun nan ana sake samun masu yi ritaya. Don haka ina rokon gwamna ya daure ya cije ya biya wannan kudaden kawai. Ina mai shaida masa idan fa ya biya wannan kudin dukkanin wani magana a jihar Bauchi ya rufe kenan. Wannan da yanzu gwamnan nan zai fara biyan kudin giratuti da zai fi kowa jin dadi, kuma sakayyar da zan yi masa shi ne zan yi gangamin samar masa da jama’a a zaben da ke tafe.

 

Shi gwamna ya ce ku je ku kawo masa kididdigar da zai yi amfani da ita ta hakika, ku kuma kuna maganar cewar kudin nan daidai kuka gabatar masa ina matsalar take?

Idan gwamna ya ce a kawo masa sunayen mutane nan da suke bin kudin nan za a kawo masa, kuma idan aka gabatar masa da sunayen da ba su ba ne nan ma ya sani. Wallahi idan gwamna ya ce a kawo masa jerin sunayen mutanen da suke da hakkin giratuti tun lokacin da ya amshi mulki shekaru uku zuwa yanzu, za mu kawo masa sunayen mutane da kuma adadin kudadensu, ba wani abu a boye ai.

Domin ita maganar kudin giratuti kowane wata fa ana samun masu yin ritaya don haka a kowace shekara ana samun karin kudaden giratuti, yanzu idan gwamnan ya tsaya bai biya ba ma, kudin nan za su ci gaba da hauhawa ne, kai ko a watar da ta gabata kusan mutane 80 ne suka yi ritaya a jihar nan, don haka ka ga kowace wata kudin karuwa suke yi, idan wata shekara ma ta zo za ka sake jin kudin sun karu ne ai, ko raguwa ake son su yi alhalin ba a fara ragewa ba?

 

Daga lokacin da M.A ya hau kan mulki zuwa yau, za ka iya kiyasta adadin ma’aikatan da suka yi ritaya a jihar?

Ma’aikatan da suka yi ritaya za su kai dubu hudu ko biyar, daga lokacin da ya hau mulki zuwa yau, kuma wadannan da suka yi ritayar yawancinsu manyan ma’aikata ne ba kananan ba.

 

Daga jiha zuwa kananan hukumomin, mutane nawa ne suke jiran samun kudin giratuti?

Yanzu haka mutanen da suke jiran kudin giratuti za su kai mutum duba shida, wadanda suke jiran kudinsu na giratuti. Ina kira ga gwamna da ya biya kudin nan, idan yana son ya ga mutanen nan ne za mu iya kawo masa kowa da kowa domin ya ga wadanda suke da hakki kan kudin giratuti. Idan kuma ma zai kafa kwamiti ya ce a biya mutane nan daya bayan daya muna lale da hakan, kuma muna shirye, kowa ya zo ya gabatar da takardunsa a biyasa kudinsa duk muna shirye. Wadanda suka mutu su ma tsarinsu na nan.

 

Akwai kwamitin da gwamna ya kafa kan wannan batun, yanzu ku a kungiyance mene ne kuke son kwamitin ya yi?

Idan a ce a yi kato bayan kato ne wallahi muna shirye, domin ana son a yi gaskiya ne, muma muna son a yi gaskiya, gwamna ya sanya dukkanin wadanda yake ganin sun dace su biya kowa kudinsa ya zo a tantance shi a ba shi hakkinsa. An kuma taba yin haka a lokacin gwamna Isa Yuguda lokacin da ya ba mu Naira biliyan shida muka raba wa masu hakkinsu, ina cikin kwamitin.

 

Wane kira kuke yi ga mambobinku?

Ina kira gare su da su kara hakuri domin ina da yakinin za a biya kudin nan, mu dai kara hakuri.

 

Wasu mambobin da suke jiran kudin giratutin nan suna ganin kamar karancin matsawarku ga gwamnati shi ma ya taka rawa wajen rashin samun kudaden nan me za ka ce?

Muna iya yin mu, domin babu yadda za ka yi da gwamna domin shi ne mai sa wa mai kuma hana wa, don haka ba za mu tilasta masa ba, kuma ba za mu dauki halin yin zanga-zanga ba, domin hakan bai haifar da komai illa wani tashin hankalin da asaran rayukan jama’a, don haka muna dai kiran dukkanin matakan da hakuri bai bayar ba, zanga-zanga ma ba za ta bayar ba.

 

Akwai wasu da suke ganin kai din nan ka hade da gwamnatin jihar Bauchi har ma kasashen waje take fitar da kai, don haka ne suke cewa ka hada kai da gwamnati don haka ne ba ka yin abin da ya dace me za ka ce?

Gaskiya wannan maganar ba gaskiya ba ce, domin gwamnatin Muhammad Abdullahi Abubakar ni tun da nake ban taba tashi da ni da shi muka je wani waje kai koda daga nan zuwa Alkari ne kuwa, a kullum ni ina kare muradun mutanena ne, a matsayinsu na wadanda suke grime ni, suka fi ni ilimi suka fi ni matsayi a wajen aiki a lokacin da suke yin hidima ga kasa suka kuma fi ni komai, ni su nake dubawa.

 

Ba ka ganin rashin zafafawar da kake yi ne ya janyo jama’a suke maka wannan kallon dan amshin shatan?

To zan je na kama gwamnan da kokuwa na ce masa sai ya biya ne? shi gwamna ne kuma shugaba ne, kuma ina mutunta shi, domin shi shugaba ne. ni dai ina rokonsa da ya fara biya don Allah, mu bamu ce daman ya biya dukka ba, cewa muke ya fara biya wannan shine matsayarmu. So muke a fara biya, wadanda suke bin kudin giratuti daga 2010, 2011 zuwa 2015 a ci gaba da biyansu, har Allah ya sa a kammala binciken daga 2015 zuwa 2018 tun da a kansu shi gwamnan ke tababa. Ina rokonsa da ya tausaya mana ya yi hakan.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!