Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Evans Mai Garkuwa Ya Fashe Da Kuka A Kotu

Published

on

Shahararren mai garkuwa da jama’a Evans ya barke da kuka ya ce, sun sha bugun shi kuma basu bashi abinci.

Ranar Litinin ce aka kawo Evans ko kuma Chukwumeme a gaban babbar kotun jihar Lagos wadda ke Igbosere, inda aka kawo shi, saboda ya kara fuskantar, wasu laifuka biyu na garkuwa da jama’a.

Bayan da yaki ya sauko daga motar fursuna wadda ta dauko su, saboda ya nuna rashin jin dadin shi, daga karshe dai an gabatar da shi gaban a dakin kotu, wadanda jami’an gidan kurkuku suka shigo da shi, akan umarni mai shari’a Adebayo Akintoye.

Da aka shigo da shi dakin kotun ba tare da takalma ba a kafafun shi, an kuma sa ma shi ankwa a hannu, Eban wanda ya sa gajern wando da kuma karamar riga, nan da nan y ace ma mai shari’ar cewar yana da maganar da yake so yayi.

Ya bayyana cewar ‘’Ina da maganar dana keson nayi, tun lokacin da aka kai ni gidan kutkuku, sun yi ta mani abubuwan da basu dace ba, ba a barin a ziyarce ni, ba kuma su bani abinci sosai, ina da matsalar ido, bana iya ganin abinda ke can nesa’’.

Amma kuma nan da nan sai jami’an gidan jarun suka bada amsar shi Evans ana bashi dukkan abubuwan da ake ba fursunoni.

‘’Muna yi ma shi duk wani abinda yake so, ana kuma bashi abinci sosai, kuma mutane na zuwa ziyararshi, likita ma na zuwa yana duba shi lokaci zuwa lokaci. Ko jiya ma yazo, har ma dasafe kafin mu zo kotu , yazo ya duba shi. Saboda ya fara cewar shi bai son ya zo kotu ba, bashi da lafiya’’. Amma shi Evans ya ce, Nas ce ta gan shi’’.

‘’Amma kuma lokacin da Lokita ya duba shi jiya, ya bayyana cewar yana lafiyalau, don haka bai ga wani dalili ba, da zai hana shi zuwa kotu’’.

Shi ma mai kare  mai laifi na biyu Ogidi Ogbu, ya fadawa kotu cewar wanda yake karewa Joseph Emeka, shima yana da matsalolin da Evans yake dasu.

Sai dai darekta wadda take gabatar da masu laifi ta jihar Lagos Ms Titilayo Shitta- Bey, ta bayyana cewar Evans yana son yayi wasa da hankalin mutane  ne, ta kuma ja hankalin kotu cewar kada ta yarda da hakan.

‘’Irin haka ne ya fadawa babbar ktun Ikeja, mun rubutawa ita Hukumar kula da fursunoni, ita ma rta rubuta mana cewar ana kulawa da shi kamar dai yadda ake yi ko wanne fursuna’’.

Daga nan sai mai shari’a Akintoye yabawasu jami’an fursunan umarni na, a tabbatar ana kulawa da Evans da kuma sauran wadanda aka tsaresu tare, ana yi masu kamar yadda ake yi ma kowa. Ya kuma kara tuna su jami’an gar yanzu su Evans ba masu laifi bane, har sai bincike ya nuna jakan.

Akan bukatun Evans lauya Olukoya Ogungbeje wanda tun farko ya rubutawa kotun cewar kar a saurari shi al’amarin, sai shi mai shari’ar ya amincewa bukatun Evans

Da mai shari’a ya tashi zai tafi sai Evans ya barke da kuka yana cewar:

‘’Mutane me nene nayin maku ne, sun sha dukana, ba abinci, an kulle ni a wuri daya tun 20 gawatan Agusta shekarar data wuce, me yasa ne wannan al’amarin nawa ake yi mani tadda aka ga dama. Ya kamata in fuskanci shari’ar da ake yi mani tun ina da raina, mi yasa mutane suke son su kashe ni’’.

Daganan kuma sai lauyan shi yazo kotun yana bashi hakuri, daga karshe dai an gurfanar dasu, a wasu sababbin laifuka tare da Joseph Emeka, Linus Okpara, da kuma Bictor Aduba. A kan zargin da ake masu wadanda suka shafi ‘’Hada kai da kuma yadda suke kama mutane.

Ita dai gwamnatin jihar Lagos ta bayyana cewar su wkdanda ake zargi da aikata laifin, da wasu mutanen da suka gudu, su suka hada kai, suka kama Uche Okafor ranar 21 ga watan Nuwamba 2014 a Festac Town Lagos, suka kuma bukaci da ya basu dala milyan 2.

DPP ta bayyana cewar laifukan sun sabama sassa na 409 da kuma 269 na dokokin jihar Lagos na shekarar 2011, su laifukan idan aka aikatasu doka zata iya yanke ko  wane irin hukunci ne.

Amma sun ki yarda da cewar sun aikata laifukan. Mai shari’a Akintoye ya dage sauraren karar zuwa 25 ga watan Mayu 2018, wanda za a ci gaba da sauraren karar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: