Connect with us

WASANNI

Ba Zan Je Kungiyar Da Zan Iya  Haduwa Da Arsenal Ba, Cewa Wenger

Published

on

 

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, ya bayyana cewa bazai taba rike wata kungiya ba a gasar firimiya saboda baya son watarana ya hadu da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.

Wenger ya bayyana hakane jim kadan bayan antashi daga wasan daya jagoranci Arsenal na karshe a gasar firimiya a ranar Lahadin data gabata bayan ya shafe shekaru 22 yana jagorantar kungiyar.

Tun bayan bayyana aniyarsa ta barin kungiyar dai kungiyoyi da dama daga ciki da wajen Ingila suka fara bayyana aniyarsu na ganin yakoma kungiyoyinsu domin cigaba da koyar dasu sai dai abune mai wahala ya ci gaba da zama a gasar firimiya.

Wenger ya ci gaba da cewa bazai iya haduwa da Arsenal ba a kwanan nan saboda abune wanda bazai masa dadi ba kuma baya fatan faruwar hakan anan gaba saboda zuciyarsa bazata jure ba yaga yana buga wasa da Arsenal kuma ba a matsayin mai koyar dasu ba.

Ya ci gaba da cewa Arsenal kungiya ce wadda tayi masa komai a rayuwarsa kuma bazai taba mantawa da irin halaccin da kungiyar da magoya bayanta da yan wasa da shugabannin kungiyar suka nuna masa ba a tsawon zamansa a kungiyar.

A karshe yace yana fatan kungiyar zata nemo wanda zai maye gurbinsa cikin sauki kuma a shirye yake daya bawa sabon mai koyar da kungiyar shawara idan har ya bukaci haka saboda Arsenal tazama daya daga cikin rayuwarsa

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: