Kada A Ci Moriyar Ganga A Mance Da Kwaure! (6) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MAKALAR YAU

Kada A Ci Moriyar Ganga A Mance Da Kwaure! (6)

Published

on


08023703718 (TES Kawai )   ibrahimshehu781@yahoo.com

Jama’a masu biye da mu a wannan shafi assalamu alaikum. A wannan karo muna fatan karkare nazarin da muke yi dangane da korafe-korafen da masu hangen-nesa ke yi kan yadda ake mantawa da nagartattun jagorori musamman a fagagen masu ayyuka da sana’o’i na fasaha da basira, musamman rubuce-rubucen littattafai da shiryawa da tsara wasannin kwaikwayo. A wannan nazari da muke yi mun dauko wadansu kadan ne daga irin wadannan zaratan shugabanni don su zama zakarun gwajin dafi, tare da niyyar haska irin yadda suka rika bayyana basirorin nasu.

A yau zamu dauki dai-dai daga cikin wasu abubuwan da suka dace a rika la’akari da su ne da wasu uku uku daga ccikin wadannan jagorori suka nusar a ayyukan nasu. Zamu dauki daya daga aikin Malam Yusufu Ladan, Dan-Iyan Zazzau, da Alhaji Kasimu Yero da kuma Samanja, wato Alhaji Usman Baba Pategi. Manufarfu a nan ita ce a bayyana wa jama’a kan cewa jama’a da zamantakewar su jama’ar wadannan mutane suka fi damuwa da su, ba wai su kansu ba.

Misali na farko, na taba tambayar Mai girma Alhaji Yusufu Ladan kan cewa wasnnanin kwaikwayon da yake rubutawa da kuma shiryawa har ana gabatar da su a gidan rediyo, ko ana biyansu wasu kudade na daban ne, ganin cewa a yanzu wannan fage ya zama na jari hujja? Amsarsa ita ce, ai wasannin da suke yi raba-darnin aikinsu na rediyo ne, saboda haka bas a hangen a nemo wasu makudan kudade a biyasu. Baya ga haka kuma don sun wayar da kan jama’a da kuma tayar da su daga tsimi a matsayinsu na wakilan jama’a ta hanyar basirar da Allah ya ba su, sai su ce zasu zura ido a biyasu? Ya bayar da misali da wani wasa na Kamar da Gaske  ya tsara shi ne kan yadda ake samun wasu malaman makaranta ke bata dalibansu ‘yammata ne da kuma illar da ta ke jawowa ga al’umma sannan da hukucin da ke hawa kan irin wadannan miyagun malamai. To irin wannan wasa ai manufarsa kyautata tarbiyya da kuma rayuwar jama’a, ba sharholiya ta rayuwa kawai ba.

Idan an luara da idon basira, irin dabarar da wannan fasihi ke yi amfani da basirar da Allah ya ba shi don amfanar da jama’a kenan.

Wani misali shi ne yadda Samanja Mazan-fama, wanda daga baya ake yi masa lakabi da Baba Samanja ke takarkarewa a koda yaushe wajen rubutawa da tsara wasannin kwaikwayo da suka hada da na rediyo da talabijin, duk da niyyar kyautata rayuwar al’umma. Ya shiga tarko na barazana ga rayuwarsa sau da dama, kan yadda wasu da suke ganin yekuwar da yake yin a kawo gyara a tsakanin al’umma kamar da su yake yi, kuma don me za a ce su daina. Haka kuma a daya gefen ya samu yabo daga wasu kan taimakawar da yake yi da basirarsa. Misali daya a nan shi ne wani jan hankalin Gwamnati da ya yi, sa’ilin da ake neman kara jami’o’i a kasar nan, sais hi kuma cikin wasan Duniya Budurwar Wawa ya ankarar da ita Gwamanti cewa zai fi dacewa a kyautata tare da inganta wadanda tuni ake da su, kafin a yi tunanin hina sababbin, domin kuwa idan ba a yi hattara baa bin zai zame haihuwar guzuma, ‘ya kwance, uwa kwance.

Misali na uku shi ne dangane da marigayi Kasimu Yero. Na bayyana a cikin wata makala da na gabatar cewa sa’ilin da ake ta yekuwar yadda za a kara dankon zumunci tsakanin al’ummomin kasar nan wadanda ke da mabambantan kabilu da addinai, sai aka shirya wani fim mai lakabin Amina. A wannan fim dai an nuna yadda a dalilin ceto wata ‘yar kabilar Ibo, mai suna Nketchi, ta kai ga har sai da wani babban Sarki Bahaushe a arewacin Nijeriya ya aureta, daga baya kuma har danta Yarima Musa ya za gaji mahaifinsa.

Da irin wannan dabara ce hazikai irin su Kasimu Yero da Usman Baba Pategi, da Yusufu Ladan, da Shu’aibu Makarfi, da su Muhammadu Ango Zariya da Adamu Gumel da makamantansu suka yi ta kyautata wannan fage na wasan kwaikwayo da fina-finai.

Bukatar da ake da ita ce a rika waiwayen irin ayyukansu da kuma tunanin yadda za a inganta tare da zamanantar da wasannin kwaikwayo da fina-finai, a gefe daya kuma ba tare da zarmewa, ana wuce makadi da rawa ba, ko kuma shigo da gurbatattun abubuwa wadamda ba namu ba ne. wato dai abubuwan da zasu zama Bambara-kwai. A dai lura, da na gaba, ake gwada zurfin ruwa!

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai