APC Ta Yi Wa Ali Modu Sheriff Kyakkyawar Tarba A Borno — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

APC Ta Yi Wa Ali Modu Sheriff Kyakkyawar Tarba A Borno

Published

on


Tsohon gwamnan jihar Borno, kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta kasa, Sanata Ali Modu Sheriff ya samu gagarumar tarbar kusoshi da magoya bayan jam’iyyar APC, a birnin Maidugurin jihar Borno, biyo bayan ayyana aniyar sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

A cikin jawabin da Sanata Modu Sheriff ya gabatar, a taron masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da sauran magoya bayan ta, a bukin sauya shekar tasa, a ranar Jumu’a, a gidan gwamnatin jihar Borno. Wanda aka  tsammaci Shariff zai yi tsokaci kan abubuwan da suka faru a baya, amma sai ya karkata akalar zancen sa a kan hadin kai, lalubo hanyoyin samun dawamamen zaman lafiya da bunkasa jihar.

Sheriff, wanda yake zaune kusa da Gwamna Shettima, inda ya mike tsaye tare da yiwa sauran jama’ar da ke zauren taron gaisuwa ta musamman, sannan ya bayyana cewa ya yafe wa duk wanda ya yi masa wani laifi, kuma ya sa kafa ya take abinda ya wuce.

“yau rana ce ta hadin kai; na yafe wa duk wanda ya muzguna min, kuma zan so a nan in bayyana a fili karara cewa, ba zan yi la’akari da abubuwan da suka faru a baya ba- abinda ya wuce ya riga ya wuce.” Inji shi.

“yanzu babban abinda ya fi dacewa mu dauka da muhimmanci a gare mu shi ne, ta yaya zamu habaka jihar mu ta Borno, wannan shi ne lokacin da ya dace mu sake gina Borno.”

“a baya na bar wannan jam’iyya zuwa PDP matsayin dan jam’iyya tamkar kowa, wanda daga bisani na kasance shugaban ta na kasa. A bisa gogayya da kwarewar da nake da ita, a lokacin da nake shugaban PDP na kasa, jihohin da suke da masu jefa kuri’a da yawa, sun fi samun tagomashin gwamnatin tarayya”.

“dole mu kula da wannan, kuma tun da wuri kamata yayi mu farka, mu yi tururuwa wajen zuwa cibiyoyin da ake rijistar katin zabe, saboda haka ta wannan yanayin ne zamu yi ruwan miliyoyin kuri’u ga dan takarar shugabancin kasa a zaben 2019”. Inji Modu.

A jawabin gwamnan jihar Borno Kashem Shettima, ga kusoshin jam’iyyar, wanda da fari ya bayyana matukar jin dadin sa dangane yadda Ali Modu Sheriff tare da sauran wadanda suke mara masa baya wajen sake dawowa APC, ya ce wannan abin mutuntawa ne.

Bugu da kari kuma, ya ce jam’iyyar ba zata taba lamunta da hawan-kawara ko kama-in-keta daga wani dan takara ba, musamman a daidai lokacin da jam’iyyar ke kokarin gudanar da zabukan shugabanin jam’iyyar a matakin unguwanni da kananan hukumomin ba.

Yau kusan shekaru bakwai ana zaman doya da man ja tsakanin Gaamna Kashem Shettima da maigidan sa- Sanata Ali Modu Sheriff, wanda sai a cikin yan kwanakin nan ne, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya sasanta tsakanin kusoshin, a wani zaman sulhu; wanda ya hada har da Kashim Imam da Babagana Kingibe, a Abuja.

 

Advertisement
Click to comment

labarai