Hukumar Kiyaye Hadurra A Zariya Ta Shawarci Masu Tafiye-Tafiye — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Hukumar Kiyaye Hadurra A Zariya Ta Shawarci Masu Tafiye-Tafiye

Published

on


Saboda yawan hadurra da suke faruwa a hanyoyin da suka tashi daga Zariya, jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa da suke kula da shiyyar Zariya, sun nuna matukar damuwarsu na yadda ake hadurra, a kuma rasa rayuka, a karshe,a rasa yadda za bi a gano ‘yan uwan gawarwakin da

suke rasuwa a dalilin hadurran.

Babban jami’an hulda da jama’a na hukumar mai ofishi a Zariya, Alhaji Yahaya Idris ya bayyana wannan damuwa a zantawarsa da manema labarai a Zariya.

Alhaji Yahaya Idris ya ci gaba da cewar sau da yawa in Asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na yajin aiki, in an yi hadari, ya kai ga an rasa rai ko kuma rayuka, su kan rasa inda za su kai gawar wanda ko kuma wadanda suka rasu, kuma,kamar yadda ya ce ba abu ne da za su aje gawar a filin asibitin su ta fi ba.

Kan haka, Alhaji Yahaya Idris ya shawarci ma su hawa motocin haya da kuma ma su motocinsu na kansu, da a duk lokacin da za su yi tafiya, su rika daukar wata takardar shaida da za ta kunshi sunansu, da adireshinsu da inda suka fito da inda za su da kuma lambar wayar wani ko wata da za a iya tuntuba, ko da wata matsala ta faru, jami’an hukumar kiyaye hadurra za su sami saukin gano yadda za su yi da gawarwakin da aka samu a duk hadari ko kuma hadurran da suka faru.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kiyaye hadurra a shiyyar Zariya ya kara cewar, wadannan matsaloli da suke fuskanta ba a motocin haya suke samu kawai ba, suna samu a motocin da ba na haya ba daga lokaci zuwa lokaci.

Idan sun sami wannan matsala a lokutan da Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ke yajin aiki, kamar yadda ya bayyana a baya, su kan tuntubi kantomomin kananan hukumomi da suke shiyyar Zariya, na yadda za a yi wa gawa ko kuma gawarwakin da aka samu, kuma kamar yadda Alhaji Yahaya y ace, kantomomin na bayar da gudunmuwar duk da ta dace, a kan lokaci, sai dai a kwai wasu tsare-tsare da ake yi rundunar ‘yan sanda, kafin a yi wa gawar ko kuma gawarwakin sutura.

Duk da haka, ya kuma nuna matukar damuwarsa da yadda ‘yan kasuwa ke baje kayayyakinsu a kan hanyoyi, musamman a bakin kasuwar Tudun wadan Zariya da P/Z da kuma sassa da dama na kasuwar Sabon garin Zariya, mafiya yawan lokuta, a cewar Alhaji Yahaya ya ce, su kan tuntubi jami’an karamar hukumar Sabon gari ko karamar hukumar Zariya, domin daukar matakan da suka dace, domin rage matsalolin da suke faruwa a wadannan wurare da aka ambata.

A dai zantawar da wakilinmu ya yi da Alhaji Yahaya Idris, ya koka na yadda aka bar wani wajen ratse na motoci a P/Z, kamar yadda ya ce, ya dace a toshe wannan waje, domin ya na kawo matsaloli ga motocin da suke juya wa a wajen.

A karshe, Alhaji Yahaya Idris, ya nuna matukar jin dadinsa da yadda ma su abubuwan hawa ke ba su goyon baya da hadin kai, a duk lokutan da suka tashi aiwatar da wasu ayyuka da kuma yadda ake ba su labarin faruwar hadurra a sassa daban-daban na Zariya, ya ce, ya na fatan hakan zai ci gaba, domin rage faruwar hadurra a wannan shiyya baki daya.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai