Ba Rabo Da Gwani Ba… Yadda Rasuwar Hauwa Maina Ta Girgiza ’Yan Kannywood — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BIDIYO

Ba Rabo Da Gwani Ba… Yadda Rasuwar Hauwa Maina Ta Girgiza ’Yan Kannywood \

Published

on


A ranar Alhamis din da ta gabata ne masana’antar shirin finafinan Hausa, Kannywood, ta yi babban rashi sakamakon rasuwar daya daga cikin manyan jarumai mata da ke Kaduna, wato Hajiya Hauwa Maina.

Wannan rasuwa ta yi girgiza matukar girgiza masu sana’ar. Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya tattaro mu ku kadan daga cikin bayanan ta’aziyya da wasu abokan sana’arta su ka yi a lokacin alhinin rasuwar.

 

Masana’antar Shirin Fim Ta Yi Babban Rashi

– Shugaban Hadaddiyar Kungiyar MOPPAN na kasa, Malam Abdullahi Maikano

Marigayiya Hauwa Maina ta na da kaifin basira da jajircewa a wajen aiki. Hakika jarumar ta bar gibi mai wahalar cikewa, musamman ma ko da a kungiyance ne, saboda irin hidimar da ta yi, don cigaban Kannywood.

Na san ta kimanin shekara 25 da su ka wuce. Ta na da kirki kwarai da gaske, sannan mai nutsuwa ce da kamun kai. A madadin kungiyar MOPPAN, Ina mai mika ta’aziyyarmu ga ’yan uwanta, ’ya’yanta da daukacin abokan sana’arta bisa wannan babban rashi. Ina rokon Allah Ya gafarta kurakurenta, Ya sanya aljanna makoma.

 

Mun Yi Babban Rashi

-Shugaban Kungiyar Jarumai, Malam Alasan Kwalle

Allahu akbar! A madadin kungiyarmu ta jarumain Kannywood, mu na mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalai da abokanmu da ’ya’ya da ’yan uwan Hajiya Hauwa Maina. Allah Ya ji kan ta, Allah Ya sada ta ga Manzon rahama Muhammad bin Abdullah (SAW). Amin Ya Allah.

 

Za A Yi Begen Rashin Ta A Lokeshin

-Shugaban MOPPAN na jihar Kano, Alhaji Kabiru Maikaba

Hauwa Maina mai hakuri ce da sanin yakamata, ga ta kuma da dattaku. Bugu da kari, Allah Ya yi ma ta baiwa ta iya bayar da shawarwari a lokeshin lokacin da a ke daukar fim, musamman idan ta ga wani gyara. Ba na manta irin shawarwarin ta rika ba mu a lokacin daukar fim din Ladidin Baba.

Ta na sanya wa lokeshin ya zama abin sha’awa da jin dadi, saboda iya mu’amularta da mutane. Ta iya tafiyar da na kasa da ita, sannan kuma ta iya biyayya ga na gaba da ita. Tabbas gabadayan masana’antar za ta yi rashin gwarzuwa irin Hauwa Maina. Allah Ya ji kan ta da rahama.

 

Ta Rasu A Lokacin Da Kannywood Ke Bukatar Ta

–Shugaban Kwamitin Tuntuba Na Kannywood Banguard, Alhaji Ibrahim Mandawari

Allah ya ji kan Hauwa Maina, Allah ya ji kanta da rahama, amin. Babu shakka Kannywood ta yi babban rashi ta fannoni da dama, domin kuwa ta rasu a lokacin da wannan masana’anta ke matukar bakatarta. Ta fuskar acting, Hauwa ta kai kololuwa wajen gwanintar iya aktin, domin kuwa ko a fim dinta na karshe da ya fito, wato Hangen Nesa, za a ga yadda kwarewarta ta bayyana.

Sannan a fuskar kiyaye mutuncin wannan sana’a tamu, Hauwa ba ta wasa da sana’ar shirin fim, domin kuwa da wahala furodusa ya yi kuka da ita matukar ya na da tsari a cikin aikinsa. Kazalika, Hauwa ta iya zama da mutane, musamman a lokeshin, domin da wahala a sami sabani da ita a wajen daukar shirin fim da wani jarumi ko jaruma ko ma’aikata.

Hauwa Maina muzakkara ce ko na ce mace mai kamar maza, domin kuwa ko a Indiya zan iya tunawa yayin da a ke koya ma na aiki da kyamara irinta sinima, ita ce ta fara tunkarar kyamarar  yayin da malamin namu ya ce wa zai fara gwada dora kyaramar a kan tripod.

Ni a karan-kaina tun da na fara aktin ban sami jaruma da na ke so a hada mu aiki ba sama da guda uku; wato Hauwa Ali Dodo (Biba) da ita Hauwa Maina da kuma wata jaruma da ta rage a wannan industry a yanzu.

Na fara aktin da Hauwa Maina a cikin wani shiri da a ka shirya a Zaria kimanin shekaru 15 da su ka wuce, inda daga nan na gamsu da kwarewarta. Na yi shirin Mushakata da ita bayan dawowarmu daga Indiya, inda na je har Kaduna na yi hira da ita (In sha Allah zan fito da shirin zuwa can gaba, domin a ji kalmomin da ta fada).

Ko a shirin Hangen Nesa din can da na fada, Hauwa ta yi wasu kalmomi wadanda ta ke nuna kamar lokaci ya taho inda ta ke cewa “me ya sa ba ma tunanin komai sai duniya, duniya, duniya, ba ma tunanin lahira?”

To, Allah Ya ji kan Hauwa da gafara Ya sa Aljanna makoma, amin.

 

Advertisement
Click to comment

labarai