Muna Maraba Da Masu Sha’awar Zuba Jari A Kafin Lemo - Hakimin Parda — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Muna Maraba Da Masu Sha’awar Zuba Jari A Kafin Lemo – Hakimin Parda

Published

on


Alhaji Usman Idris Parda, Shi ne Hakimin Parda mai shelkwata a garin Kafin Lemo, gogaggen Ma’aikacin Banki, Jajirtaccen Basaraken Gargajiya, a tattaunawarsa da Wakilinmu A Kano Abdullahi Muhammad Sheka, Alhaji Usman Idris Parda ya yi waiwaye wanda Bahaushe ke cewa adon tafiya, inda ya bayyana yadda ya gaji mahaifinsa bayan rasuwarsa, sannan kuma ya yi dogon bayani kan irin albarkatun da Ubangiji ya jibge a wannan masarauta ta Kafin Lemo. Haka kuma ya tabbatar da yin lale marhabin ga masu sha’awar zuba Jari domin amfana da wannan ni’ima da Allah ya jibge a yankin da yake shugabanta. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance.

 

Za muso ka gabatarwa da Jama’a kanka da kanka?

Alhamdulillahi ni sunan Alhaji Usman Idris Parda an haifeni garin Gatangar Warji dake karamar Hukumar Warji a Jihar Bauchi cikin Shekara ta  1967, na fara da karatun Allo kasancewar ban samu shiga karatun ilimin zamani da wuri ba.  Bayan na samu abinda na samu na shiga makarantar firamare, nayi sakandire har kuma na samu shaidar diploma, daga nan na fara aiki da wani Banki a matsayin akawu, wanda nayi aiki na tsawon shekara biyu daga 1978-1989. Daga nan sai na wuce zuwa Jami’ar Maiduguri inda na samu digiri na na farko.  Na gudanar aikin yiwa kasa hidima a wani banki a Jihar Kaduna, wanda sai da na kai mukamin Akanta har kuma na zama  Manajan darakta.

 

Kasancewarka gogaggen ma’aikaci ya aka tsinci kai a harkar sarautar gargajiya?

Kamar yadda aka sani mahaifina na gada kasancewarsa Dagacin wannan gari  na Kafin lemo, bayan rasuwar Mahaifina  kamar yadda na ambata da farko alokacin shi ne dagacin Parda har kuma Allah ya karbi rayuwarsa, hakan tasa al’ummarmu suka matsa cewar sai na dawo na gaji mahaifin nawa, bayan na dawo ne  aka nada ni amatsayin dagacin Parda a shekara ta 1998. Bayan nan ne kuma alokacin mai girma  Gwamna Malam Isah Yugudu ya shirya samar da karin masarautu, Allah ya kaddara akayi wannan masarauta dana ke rike da mukamin dagaci, aka daga likkafar ta ta koma Kasar Hakimi wanda aka nada ni amatsayin Hakimin Parda mai shelkwata a garin Kafin Lemo,  Mukamin da na ke rike dashi har zuwa wannan lokaci.

Kamar yadda aka sani harkar sarauta bata da dadi tana da wahalar gaske. musamman kasancewar yadda al’ummar mu ta ke, idan akace kai ne shgabansu komai suna dora shi akanka, sun yarda kuma sun aminta da cewa kai ne zaka aiwatar da duk wata sabgar jagoranci na yau da kullum. Sun damka  wannan amana wadda dole idan kana bukatar gamawa lafiya  sai ka jajirce tare da sadaukar da kai da kuma tabbatar da rikon amanar da suka damka ahannun ka. Idan kayi haka ina tabbatar da cewa zaka ji saukin gudanar da harkokin jagoranci cikin nasara. Saboda haka matukar ka dauki sarauta da sauki tafi komai sauki. Komai ya na da tsari idan ka ga matsala to kaucewa tsari akayi.

 

Kamar yadda labari ya bayyana wannan masarauta ta Kafin Lemo akwai albarkatun kasa masu yawan gaske da Allah ya horewa wannan yanki,  shin ko Mai girma Hakimi zai dan gutsurawa mai karatu wasu daga cikin wadannan ma’adanai da ke shimfide a wannan yanki?

Alhamdulillahi Kamar yadda aka sani shi arziki na Allah ne kuma alhamdulillahi Allah ya kwararawa wannan kasa albarka daga sama, saboda haka Allah bai saukar da wannan albarka don mu kadai ba, Muna kara yiwa Allah godiya da ya hore mana wannan arziki, kuma lale marhabin da duk wanda ke bukatar zuwa domin hada karfi damu wajen amfana dashi, musamman bisa tsarin dokar kasa da kuma tsarin masarautun mu.

Allah cikin ikonsa ya hore mana magudanun ruwa wanda hakan ya bamu damar samun sukunin gudanar noman rani da na damina. Ta fuskar noma Allah yasa muna da kasar dake karbar duk wani irin shuka idan kazoo kafin lemo zai fita, yanzu haka cikin gidana akwai kwakwar manja, wanda muke ganin sai kaje kudancin kasar nan ake samunta, Dubi yadda auduga ta ke a wannan yanki, Ridi, Gyada, rake, albasa da sauran kayan amafanin gona, wannan duk sun ta’allaka da wadatar ruwan da muke dashi. Muna da Fadamu gamu da isasshen tuddai da kuma Jigayu.

