Jarumin Sarki: Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu III — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MAKALAR YAU

Jarumin Sarki: Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu III

Published

on


08148507210   mahawayi2013@gmail.com

Mai karatu barkanmu da warhaka, barkanmu da saduwa a wannan shafi mai matukar ilmantarwa. In Sha Allah zan kasance mai ci gaba da rubutu a wannan shafi domin bayar da tawa gudumawar wajen wayar da kan jama’ a a wasu abubuwan da ka iya tasowa, inda in Allah ya yarda  za mu rinka yin bayanai game da batutuwa daban-daban, wadanda za su kasance masu amfani gare mu, da kuma ci gabanmu ta hanyoyi da dama.

A wannan makon, wanda yake kuma shi ne karo na farko, za mu yi wani dan takaitaccen bayani ne a kan Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dakta Abubakar Shehu Abubakar III, wanda  Allah ya yi ma Sarauta yana da kananan shekaru, sakamakon rasuwar mahaifinsu, Alhaji Shehu Abubakar.

Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dakta Abukakar Shehu Abubakar lll, wanda al’ummar suke yi masa lakabi da mai ‘horon a bi Allah,’ ko kuma  ‘jarumin wannan lokacin.’ An haife shi a ranar 17 ga watan Nuwambar  shekarar  1977 a cikin jiharsa ta Gombe.

An sanya shi a makarantar Firamare da ke jihar Gombe daga shekarar 1982 zuwa shekarar 1988. Daga nan ya wuce zuwa makarantar Sakandare ta  kimiyya da ke cikin jihar Gombe daga shekarar 1989 zuwa shekarar 1995. Mai martaba Abubakar Shehu ya samu babban Digiri dinsa a fannin nazarin siyasa daga Jami’ar Maiduguri, daga shekarar 2001 ya kuma kammala a shekarar 2005.

Kafin a nada shi Sarki, ya yi aiki a wurare daban-daban , inda ya rike mukamin Kansilan sanya ido a Karamar Hukumar Gombe daga shekarar 2006 zuwa shekarar  2007.

Bugu da kari, daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2009, mai martaba Dakta Shehu Abubakar ya rike mukamin mataimaki na musamman na  Darakatan gudanar da mulki a Ma’aikatar Tsaro ta kasa da ke birnin tarayyar Abuja, inda daga baya kuma ya zama shugaban Kamfanin Kliptown Lagoon Nijeria, inda daga baya kuma ya rike mukamin babban Darakta na kamfanin ‘Horizon Interlinks Global Resources.’

Mahaifinsa, Marigayi Shehu Abubakar shi ne Sarkin Gombe na goma, kuma ya rasu yana da shekaru 76, inda kuma bayan rasuwar mahaifin nasa, a ranar 27 ga watan Mayun shekarar 2014 sai Alhaji Dakta Abukakar Shehu aka tabbatar masa da sarautar Sarkin Gombe, inda ya zamo Sarkin Gombe na goma sha daya.

Sakataren Gwamnatin jihar  Gombe a wancan lokacin, Abubakar Bage ne ya mika wa Dakta Abubakar wakisar tabbatar masa sa Sauratar Sarkin na Gombe Gombe a babban Masallacin Juma’a na garin a ranar shida ga watan Yunin shekarar 2014.

Wani abin sha’awa ga wannan bawan Allah shi ne, tun daga lokacin da ya zama Sarkin Gombe yau kusan shekaru uku da wani abu ke nan, bai ajiye irin ayyukan alkhairin da mahifinsa yake yi wa al’ummar jihar Gombe ba,musamman talakawa, inda ya dora akan kyawawan ayyukan da mahaifin nasa yake yi na, musamman na gudanar da ayyukan jin kai ga daukacin al’ummar jihar.

Mai martaba Dakta Abubakar Shehu yana jan kowa a jiki, ba ya nuna wa kowa kyama, inda hakan ta sanya daukacin al’ummar jihar a kullum suke nuna matukar jin dadinsu ga wadannan halaye na matashin Sarkin.

Bugu da kari, irin wannan tausayawar da yake yi wa al’ummar jihar ne ya sanya ya samu lambobin yabo iri-iri. Misali, a kwanan baya aka karrama shi da lambar yabo ta girmamawa daga kungiyar ci gaban Matasan jihar Gombe (GYPN).

Wani abin sha’awa kuma, wanda yake matukar jawo masa farin jini a tsakanin jama’arsa, a kullum Dakta Abubakar yana da burin ya ga an samu zaman lafiya a tsakanin al’ummomin jihar, inda yake yawaita kiraye-kirayen kowa ya zauna lafiya da juna.

Jerin sunayen Sarakunan da suka mulki Gombe a tarihi akwai, Abubakar “Buba Yero” Dan Usman Subande, wanda ya yi mulki a tsakanin shekarar 1804-1841. Sai kuma Sulaymanu Dan Abubakar daga shekarar 1841-1844. Muhammadu Kwairanga Dan Abi Bakar 1844-1882. Abd al-Kadiri Zaylani dan Muhammadu 1882-1888.

Sai kuma Hasan dan Muhammadu 1888-1895. Akwai kuma Tukur Dan Muhammadu, wanda ya yi Sarkin Gombe daga shekarar 1895-1898. Jalo dan Muhammadu daga 1898-1898. Umaru Dan Muhammadu 1898-1922. Haruna Dan Umaru 1922-1935. Sai kuma Abu Bakar Dan Umaru, wanda yay i Sarkin Gombe daga watan Janairun 1936 zuwa Janairun 1984. Sai kuma mahaifin Sarkin na yanzu, Alhaji Shehu Usman Abubakar, wanda ya hau mulki a watan Janairu, a wani kaulin kuma watan Agustan 1984 zuwa Mayun 2014. Sai kuma Sarkin Gombe na yanzu, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, wanda ya hau karagar mulki a watan Yulin shekarar 2014

An haifi Alhaji Abubakar Shehu ne a ranar 17 ga watan Disambar 1977 a cikin garin Gombe. A fara karatunsa a makarantar Firamare ta ‘Gombe Children Primary School,’ a tsakanin 1982 zuwa 1988. Daga nan ya je Kwalejin kimiyya ta gwamnati da ke Gombe a tsakanin 1989-1995. Ya kuma halarci Jami’ar Maiduguri daga shekarar 2001-2005, inda samu Digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa.

Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar ya yi ayyuka, inda ya fara da zama Kansila a Karamar Hukumar Gombe, a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2007. Daga kuma ya zama mataimaki na musamman ga Darakta mai kula da harkar mulki a ma’aikatar tsaro ta kasa da ke Abuja daga 2007 zuwa 2009.

Haka kuma Sarkin ya zama Shugaban kamfanin nan na ‘Kliptown Lagoon Nigeria Ltd.’ Ya kuma zama Darakta na kamfanin ‘Horizon Interlinks Global Resources.’

 

Advertisement
Click to comment

labarai