Abubuwan Da Ya Kamata ‘Yan Nijeriya Su Yi A Kan Kishin Kasa – Sheikh Badaru — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Abubuwan Da Ya Kamata ‘Yan Nijeriya Su Yi A Kan Kishin Kasa – Sheikh Badaru

Published

on


  • Yayin Da Wasu Ke Kishin Kasa, Mu Kanmu Muka Sani

SHEIKH BADRU MU’AZ KANO wanda a ke yi wa lakabi da ‘Matasa ga na ku’ cikakken mai kishin matasa ne da ma al’ummar Nijeriya gaba daya, bayan karatu ya kai shi kasar Masar a nan ya rike mukami a matsayin  shugaban ‘yan Nijeriya mazauna Masar. Harkokinsa na kasuwanci gaba daya a kasar Masar ya ke gudanarwa. Duba da irin gudumawar da ya ke bawa matasa ya sa su ka roke shi da ya zo jiharsa ta Kano ya wakilce su. A yanzu haka Sheikh Badaru Mu’az dan takarar Gwamna ne a Jihar Kano karkashin jam’iyyar ‘Green Party of Nigeria’. Ga yadda tattaunawarsa ta kasance tare da wakiliyarmu JAMILA UMAR TANKO:

Za mu so mu ji cikakken sunanka…

Sunana Sheikh Badaru Mu’az.

 

 

Ka bayyana wa masu karatu takaitaccen tarihinka…

An haife ni a unguwar Gwagwarwa a  2 ga watan takwas shekarar 1982.  Na yi karatun firamare a Gawuna Primary school daga nan sai na tafi karamar makarantar  sakandire ta Comercial, sai na wuce babban aji na sakandire a Maikwatashi. Na yi karatun Difuloma a kan ‘software Engineering’.  Na sami tafiyar kasar Egypt  da niyyar yin aiki a kasar  a ‘protocol office’, shi ma da na zo ambasadan  na wancan lokacin ya ce ba zai yi aiki da ni ba saboda ina da rikon addini. Allah cikin ikonSa sai na samu damar yin karatu na digiri a Arab ‘Acadamy for Science, Tech and Marine Engineering Trade Logistic and International Transportation’. A yanzu haka ina kasuwanci a nan kasar Masar.

 

A matsayinka na matashi da ya yi gwagwarmaya  a cikin kasar nan da ma kasashen waje. Me za  ka iya cewa  game da halin da ‘yan Nijeriya su ke ciki?

Halin da ‘yan Nijeriya su ke ciki sai dai mu ce Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un zan yi magana a kan abu uku wadannan abubuwa su ne: Kaf Afrika babu al’ummar da su ke da ilimi amma iliminta ba ya mu su amfani kamar al’ummar Najeria, haka kaf Afrika babu al’ummar da  ta ke da arziki amma arzikinta ba ya yi mata amfani kamar al’ummar Nijeriya sannan kuma babu kasar da ta ke da  ma’adanai a kasa  ba ma Afrika ba kakaf duniya mu na cikin masu arzikin  wadanda su ke da ma’adanai amma ba sa yi mu su amfani  sai al’ummar Nijeriya.

 

Me ya sa ka ce haka?

Mun zauna a kasasashen waje mun ga yadda su ke yi, abin da a ke fara sakawa a rai da farko shi ne ka fara sa ka kishin kasarka a zuciya kafin ka yi kishin kanka, amma mu anan kasar an nuna mana ka yi kishin kanka  kafin na kasarka. Amma abin da ba ka sani ba shi ne idan kasarka ta shiga wani hali kai ma ka shiga wani hali ba dan komai ba idan ba ta da martaba duk in da ka je ba za a kalle ka da muhimmanci ba. Duk wanda ya ke fita kasashen waje ya sani  ka na zuwa abin da  za a fara tambayarka shi ne ‘passport’ dinka, idan ka ce babu ka shiga zargi ashe kenan wannan kasar ta na da amfani a wajenka da kuma darajar da za ta kare kimarka a duniya. Abin da ya kamata mu fara saka wa a gaba shi ne ita kasar Nijeria sannan a yi maganar kanmu mu ‘ya’yan Nijeriya.

 

Wacce hanya ka ke ganin za a bi don sakawa ‘yan Nijeriya wannan kishi a cikin zukatansu?

