Idan Aka Sa Kwarewa Wurin Gine-Gine, Za A Samu Wadatar Gidaje A Nijeriya –Masana — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Idan Aka Sa Kwarewa Wurin Gine-Gine, Za A Samu Wadatar Gidaje A Nijeriya –Masana

Published

on


Masana a bangaren gine gine idan aka bullo da wasu hanyoyi dangane da hakan, za a samu ci gaba da zai sa, ayi bankwana da matsalar da ake fuskanta ta rashin isassun gidaje..

Masanan sun bayyana hakan ne a Lagos lokacin baje kasuwar koli ta bangaren gidaje, cewar bayan maganar jin dadi, ginin gidan da ya amsa sunan shi, zai sa wanda ya mallake shi ya, samu ragowar kudi, wabanda idan babu kyakkyawan tsari, sai ya kashe su

Tsohon shugaban cibiyar injiniyoyi na kanikanci reshen jihar Lagos, Mrs Funmi Akingbagbohun, ya bayyana abinda ake nufi da smart building, shi gida ne wanda duk muhimman abubuwa da kuma kaddarori, kamar su na’urar sanyaya daki, chillers, boilers, da kuma lighting, ga kuma sadarwa tsakanin wani inji da wani. Sai kuma masu kula da shi gidan yadda za a dade ba asamu wata matsala ba.

Akingbagbohun ta kara jaddada cewar shi smart building na daya daga cikin wasu al’amura takwas, dangane da birane masu birgewa, ana bukatar ace sun samar da ko kuma sun kunshi, abubuwa bakwai saboda kasuwar birane a shekarar 2025, bai kuma kamata ace Nijeriya an barta a baya ba.

Ta bayyana cewar ‘’Babbar manufarsmart building shine yin ayyukan da suka kamata wadanda za ayi ma wadanda suke zama cikin gidan, su ji dadai akan ‘yan kudade kalilan, ga kuma yadda muhallin yake cikin, saboda duk yana samar da duk wasu abubuwan da suka kamata, tare da mafani da da tsafatatacciyar hanyar samar da duk wasu abubuwan da ake so.

Akingbgbohun ta kara jaddada cewarb ‘’Majalisar dinkin duniya tana sa ran yawan al’ummarduniya zai karu da kusan, mutane bilyan 2 da milyan 500 daga yanzu zuwa shekara ta 2050. Wannan kuma zai sa yawan mutane su karu a birane da kusan kashi biyu bisa uku, duk wadannan mutane suna son sababbin gidaje, da gine gine na wuraren da za su zauna su yi aiki.

‘’Da wadannan ire iren yawan gine ginen da muke son yi wadanda suke gabanmu, dole ne mu samu hanya wadda zata taimaka mana, bada bata lokaci ba, karuwar wani abu ba shi bane, muna bukatar canji, wanda a hankali yake samuwa, wannan kuma maganar harkar gida sai an hada da sabon zayyanar yadda ake gina gida. Wanda ba wai kawai yana da kyau bane, amma kuma ace ya kasance da yadda muhallin namu yake.’’

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na Nijeriya da Igila Mr Akin Olawore ya bayyana cewar, masu gina gidaje a Nijeriya lokacin da suke gini, ya dace a ce sun tuna ko su tuna da ko al’ummar Nijeriya nawa ne, su kuma kasance masu kokari koda yaushe su kasance masu bullo da sababbin dabaru.

Olawore wanda shi masani ne a bangaren surbeyor da kuma baluuer wato wanda zai iya fadi farashin kayan, wanda ya wakilci Babban darektan na kungiyar ‘yan kasuwa Bimbo Afolabi, ya bayyana cewar, rashin isassun gidaje a Nijeriya, yana tsakanin milyan 17 zuwa milyan 20, na gidaje wannnan a shekaru biyar zuwa takwas ne da suka wuce, don haka ana iya samun bukatar karuwa.

‘’Al’amarin gida wani abu ne wanda mutane ya kamata su samu, suna kuma daga cikin abubuwan da kowa ke so, a jerin abubuwan da suka kamata, babban abinda ya kamata a tuna da shi, lokacin da ake shirin gina gida shine, da farko la’akari da yawan jama’a, da kuma kiyasin yadda yawan jama’a zai karu nan da zuwa wani lokaci. Idan har gida damar mallakar kowa nedon haka wannnan ya nuna ke nan da akwai aiki a gaba mai yawa wanda za a yi. Idan kuma ba a yi hakan ba, daga karshe sai a gina gidajen da basu kamata ba.

