Turawa Ne Su Ka Kawo Ka’idojin Rubutun Hausa –Farfesa Abdalla — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Turawa Ne Su Ka Kawo Ka’idojin Rubutun Hausa –Farfesa Abdalla

Published

on


A makon jiya mun tsaya ne inda Babban Mataimakin Shugaban Jami’ar NOUN, FARFESA ABDALLA UBA ADAMU, ya ke shaidawa Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, hujjojinsa na raba mallaka a rubutun Hausa. Ga yadda tattaunawar ta musamman ta cigaba:

Saboda haka da a ka zo wannan maganar na ce, to yanzu misali sai ka zo ka ce da Turanci ‘my chair’. Kalmomi guda biyu ne. Ko kuma ‘my house’ ko ‘my school’. Duk kalmomi biyu ne a ka kuma raba su, ba a hade su. Don me idan ka zo Hausa za ka hade? Me ya sa ‘gidana’, ‘motata’, ‘kujerata’? Ai abubuwa guda biyu ne; da kai da kuma kujerarka. Ba daya ku ke ba. Kazalika haka ma sunaye kamar misali ‘Dankwairo’, sai mu ka duba mu ka ga Turawa sai su ce ‘Johnson’. Ka gane? Ai dan John kenan a ke fada. Saboda haka ‘Danmaraya’, ‘Dankwairo’ ma yakamata a hade su da irin su ‘Dan’Anace’…

 

To, ba ka jin kamar za su ka na turantar da Hausa ne?

Ita kanta Hausar wa ya fito ma na da dokokin? Ba Turawa ba ne? Su ne su ka zauna su ka fito da dokokin. Babu wani Bahaushe a lokacin da Turawan mulkin mallaka su ka zauna a wajen farko-farkon karni na 19 su ka fitar da yadda yakamata a yi (rubuta) Hausa. Su ne su ka fito da su; su ka sami Westerman, su ka sami sauran manya-manyan farfesoshi na Turawa su ka tsara yadda yakamata jami’an mulkin mallaka za su karanta Hausa. To, saboda haka a gurinsu mu ka gani. To, amma a manta da cewa an hade ko an rabe, sai ka fadi dalilin da ya sa ba za a rabe ba. Ni na fada na ce, ni dai Ina rabawa saboda isar da sako. To, idan kai kuma ka ce dole a hada, sai ka zo ka yi min bayani ka ce ga shi dalilinka ko kuma ka yi naka, ni ma na yi nawa. Ai ba wanda ya ce nawa ne shi ya fi ko kuma naka shi ya fi, kowa da nasa, to shikenan, don ba zama a ka yi a ka ce yanzu yau an kirkiro da hanyar da za a yi Hausa ba; kowa dole ya yi irin wannan ba. Kamar Turanci ne; ba ka isa ka je ka zauna ka ce ga yadda yakamata a yi Turanci ba. Akwai dai ‘grammer’, akwai dai waye-waye, amma akwai kalmomi da su kansu kamus din Jami’ar Odford duk shekara sai sun fito da sababbin kalmomi da a ke saka su a cikin kamus din, kalmomin nan kuma mutane ne su ka kirkire su. Yanzu kamar su ‘Social Media’, su ‘Facebook’, su ‘goggle’, yanzu sai ka ji an ce zan yi ‘goggling’ din sa. To, yanzu ‘goggle’ ta shiga ita ma, ka ga suna ne na wani abu, to amma ta riga ta zama aikatau, amma ai asali ‘noun’ (sunan yanka) ne.

 

To, mu sake koma wa kan rayuwarka. Kamar yadda ka ce kai ne farfesa na farko a fannin ilimin kimiyya dan Kano, to an ce ma a lokacin kai ne mafi karancin shekaru da ya zama farfasa. Shin gaskiya ne?

Gaskiya ne, don a lokacin da na zama farfesa shekarata 41. Duk yawan wadanda su ke farfesa a lokacin sun girme ni nesa ba kusa ba. Iyaye ne ma. Ni ne mafi karancin shekaru a cikin Hausawa dai ’yan Kano mai wannan matakin a lokacin.

 

To, kuma ya a ka yi ka sake zama farfesa a wani fannin?