Babban kalubale shi ne ga shugabannin kasar nan, da yadda su ke mulkarmu. Na taba zama mu ka yi hira da wani dan takarar shugaban kasa a kasar Masar wanda a ke kiransa Hamdu Sabbahi shi ne ya zo na uku, a lokacin da ya fadi zabe ‘yan jarida  su ke tambayarsa cewa yanzu ka  fadi zabe, me ka ke bukata Allah ya yi ma ka nan gaba? Sai ya ce in a san ransa ne Allah Ya yi masa shugaban kasar Nijeriya. ‘Yan jaridu su ka yu carko-carko dan da yawa ba su san ma Nijeriya ba. Su ka tambaye shi ina ne Nijeriya? Sai ya ce duk duniya babu kasar da ta ke da arziki amma ba ta san yadda za ta kashe ba, babu in da su ke da masu ilimi da mahaddata kur’ani irin kasar hatta matan aure a cikin gidan aure mahadda ne , haka babu kasar da a ka tara masu hakuri masu biyayya  ga shugabanninsu irin Nijeriya, amma in da su ka shiga cikin wahala shi ne rashin shuwagabanni na gari. Har ya ke cewa da za a bashi shugabancin kasar Nijeriya na shekara goma to da babu kasar da za ta tsone masa ido a duniya. Hakan da ya fada sai ya zaburar da ni na ji ina so in tsaya takarar shugaban kasar Nijeriya amma duba ga dokar kasa, shekaruna ba su kai ba ba. Amma idan ki ka duba kaf fadin Nijeriya babu wata jahar da ba ta da mutanenta anan kasar wadanda mu ke tare da su.

 

Kamar yadda tarihinka ya nuna ka shugabanci al’ummar Nijeriya mazauna kasar Masar. A tsarin mulkinka shin ka yi amfani da shawarwarin da dan takarar nan ya ba ka?

Haka ne na shuganci ‘yan Nijeriya mazauna kasar Masar wanda har gobe su na kwadayin in zo in kara tsayawa ni ne na ki, har yanzu ana tuntuba ta a kan yaya za’ayi in yarda in tsaya  na ki, ba dan komai ba sai dan irin abubuwan da na gani kuma  kasata Nijeriya ta na bukatar irin mu matasa, mu ya kamata mu fito a gyara ba dan kan mu ba, akwai ma su zuwa nan gaba ‘ya’yanmu da jikokinmu su zo su mora.

 

Wanne kira za ka yi ga ‘yan Nijeriya musamman matasa?

Nijeriya sai addu’a  bayan nan ‘yan kasar su taru su cashe su kasa su tsare su duba amanarsu da aka bawa shugaba idan bai yi musu aiki ba su fito su yi magana amma a bawa shugabanni kudi su cinye babu mai yin magana in dai wannan ne babu yadda za a yi a samu gyara.  Ina kira ga ‘yan uwana ‘yan Nigeriya ma su mutunci da daraja da su dage su kafa su tsare, abubuwan nan a lissafe su ke a rubuce a takarda sai ka auna ka ga wane aiki su ka yi ma ka ? Idan ba su yi ma ka komai ba  ka yi kokari ka kai kara zuwa  EFCC ta kwato ma ka hakkinka daga nan sai ka ga hakkokin mutane su na fitowa. Ina kira ga ‘yan Nijeriya  su daina gani su na kawar da kai, ya kamata su yi magana a kan hakkunansu ita ce hanyar kwatar ‘yanci.

 

Da alama ka na da kishin al’ummarka. Wanne irin duba ka yi ga mata da su ke zaune a cikin gidajensu na aure ba sa yin komai?

A cikin tsare-tsarenmu da mu ke da shi mu na da kudirin yadda  za a tallafawa mata da kananan yara. Babban abin da ya sa ke cusa mu a cikin siyasa sabo da mata da matasa ne, musamman ma mata. Mata su ne iyayen al’umma, duk wani namiji mace ce ta haife shi  kuma ya na da  mace yaya ko kanwa kuma mace zai aura kuma ya haifi mace. A rayuwa ta addinin musulunci ana bawa mace fifiko da daraja fiye da yadda ba ka zato sabanin a kasar mu Nijeriya.  Misali a wannan kasa ta Masar duk namijin da ya auri mace idan ya sake ta doka ce duk in da ya ke aiki za a raba albashinsa gida biyu ana ba ta rabi, shima ya na  daukar rabi. Hakan ya sa da mutum ya saki mace gara duk abin da ake ciki su yi hakura su jure su  zauna lafiya.

 

Ka na ganin idan har ka zama Gwamnan Kano za ka kawo irin wannan tsari a jaharka? 