Ya ci gabada bayanin cewar manyan matsalolin da suke shafar gida a Nijeriya sun hada da yadda ake samun filin gini, rashin tsaro na yadda za a kare shi filin, rashin masu taimakawa da rancen kudi, sai kuma rashin kayayyakin gini, ga kuma maganar yadda kasuwar gidaje take, sai kuma wata matsala wadda wannan ta shafi duniya ne, abin kuma ya zama na hira nr tsakanin masana harkar gidaje da ginasu.

Ga kuma maganar yadda bukatar sauri wajen kammala gidaje, damar sayensu, yadda aka zana taswirar yadda gidan take, kudin da za abiya maginan, da kuma fasahar gini na zamani, da kuma sauransu.

Olawore ya kara jaddada cewar ‘’Idan duk aka hada wadannan gaba daya, wannan ya nuna ke ne, da akwai ayyukan yi wanda bangaren gida ke samarwa. Gudunmawar da gwamnati ya kamata ta bada a bangaren samar da gidaje, kamata yayi a samar da hanyoyin yin haka ta tsare tsare, da kuma manufofi.

Kungiyoyi masu zaman kansu da suka hada da bangaren kamfanonin samar da kudade, kayayyakin gine gine gine, masu masana’antu, ‘yankasuwa, makarantu, masu zayyana yadda za a gina gidaje, sun hada da kwararru ta bangaren gina gidaje. Da yake ana da yawan matsa dasuka wuce milyan 100 yanzu da kuma, nan gaba, akwai bukata ta a kira wani taro na masu ruwa da tsaki, a bangaren gine gine, da kuma matsalolin da aka yi magana akansu, saboda kamata yayi a samo bakin zaren.

Shima Oba na Lagos Rilwan Akiolu wanda ya shugabanci bikin bude kasuwar kolin gidaje ta Lagos, ya bayyana cewar maganar gidaje masu saukin kudi wannan maganar da ce, yanzu kuwa abin baya yiyuwa, ya dace gwamnmati ta samar da wata dama saboda ‘yan Nijeriya su sa jarinsu a bangaren gidaje.

Ya ce, ‘’Ba wata mafanar gidaje masu saukin kudi sai dai idan muna yaudarar kanmu ne, duk abinda gwamnati ya dace tayi shine, samar da abubuwan more rayuwa, kamar wutar lantarki, da kuma cikakken al’amarin tsaro, sai dai kawai idan kuma muna son mu rudi ko kuma yaudari kanmu, me nene abinda yake da arha yanzu a kasarnan? Amma idan muna da hanyoyin masu kyau, tsaro, wuta, ruwa, duk kuma wani sauran abu, na iya biyo baya, idan aka kara haraji , sai farashin komai ya karu, dagaban kuma sai mutane su fara magana.

‘’Duk wasu abubuwan da gwamnati ya kamata tayi, wanda kuma zai kasance, wasu ayyuka ne na jinkai, wato yadda mutane za su iya saye da ‘yan kudadensu kalilan, da kowa zai iya saye. Kamata yayi mutane su taimakwa gwamnati, tsakanin Lagos da Ibadan alal misali, gwamnoni uku suna iya hada kansu, su gyara dazuzzuka, su taimakwa mutane, su koma gona saboda rayuwarsu, wadannan sune kananan abubuwa wadanda za su iya taimkawa mutane saboda tattalin arziki ya inganta’’.

Shugaban kwamiti na kasuwar duniya ta bangaren gidaje, Mr Moses Ogunleye ya bayyana cewar taken shi bikin baje kolin shine ‘’Gidaje masu kayatarwa’’ an zabi hakan ne saboda masana harkokinn gidaje, su samu hanyoyi wadanda za a yi gini wanda zai dore, ba daga baya ba, abin kuma ya wargaje, amma kamata yayi a rika gina gidaje wadanda za su yikarko wato dadewa, masu ban sha’awa, da kowa zai so su.

‘’Muna shirye koda yaushe kuma mun amince a matsayinmu na ‘yan Nijeriya, dole ne mu rika tunawa da maganar kasarmu da ci gabanta, yadda zamu inganta albarkatun kasarmu, yadda za a ingantasu, yadda za ayi amfani da fasaha, su kasance sune a gabanmu.’

 

Advertisement
Click to comment

labarai