An Gudanar Da Zaban Shugabannin Jam’iyyar APC A Katsina Cikin Nasara  — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

An Gudanar Da Zaban Shugabannin Jam’iyyar APC A Katsina Cikin Nasara 

Published

on


Jam’iyyar APC a jihar Katsina ta gudanar da zaban shuwagabannin jam’iyyar a matakin kananan hukumomi cikin nasara kamar yadda manema labarai suka zagaya wasu wuraran da aka gudanar da wannan zaban a shekaranjiya asabar.

Wannan dai yana daga cikin tsarin da uwar jam’iyya ta yi na gudanar da zaban a duk fadin tarayyar Najeriya domin samar da sabbin shuwagabannin da za su tafiyar da jam’iyyar a matakin mazaba da karamar hukuma da jaha da kuma kasa baki daya.

A jihar Katsina kimanin masu kada kuri’a 11,639 suka fito a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina domin kada kuri’arsu a zaban da ya gudana na shugabanin jam’iyya a matakin kananan hukumomi.

Zaban wanda aka gudanar da shi cikin nasara ba tare da wani tashin hankali ba ya samu fitowar masu jefa kuri’a ba kamar wanda ya guduna a satin da ya wuce ba, inda aka samu wasu kurefe-kurafe wanda kuma masu shirya zaban suka ce ba su samu korafi a rubuce ba har yanzu.

Wuraran da manema labarai suka zagaya domin ganewa idanunsu yadda wannan zabe ya gudana sun hada da mazabar kangiwa da ke cikin garin Katsina da kuma karamar hukumar Rimi da Batawarawa da Charanci da Kaita da kuka Jibia.

A cikin garin Katsina mutane 32 da suka samu nasarar lashe zaban da ya gudana inda kuma nan ne cibiyar siyasar jihar Katsina kamar yadda baturan zabe Alhaji Bala Saulawa ya bayyana jin kadan bayan kammala zaban ya ce an yi shi cikin nasara ba tare da wata matsala ba.

Sai dai kuma a zaban da ya gabata wasu masu rajin takara a karkashin jam’iyyar APC sun yi zargin cewa an hana mutanen su sayan fom din takara zargin da kwamitin shirya zaban ya ce ba gaskiya bane ba wanda aka hana sayan fom ko yin takara.

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai