Farashin Mai Ya Yi Tashin Gwauron Zabo — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Farashin Mai Ya Yi Tashin Gwauron Zabo

Published

on


Samfarin danyen mai da ake kira Brent sweet, ya yi tashin gwauron zabo a ranar litinin data gabata duk da matsalar tattalin arziki da kasar Benezuela take fuskanta, inda hakan yake kara zama barazana wajen samar da danyen man a kasar.

Har ila yau, farashin danyen mai a kasar Amurka shima ya tashi, inda ya kai sama da kashi 70 na dalar Amurka a karon farko tun a cikin watan Nuwambar shekarar 2014.

Hakan ya janyo damuwa a tsakanin wadanda suka damu akan matakin da Amurka ta dauka na kodai ta janye shiga cikin yarjejeniya da kasar Iran.

Mai makon hakan, Amurka tana son ta sanya takunkumi akan Tehran, ta hanyar ajiye maganar sayar da mai a kasuwar duniya a gefe.

Sai dai, danyen mai na kasar China Shanghai wanda aka kaddamar dashi a cikin watan Maris, ya janyo karyewar dala idan aka canzata har ta kai 71.32 na gangar danyen mai, wanda ya karu zuwa dala 72.54 a ranar litinin data gabata.

Masu hasashe sunyi gargadi akan zurfafar karayar tattalin arziki data aukuwa jigajigan masu fitar da danyen mai dake kasar Benezuela, inda hakan zai iya zama barazana wajen sarrafa danyen man da kuma fitar dashi zuwa wasu kasashen duniya.

Danyen mai na kasar Benezuela ya ragu tun a farkon shekarar 2000 zuwa ganga miliyan 1.5 a kullum, ganin cewar, kudancin kasar Amurka ta gaza zuba jari mai yawa don kare masana’antar ta mai.

A cewar wani jami’i mai suna Greg McKenna, abin yafi karfin matslar da kasar ta  Benezuela ke fuskanta.

Yace, babban labari a wannan satin shine, akan magar yarjejeniyar makamin linzami na   kasar ta Iran.

Ya kara da cewa, mafi yawancin shiga kasuwar, ana sa ran shugaba Donald zai janye daga yarjejeniyar.

Kasar Iran ta sake zamowa kasar dake a kan gaba wajen fitar da danyen mai a shekarar 2016 bayan takunkumin da aka kakaba mata an cire shi akan shirin ta na sarrafa makamin linzami.

Da yake bayyana kwankwanton sa akan amincewa da kasar ta Iran, Trump ya yi barazanar janyewa daga yarjejeniyar ce a shekarar 2015 saboda karin wa’adin takunkumin wanda ya kare a ranar 12 ga watan Mayu.

Wannan matayin, zai iya janyowa kasar  Iran koma baya wajen fitar da mai zuwa wasu kasashen duniya.

 

Advertisement
Click to comment

labarai