Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yadda Tsawa Ta Kashe Min ‘Yan Uwa Uku’

Published

on

Wata matar aure mai suna Henrietta Anthony, ta bayyan yadda tsawa ta hallaka ‘yan uwanta su uku da ake kira  Aisha Useni da Felicia Istifanus da Istiah James a loacin da sandar sadaewa mallakar kamfanin sadarwa na telecommunications ta dado masu a Jalingo cikin jihar Taraba a ranar safiyar Asabar data gabata.

Kimanin mutane biyar suka mutu, inda kuma mutane da dama suka samu raunuka sakamakon tsawar.

Tsawar ta kuma rusa gidaje da dama da ofisoshi da makarantu da wajajen shakatawa na jami’I da sauran su.

Shugagaban kwamitin bayar da shawara akan kiwon lafiya dake asibitin kwararru na jihar Taraba Dakta Dashe Dasogot, ya shedawa kafar dillancin labarai na kasa cewar mutane biyar da suka rasa rayukan su an kawo asibitin an kuma ajiye gawarwakin su a dakin ajeye gawarwaki na asibitin.

Dasogot ya ce, mutane biyu da suka samu raunuka ana kan yi masu magani a dakin bayar da gaggawa na asibitin, inda kuma mutane hudu suka mutu a lokacin da tsawar ta auku mau a kusa da kofar asibitin mu daya kuma daga cikin gari aka kawo shi.

Wata ganau uwargida Henrietta Anthony, ta shedawa kamfanin dillancin labarai na kasa cewar, ‘yan uwan ta uku Aisha Useni da Felicia Istifanus da kuma Istiah James suna daga cikin wadanda suka mutu.

Matar wadda take da gidan sayar da abinci daura da kofar asibtin ta ce, ‘yan uwan nata sun baro gida da wuri don zuwa gidan abinci aiki a lokacin da lamarin ya auku.

Ta ci gaba da cewa, sun kammala girki sun kuma shirya tsaf, don fara sayar da abincin da kimanin karfe 6:00 na safiyar ranar a lokacin da tsawar ta fadowa karfen kamfanin sadarwar harda su da kuma wani da ya zo sayen abinci da wani direban kwamishinan ma’aikatar ruwa Mista Emmanuel Gowon, da ya zo sayen abinci, inda ya mutu nan take kuma wata mai shago mai suna Konah Danjuma itama ta samu rauni a kafada da kai.

Shima Daraktan sadarwa na majami’ar Diocese dake Jalingo, Babban Rabaran John Jerome, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na kasa cewar, wani malami na St. Thomas dake a jami’ar jihar Taraba dake Jalingo, Babban Rabaran  Pontianus Jaffla da daliban jami’ar su bakwai suma sun samu raunuka.

Jerome ya ce, malamin da daliban tsawar ta rutsa dasu ne a lokacin suna gunar da ibada a lokacin da ginin cocin ya rushe.

Acewar sa, Pontianus ya samu raunuka a kanshi an kuma yi masa mahani a asibi mallakar gwamnatin tarayya dake Jalingo, inda daga baya aka sallamo shi.

Ya kara da cewa, daya daga cikin daliban anyi masa magani an sallamo shi, amma sauran shida har yanzu ana yi masu magani a asibitin.

In ba a manta ba, kwanan baya kafar dillancin labarai ta kasa, ruwan sama na farko a Jalingo a cikin sati biyu da suka shige, yana tafe ne tare da tsawa, inda har tsawar ta bannata wasu kaya musamman a jama’ar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: