Jam’iyyar PDP Ta Yi Kyakkyawan Tanadi Don Mata (I) -Halima Kajuru — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Jam’iyyar PDP Ta Yi Kyakkyawan Tanadi Don Mata (I) -Halima Kajuru

Published

on


HAJIYA HALIMA YUNUSA KAJURU, ita ce Shugaban mata na Jam’iyyar PDP sashen Arewa maso Yammacin kasar nan, wanda ya kunshi, Kaduna, Kano, Katsina, Zamfara, Sakkwato Kebbi da Jigawa. A wannan tattaunawar da ta yi da wakilinmu, UMAR A HUNKUYI, a Ofishinta da ke Kaduna, ta fara ne da bayanin rashin katabus din Jam’iyyar da ke mulki yanzun ta APC, sannan ta yi tilawar tulin ayyukan alheran da gwamnatin baya ta PDP ta aiwatar a kasarnan, inda ta karkare bayanan na ta da yi wa Mata albishir kan tanaje-tanajen abin alheran da Jam’iyyar ta PDP ta tanadar masu matukar suka sake mayar da ita kan karagar mulkin kasarnan kamar dai yadda matan suka sharbani romon Dimokuradiyya a wancan karon da Jam’iyyar ta PDP ke mulki. A sha karatu lafiya:

Me za ki ce kan shekaru uku da dori na mulkin Jam’iyyar APC?

Bisimillahir Rahmanir Rahim. To duk dai dan APC in ka tambaye shi ko akwai wani abu da suka tabuka a cikin shekarun nan uku da doriya, amsar da zai ba ka ita ce, sun samar da tsaro da kuma hana cin hanci da rashawa, wannan dai shi ne suke kamfen a halin yanzun. Wanda a zahiri, shi wannan tsaron wanda dama can tun farko da shi suka yi farfagandar kamfen har suka ci zabe, yanzun kuma har suke tutiya suna riya cewan sun samar da shi, wanda a zahiri sam babu shi.

Iyi an samu raguwan tashin bamabamai a wasu wurare, amma kuma yanayin mulkin na su ya haifar da wasu sabbin hanyoyin na rashin tsaron. Can a baya a nan Arewa mu ba mu san wani abu wai shi garkuwa da mutane ba, amma yanzun abin da muke jin shi a can kasan kudu, yanzun ya dawo mana a nan Arewa, wanda su na su ma a can kudun sai ka fita ne suke tare ka, sai da muka koya masu a zo har gidanka a buga maka kofa ka bude a yi awon gaba da kai, ko a kwashi matanka da ‘ya’yanka an ta fi da su kenan. Sabanin tashin bamabamai, wanda yake aukuwa a wasu sassa, wannan ya zama ruwan dare gama duniya. In a mota kake tafiya baka tsira ba, in kana gida ma ba ka tsira ba, da zaran kana tafiya ka ga wata mota ta wuce ka sai gabanka ya fadi, saboda tsoron in ba a sace ka ba, ana ma iya kashe ka,don haka ina maganan cewa an samar da tsaro a nan.?

Sannan kuma maganan yaki da cin hanci da rashawa da suke yi, har yanzun fa ba mu ji an ce yau ga shi an kama wani ya cinye kudi an kwace kudin an kai shi kotu an hukunta shi ga shi can ana tsare da shi a kurkuku ba. wanda idan da a ce sun yi hakan, zai iya zama darasi ga saura ta yanda in ma an ce wani ya ci dukiyar talakawan ma ba zai ci ba, to ba a yi wannan ba, ba abin da aka yi, sai kururuwa suke ta yi, abin ya zama tamkar waka a bakin su amma in ka laluba ba abin da aka yi.

To idan da za su lura da hakan, su kuma gane ma sun ci zaben don ni ina ganin har yanzun su ba su ma yarda da cewa sun ci zaben ba, to da za su gane hakan, da sai su tsaya su yi wa jama’a aikin da aka zabe su domin shi. Ga dai babu wasu ayyukan a zo a gani da suka yi, ga rashin aikin yi da ya addabi mutane, ga dai abubuwa nan tuli tari sun kasa aiwatar da komai sai hayaniya a shekarun nan sama da uku da suka yi kamata ya yi a ce sun ci karfin ko da abu guda ne amma sam ba wani abin da suka iya aiwatarwa.

 

Wace riba kike ganin mata sun samu a gwamnatin PDP wacce kike ganin ba su same ta ba a wannan gwamnatin?

Mata sun taka mahimmiyar rawa a lokacin gwamnatin PDP, hakanan ita ma gwamnatin ta PDP ta taka masu mahimmiyar rawa. A wancan lokacin na mulkin Jam’iyyarmu ta PDP, kama daga kan Uwargidan Shugaban kasanmu har ya zuwa matan gwamnonin mu, duk sun bude ayyuka da kuma hanyoyi kala-kala wadanda matan suka ci gajiyar su. Mata a wancan lokacin sun karu ta misali a koya masu sana’a, a kuma ba su jari, an kuma ba su mukamai manya-manya har ma da kananan tamkar takwarorin su maza.

Misali a nan, ni a karamar hukuma ta da na fito, watau Kajuru, Mace mawuyaci ne a baya can ta iya zama kansila in ana zabe. sai muka sami matar gwamnan mu na PDP a wancan lokacin muka ce ma ta, to ko a mukaman nan na rikon kwarya da ake sanyawa, a daure a sanya mata mana. Muka ko yi sa’a, ta yi wa mijinta magana, ya kasance a duk karamar hukumar da aka nada kansiloli hudu sai da aka sanya mace guda. Don haka take a lokacin, sai da muka samu mata 23 a nan Jihar Kaduna sun yi kansila. A mataki na tarayya kuwa, Shugaban kasa ya baiwa akalla mata takwas mukaman Ministoci. An kuma baiwa matan mukaman shugabancin manyan ma’aikatun gwamnati da dama, ba kuma wata Majalisar da za ka je, in ka debe kamar irin su Kano haka, sabili da al’adunmu da kuma Addini, amma duk Majalisunmu akwai mata a cikin su. Amma hatta a nan Kaduna, a kan sami mata uku har ma hudu a Majalisa, amma yanzun fa? Ai ka ga babu mace ko da guda a cikin majalisa. Sam mata ba su da murya ba kuma su da wakilci a cikin majalisa, ba mace wacce ta san wane hali ne mata ke ciki ballantana ta taimake su, don haka matan ke shan wahala matuka a wannan gwamnatin. Ba wani abin da ake yi masu ko da kuwa da sunan tallafi ne, su dai suna nan a cikin gida kawai ajiye.

Sun ta fi sun bar mata a baya, amma dai mu a PDP muna nan tare da mata, hatta wannan zaben na kananan hukumomi da za a yi a Kaduna ranar 12 ga wannan watan, a shiyyan da na fito kadai, watau shiyya ta biyu, sai da muka yi kokari muka tabbatar da cewa mata har uku sun ci zaben fidda gwani a cikin Jam’iyyar mu, biyu a Chikun daya kuma a Kajuru, da kuma izinin Allah da karfin kuri’ar da za mu jefa masu za su lashe zabukan na su.

Advertisement
Click to comment

labarai