Kwarai kuwa, a cikin kudire-kudirenmu mu na da tsarin  za mu taimaki mata musamman a bangaren zaman aure kamar yadda mai martaba sarki Sunusi Lamido ya ke magana tabbas za a dawo a dabbaka wadannan dokokin  na yadda mace za ta yi zaman aure. Duk wanda ya ce zai kara aure sai a duba a ga yaya ya ke, zai iya rike matan? Ga matarsa da yaransa na gida idan bai kula ba dole gwamnati za ta tirsasa shi ta karbi abin da ya ke hannunsa ta bawa yaran nan don su sami ilimi da rayuwa mai in ganci, haka ma mata za a kwatar musu hakkinsu ta kowanne bangare. Za mu  dauki ma’aikata mata masu kula da wannan don su dinga fito mana da abin da ya ke faruwa a cikin gidajen aure, gwamnati za ta kira wannan miji da ya ke zaluntar matarsa a tsawatar ma sa domin ya gyara .

 

Mata da yawa matasa har da ma matan aure musamman a arewacin Nijeriya sun fada harkar shaye-shaye. A ganinka me ya jawo wannan?

Babban tashin hankali matan aure sun koma ‘yan shaye-shaye na benalin da sauransu, innalillahi wa’inna ilaihi rajun wannan babban abin tashin hankali ne matuka dole tarbiyya ta tabarbare domin mace ita ce malama ta farko wajen tarbiyyar yaro. Abin da ya ke jawo hakan har da rashin kula daga bangaren mazan, su suke cusawa mata haushi da takaici. Za mu yaki wannan mummunan akida dari bisa dari yadda za a yi zaman aure mai inganci a haifi yara ma su  tarbiyya yadda za su girma su taimaki al’umma gaba daya.

 

Me za ka ce game da ilimin ‘ya’ya mata?

Mu na da kudiri idan Allah Ya ba mu gwamnati, za mu bayar da ilmi kyauta domin idan mace ta sami  ilimi al’umma gaba daya ce ta samu.  A bangaren lafiya da yawa mata za mu cusa domin su kula da ‘yan uwansu mata. Babu abin da ya ke damuna irin in ga namiji ne ya ke duba matata, ina so in tabbatar mi ki da cewa duk wani bangare na ilimin mace zai yi amfani a jahar Kano mu na da tsarinmu a kasa. Lallai  jama’ar Kano za su yi alfahari da wannan ilimi na ‘ya mace za mu bunkasa shi fiye da yadda a ke tunani,  na maza ma ba a bar su baya ba.

 

Wacce hanya ka ke ganin za a bi domin tallafawa rayuwar matasan Nijeriya, duba da ganin irin halin rashin aikin yi da su ke ciki a halin yanzu?

Har kin sosa min inda ya ke yi min kaikayi wallahi ina tausayin matasan Nijeriya duk wata al’umma da ta ci gaba ta na yiwa matasanta tanadin dan su zama wani abu nan gaba, ko an ki ko an so matasan nan su za su rike kasar nan gaba amma a nan Nijeriya manya kokari su ke su danne matasan su durkusar da su, su tashi ba su da wani katabus. Zan ba ki wani misali an taba yin wata Gwamnati a jahar Kano, ba a taba yin Gwamnatin da ta bawa matasa jari da koya mu su sana’u ba kamar wannan ba, amma abin da ta kasa ganewa shi ne mun ba ta shawarar cewa dole fa sai an  duba yaya matasan nan su ke ciki bayan an basu jari sun tafi, dole sai an bi su ana ganinsu ana bincikarsu a gyara mus kuskurensu, a kalla a sami kimanin shekara ana gadinsu sai an tabbatar da cewa wanan tsarin ya zauna. Amma sai  gwammanti take ganin kawai ba sai ta saka musu ido ba.  Misali an koyawa matashi aikin kafinta an saya wa ma sa abin kimanin Naira dubu dari amma idan ka bashi sai ka ga ya je ya siyar Naira dubu ashirin. Wannan ba laifin matasa ba ne, laifin gwamnati ne da ba ta saka mu su ido ba. Ya na daya daga  cikin burinmu mu bunkasa matasa  su dogara da kansu. Idan Allah  Ya ba mu dama za mu samarwa matasa aiki kamar kimanin su miliyan biyu a fadin jahar Kano, Allah Ya ba mu wannan ilimin yadda za mu yi.

 

Mun gode kwarai.

Ni ma na gode.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!