Allah ya horewa wannan kasa ta Kafin Lemo wani Dutse wanda ya taso tunda daga Gwaram ya ratsa ta Warji, ya wuce Ningi ya biyo ta Kafin Lemo ya wuce har zuwa Karamar Hukumar Doguwa a Jihar Kano.A cikin wannan dutse anyi ittifakin akwai Tantalizer, Kuza, Zinare, Tawalin wani sinadarin hada Maganunuwa, akwai dutsen kawa da aka fi sani da (Iron), duk wadanan an tabbatar dasu. A binciken da ala gudanar  bayan auna wadanan albarkatu dake karashin wadannan duwatsu idan kayi arewa  har zuwa Kazaure  zinare ne akwance a karkwashin kasa.

Sai kuma wadatattun dazuka wanda ke bayar da kyakkyawan yanayi ga makiyaya, hakan tasa muke da isasshen nama da kuma nonon da ake amfani dashi a sassan kasar nan, kuma alhamdulillahi yanzu ana kara samun kwanciyar hankali, muna ta kokari jawo hankalin masu sha’awar zuwa jari a duk bangaren da suke da sha’awa cikin abubuwan da na bayyana, ashirye muke mu yi masu jagora ga hukumomin da abin ya shafa domin cika dukkan ka’idar da aka gindaya a hukumance. Saboda haka kofarmu a bude ta ke arziki Allah ya yishi ba don mu kadai ba.

 

Kamar yadda aka sa ni kowacce al’umma na da irin nata tsarin, shin ko ya al’ummar Kafin Lemo suke ta fuskar karbar Baki?

Alhamdulillahi Mutanen mu wayayyu ne, wannan tasa zaka yi mamaki yadda masarautar Parda ta hade al’ummun arewacin kasar na baki daya, ka ga dai saboda kyakkyawar mu’amilla anan garin akwai unguwa guda ko na ci gari guda Daurawa, Katsinawa, Zamfarawa wadanda hakar Kuza ya kawosu har suka zama ‘yan gari. Bari kaji babban abin ta’ajibin har Garin Ghana muke dashi anan, kuma jama’ar kasar Ghanan ne a wurin muna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna unguwa guda ke garesu. Ga kuma Nasarawa da Barnawan Kafin Lemo.

Saboda haka mu anan ba mu san wani abu kabilnaci ko sabanin a harshe ba, kowa zaune muke dashi lafiya, wannan tasa aduk lokacin da na hangi wani al’amari da na tabbatar da zai amfani al’umma ta bana kasa guiwa a tsaye na ke, kuma alhamdulillahi ina samun cikakken goyon bayan jama’ar da na ke shugabanta,

 

Ba za a  rasa wata matsala da wannan yanki ke fama da ita ba, ko Mai girma Hakimi zai dan bayyana wasu daga cikin matsalolin?

Gaskiya mu a wannan gari babbar matsalar mu ita hanya  da rashin wutar lantarki, duk yadda muka kai da kokari idan ana maganar hakar ma’adanai, ko fita da kayan amafnin gona  zuwa kasuwanni dole ana bukatar hanya, to ga duk wanda yasan wannan yanki na Kafin Lemo akwai wani babban tabki wanda duk mai bukatar isa wannan yanki sai ya tsallaka shi, sau da yawa idan ruwa ya kawo jama’armu na fama da matsalar fiton kayan su zuwa inda suke bukata.

Haka itama matsalar wutar lantarki lokaci ya yi da ko da masu bukatar zuba jarin sun zo zasu bukaci wutar lantarki domin amfani da injinunsu, saboda haka muna fatan hukumomin da abin ya shafa za’a gaggauta taimakawa wannan yanki ta hanyar mangance mana wadancan manyan matsalolin guda biyu. Muna da kananan asibitoci a kusa damu, amma dai idan hali ya yi akwai bukatar samar da babban asibiti a wannan tsallake domin saukaka tafiya zuwa makwabtan garuruwan da muke  kusa dasu.

 

Ya danganta take tsakaninka da al’ummar da kake shugabanta musamman ganin yadda suka amince da duk wani abu da akace kai ne ka kazo dashi?

Wallahi Amana na rike masu shi yasa suma suka rike min tawa amanar ta jagorancinsu, bana gudun jama’ata kamar yadda suma basa guduna, ko ina tare muke gudu mu kuma tsira tare.

 

Mene Sakonka na karshe ga al’ummar da kake shugabanta?

A kullum fatanmu shi ne jama’a su kara himmatuwa wajen dogaro da kai, sannan kuma a tabbatar da ganin ana samun cikakken zaman lafiya, sannan a tashi haikan a nemi ilimi, muna jadadda godiyarmu tare da rokon Allah ya karawa Sarki Ningi lafiya, musamman ganin yadda yake yin duk mai yiwuwa wajen ganin al’ummar kasarnan sun samu cikakkiyar damar amfanar tsare tsaren Gwamnati.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!