Ba Ka Bukatar Lasisi Don Kafa Ma’aikatar Samar Da Wutar Lantarki Mai Zaman Kanta –Fashola — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Ba Ka Bukatar Lasisi Don Kafa Ma’aikatar Samar Da Wutar Lantarki Mai Zaman Kanta –Fashola

Published

on


Ministan wutar lantarki da ayyuka gidaje Babatunde Raji Fashola, ya sanar da cewar, duk wanda yake buktar kafa masna’antar wuta don yinkasuwanci zai iya yi ba tare da ya karbi lasisi ba.

Raji ya sanar da hakan ne a hirar sa da manema labari lokacin da ya kai ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar Jigawa.

Ya ce, gwamnatin tarayya maici a yanzu, tana son ta karfafawa ‘yan kasuwa zaman kansu gwaiwa don su zuba jarin su a fannin samar da wutar lantarki a kasar nan ga alummar gari. Fashola yaci gaba da cewa, duk wanda yake bukata koda kamfanoni ne masu zaman kansu, za a basu damar samar da wutar lantarki mega watt biyu don sayarwa da alummar gari ba tare da sun karbi lasisi ba.

A cewar sa, “muna baiwa jama’a da kuma kananan ‘yan kasuwa kwarin gwaiwa don su dinga sayar da wutar lantarkin ba tare da sun kashe kudi masu yawa ba.”

Da yake yin tsokaci akan fara aikin na’urori samar da wuta masu yin aiki da hasken rana na kamfanoni masu zaman kansu musamman wadanda ke jihar jigawa da suke son zuba jari ya ce, masu son zuba jarin sun tsaya ne kai da fata akan son sayar ga gwamnati amma ranar da aka ware bata samu ba.

Raji ya kara da cewa,” amma har yanzu muna kan tattaunawa dasu kuma da zarar mun cimma matsaya da masu son zuba jarin, za’ a fara gudanar daaikin. Raji a karshe ya yabawa gwaMnatin jihar akan bayar da aka 2,000 don kafa aikin samar da wuta na gwamnatin tarayya mai haken  a jihar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai