Abin Da Ya Sa Na Amsa Kiran Tsayawa Takarar Sanata - Isa Yuguda — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Abin Da Ya Sa Na Amsa Kiran Tsayawa Takarar Sanata – Isa Yuguda

Published

on


Malam Isa Yuguda wanda tsohon gwamnan jihar Bauchi ne, kuma shi ne suka fito suka kara a yakin neman zaben 2015 a kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu da marigayi Malam Ali Wakili wanda guguwar APC ta yasar da shi, ya jaddada bukatarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu domin maye gurbin Wakili.

Isa Yuguda wadda ya bayyana wa manema labaru jiya a Bauchi kan cewar ya fito ne ba a kashin kansa ba sai domin ya amsa kiran dumbin jama’an jihar Bauchi da suke ta rokonsa na ya fito domin ya ci gaba da daurawa daga aiyukansa na alkairi da ya jimfida musu musamman a lokacin da yake gwamna da sauran aiyukan da ya yi a baya na banki da sauransu.

Malam Isa Yuguda, ya kuma shaida wa manema labarum cewar shi bai sanya neman kujerar a ka ba, da marigayi Ali Wakili wanda kanine a garesa na raye da sam ba zai fito neman wannan kujerar ba, la’akari da alakar da ke tsakaninsu.

Yuguda ya bayyana cewar ko a zaben 2015 da ya gudana, wasu ‘yan siyasa ne suka kai mari wajen ganin ya tsaya wanda daga bisani kuma ma suka bar jikinsa domin ba don Allah suke tarayya da shi ba.

Ya kuma fito ne a karkashin jam’iyyar Green Party of Nigeria wato GPN domin neman sa’a a zaben maye gurbi da kuma zaben 2019 da ke hararmu.

Ta bakinsa; “Ana ta kiranyen-kiranyen na fito na tsaya neman kujerar Sanata a 2019, amma ni har ga Allah, har a cikin zuciya ta, na yanke, na kuma hakikance kan cewar muddin Ali Wakili yana da rai kuma ya zo ya sameni a matsayina na Wansa, ya ce min zai tsaya to ba zan yi takara da shi ba. Ko a 2015 din ma kaddarace, domin na yi na yi da mutane domin na ce musu ba zan yi takara da kanina ba; ‘yan siyasa suka matsamin, wanda mafiya yawansu zukatansu bai da kyau. Yau kana ganinsu mafiya yawansu bana tare da su, sune suka cika fom suka yi ta kaiwa da komowa, ni ban taba fitowa kamfen na ce ina neman Sanata a zaben 2015 ba, amma kaddarar Ubangiji yau Allah ya amshi ran Ali Wakili, (Allah gafarta masa),”

Isa Yuguda ya ci gaba da cewa, “Wannan fitowar da na yi a wannan lokacin domin neman Sanata babu wani da nake ganinsa a matsayin Kanina wanda ya fito neman kujerar nan, na biyu kuma ganin cewar al’umma sune suka yi ta fitowa suna cewa Malam don Allah ka fito domin ka yi Sanata don ka taimakemu, wannan rokon da jama’a ta suke ta yi min, kuma ina da lafiya ta, inda da karfi da zarafi sai na ga zan iya taimakawa. Da badin jama’a na bane suka hakikance na fito, wallahi da ba zan fito ba. Jama’an Bauchi sun kirani kuma na amsa musu domin gudanar musu da nagartaccen aiki,” In ji Isa Yuguda.

Da yake bayyana girman da sanayyar sabuwar jam’iyyarsu ta GPN wanda ya fito neman Sanatan a cikinta, Yuguda ya bayyana cewar samun nasarar jam’iyyar yin Allah ne, domin Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so “2007 ANPP duk da ta sanu a wasu jahohin amma ai a jihar Bauchi ba santa ba; cikin yardar Allah daga fitowata a wannan jam’iyyar, wata uku kacal na yi ina kamfen kuma na ci kujerar gwamna, domin mutanen Bauchi sun sanya ni a gaba suna sona sai da na yi nasara, yanzu haka jama’a sun sake samun fahimta sosai kan yadda ake siyasa da gudunar da mulki, jama’anmu Malam Isa suke so ba jam’iyya ba, domin haka ne na ke shaida maka cewar ina ganin nasara cikin yardar Allah,”

Malam Isa Yuguda wanda ya kuma shaida cewar da zarar ya samu zarafi a zaben da ke tafe, zai yi kokarin share wa jama’an Bauchi musamman jama’an Bauchi ta Kudu hawaye, domin kuwa zai yi amfani da kwarewarsa wajen samar musu da hanyoyin ci gaba domin gina kasa a kowani lokaci, ya yi fatan Allah ya jikan kasaninsa Ali Wakili.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!