To, na ce ba zan iya zama Ina ta nazari a kan ilimi ba, saboda na ga mun yi rubutun, abin ya ki ci ya ki cinyewa, sai na ce gwanda na kyale wadansu su yi, ni kuma bara na shiga wani abin. Shi ne har na gaya ma mu ka zo mu ka yi ‘fonts’ (haruffa na Hausa masu lankwasa), mu ka fara rubutu, a ka fara kalubale. Sai a ka zo za a yi ‘conference’ a kasar Jamus a wata jami’a a kan muhimmanci adabi a Afrika. To, akwai wani Bature a na kiran sa Farfesa Graham a London, wanda shi malamin Hausa ne; ya kuma iya Hausar rangadadau. A kanta ya yi digirin-digirgir dinsa kuma ita ya ke koyarwa a London. Mun zama abokai da shi tuntuni. To, shi ya na da sha’awa na abinda ya ke faruwa na muhawara a kan litattafan soyayya har ma rubutu ya yi, kuma ya dogara ne kan abinda mu ka ba shi ya yi rubutun. Abin ya na birge shi. Shi, kamar yadda kowane Bature manazarci ya ke yi, bai dauki wani dangaranci ba, bai ce da kyau ko babu kyau ba. Mu ma a kan wannan salon mu ka biyo. Abinda ya dauka shi ne, wannan a na yin muhawara kuma ta na da muhimmanci a yi ta yin muhawarar. Da haka za a samu fahimta a kan me ke faruwa.

To, sai a ka gayyace shi wannan taron ya je a Nuwamba 2004, don ya gabatar da makala. Asali shi ma wacce ta gayyace shi dalibarsa ce. Ita ma ta yi rubutu a kan adabin Afrika kuma a ciki ta tabo litattafan soyayya na Hausa. Sai ta ce da shi ya zo ya gabatar da makala a wajen. Da ya ke Bature ne; bai da nufaka a zuciyarshi, sai ya ce, ‘a’a, ni rabona da na yi nazari a kan wannan na jima, amma akwai Abdalla Uba Adamu ya na yi kuma ya na dadin yadda ya ke yi, ku yi ma sa magana ku ji ko zai yarda’. Sai su ka rubuto min, sai na ce ‘ah! zan yarda, zan zo’. To, a lokacin duk wannan mahawara da a ke yi na tattara na rubuta wata makala da a ke kiran ta Bulullukai Daga Tafkin Da A Da Shiru Ya Ke (a fassarar Turanci). Abinda na ke nufi da wannan shi ne, mu na ta rubutu da Hausa, amma ’yan Kudu ba su sani ba, Turawa ma ba su sani ba, alakulluhalin a na daukar mu jahilai, saboda ba mu da rubutun boko wadanda su kai na Turanci, sai ga shi ashe idan ka duba dan a karkashin tafkin da ya ke ba ya motsi; tafki haka shiru iska ba ta karkada shi, ashe kasansa ya na zababbaka ya na tafasa, to yanzu sai ya doko sama ya dinga bulullukai ya na kuma bulullukowa. To, wannan shi ne na ke nufin cewa Hausawa fa sun iso, amma fa tuntuni sun jima tun 1933 su ke yin rubutu, amma da Hausa. Amma duk ba a san da wannan ba. Saboda haka a daina yi ma na kallon jahilai.

Na bada tarihin yadda a ka samu rubuce-rubucen Hausan da yadda har a ka zo kan wannan labaran soyayyar da a ke cewa. Sai na aika mu su Jamus. Da na aika mu su, sai shi (Farfesa Graham) na aika ma sa kwafi. Ya na gani sai ya bugo min ya ce, ‘a’a, wannan ya yi mu su yawa; mu akwai wata mujalla a na kiran ta ‘Research in African Literature’, wata muhimmiya shahararriya’ ya ce a nan yakamata a buga ta (makalar). ‘Wannan don Allah kada ka ba su duk gabadaya, ka daddatse’.

 

Za mu  kwana nan. Sai kuma makon gobe da yardar Allah za mu ji yadda a ka karke kan batun gabatar da mukalar tasa a Jami’ar da ke kasar Jamus da kuma yadda har lamarin ya kai ga Farfesa Abdalla ya samu sake zama farfesa a karo na biyu bisa wannan tafarki.

Advertisement
Click to comment

labarai