Cikin Ruwan Sanyi PDP Ke Kamfen Dinta – Ahmed Tahir — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Cikin Ruwan Sanyi PDP Ke Kamfen Dinta – Ahmed Tahir

Published

on


An nemi Jam’iyyun kasan nan da su yi koyi da Jam’iyyar PDP musamman kan irin matakan da Jam’iyyan ta PDP ke bi wajen yakin neman zaben ta, daya daga cikin Shugabanni masu kula da harkokin Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, sannan kuma, daya daga cikin masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Kaduna ta Kudu. Gogaggen dan siayasa, wanda ya riki mukaman siyasa da dama a baya, kawo yanzun, tsohon dan Majalisa, mai wakiltar mazabar  Tudun Wada a wancan karon, Alhaji Ahmed Tahir, ne ya yi wannan kiran. A wata ganawa da ya yi da manema labarai a Ofishin sa da ke Kaduna. Ya bayyana yanda Jam’iyyar su ta PDP ke gudanar da yakin neman zaben ta a cikin ruwan sanyi, inda ma har ya bayyana cewa, a mafiya yawan lokuta, abokan hamayyar na ta ne suke yi mata kamfen. Sai ya yi kira da a gudanar da siyasa cikin tsafta da kwanciyar hankali ba kuma da gaba ba.

Da yake amsa tambayar yadda Jam’iyyar na su ta PDP ke gudanar da kamfen din ta cewa ya yi, Hakika suna daukan matakai, kama daga birane har ya zuwa kauyuka, in Allah Ya so Ya yarda, muna da tabbacin hanyoyin duk da muke bi za su kai mu ga nasara. In ma ka lura da kyau, za ka ga yakin neman kuri’ar da PDP ke yi ba mai za fi ne ba, domin cikin ruwan sanyi ne, ba ka taba jin ana zagi ko duka ko cin mutuncin wani da makamantan hakan. PDP, tana kamfen ne cikin natsuwa, sannan kamfen din namu ma, ma fi yawan su a wajen abokan adawa ne muke tsintar sa, watau abin da ake cewa a hausance, tsintuwar dami a kala, domin kuwa su na yi mana kamfen ne da kura-kure da kuma tabargazan da suke rafkawa,

Mu a kullum kamfen din mu na magana ne, ita ce kuwa, me za ka yi, me kuma ka yi, shekaranjiya kuma me ka yi, gobe kuma me za ka yi? Kuma da wace hujja ce kake tabbatar wa da al’umma cewa abin da kake fada ma su gaskiya ne, me kuma za su dogara da shi a gare ka cewa in sun zabe ka ba za ka saba ma su ba, ba kuma za ka ci amanan su ba? duk wannan shi ne kamfen din da PDP ke yi, sam ba ma kamfen din tashin hankali.

Da yawan mutane ba PDP ce ta ce su dawo ba, ba kamfen PDP ta yi masu ta ce su dawo ba, abubuwan da ke gudana na zahiri ne da suka ji suka kuma gani, su suka sanya jikin su ya yi sanyi, sai suka gwammace su dawo PDP din. Mu na zaune a gida, mu kan ji wata banbarma na su, sai mu dauka mu fayyace wa mutane ita, shikenan ka ga sun yi mana kamfen. Mafiya yawan mutane ma yanzun su na wadatuwa ne da abin da suke ji ma kunnuwan su a gidajen Rediyo, suke kuma gane ma idanuwan su a tashoshin talabijin, sai ka ga sun komo gare mu ba ma tare da mun ce ma su komai ba.

Da yake  kwatanta shekaru 16 da PDP ta yi tana mulki a wancan lokacin da kuma shekarun da wannan gwamnatin ta yi a wannan lokacin ta fannin ci gaba da samar da manyan ayyukan raya kasa cewa ya yi.

Tabbas a wancan lokacin, komai adawar mutum ya san an yi ayyukan raya kasa kuma manya-manya har zuwa kananan ma su dimbin yawa, wadanda a dan wannan zaman namu ba sa lissaftuwa, duk da cewa an yi kura-kurai, kurakurai kuwa dabi’ar dan adam ne. su ma masu mulkin a yanzun ai abin da ya hana su iya tabuka komai kenan, kura-kuran, wanda munin na su kuma shi ne ba sa daukan gyara, duk wannan zafi da radadin da ake jin sa, ai kurakuran na su ne suka janyo su. Saboda kurakuran na su, yanzun tun ma ba a je ko’ina ba, PDP tana zaune a gida jama’a suke kwankwasa mata kofa, su na fadin, ‘abin da ya faru jiya mun gane akwai kuskure a ciki ku dawo,’ duk abin da ke ta faruwa kenan.

Ka ga dai a wadancan shekaru 16 da kake magana an sami ci gaba matuka ainun, tattalin arziki kuma ya karu sosai, an sami sabbin manyan ayyukan raya kasa kala daban-daban kuma a dukkanin sassan kasarnan. Ko da kuwa za ka ce, ai a lokacin ne irin su Boko Haram suka bullo, amma dai abubuwan alherai masu yawa duk a zamanin ne suka bullo, sannan kuma ma matsalar Boko Haram ba matsala ce ta Nijeriya kadai ba, matsala ce ta kusan duk duniya. Don haka ka ga ashe ma wannan din ba kyankyasan PDP ne ba.

Yanzun kuma ga halin da ake ciki, wadanda suke ganin ba a iya ba, to sun karba, amma yanzun misali, buhun wake yana tsakanin dubu 17 ko 18 ne, buhun gero ya kai har dubu 12, buhun masara ya kai dubu 11, an taba samun makamancin hakan a zamanin mulkin Jam’iyyar PDP? Sam-sam, PDP ba za ta yarda da faruwar hakan ba, domin duk wannan wahalar kan wa take komawa? Ai kan talaka ne take komawa. To duk siyasa kuwa in aka ce talaka bai samu sauki ba, ai ka ga siyasar ba ta yi amfani ba kenan, wane kamfen kuma za ka yi masa? Yana neman abin da zai ci yana neman ya gagare shi, sai kai kuma ka je ka matsa masa da zancen siyasa to da wanne zai ji.?

A karshe ya yi kira ga ‘yan siyasa musamman yanzun da aka fara buga gangar siyasan, da su daure a yi siyasa mai tsafta, a saka hankali a cikin duk ayyukan siyasan da ake yi, ina kira ga sauran Jam’iyyu da su yi koyi da irin rawar siyasar da Jam’iyyan PDP ke takawa, ba zagi ba duka, ba bata suna ba cin mutuncin kowa.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!