Connect with us

RAHOTANNI

Boko Haram: Abin Da Ya Sa Ba Zan Sake Komawa Konduga Ba –’Yar Gudun Hijira Hamsatu tare da diyarta

Published

on

Boko Haram: Abin Da Ya Sa Ba Zan Sake Komawa Konduga Ba –’Yar Gudun Hijira

Hamsatu tare da diyarta

 

 

Wannan wani rahoto ne wanda kafar sadarwa ta PREMIUM TIMES ta wallafa shi a karshen makon nan. Ganin muhimmancin rahoton wanda aka wallafa shi da harshen turanci ne ya sa Wakilinmu ABUBAKAR ABBA ya fassara domin amfanin masu karatunmu.

Malama Hamsatu Mustapha, yar shekara 36 bazawara ta bayyana cewar bata da wni zabi da ya wuce ta manta da maganar da garin su bayan da harin ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai a kauyen su na Konduga dake cikin jihar Borno, inda hakan ya tilastawa iyalan ta yin gudun hijira yaukimanin shekaru uku.

Tana daya daga cikin ‘yan gudun hijra da suka tsallke hare-haren ‘yan kungiyar ita da iyalanta gaba daya. Wannan ya sanyaya mata rai da kuma farin ciki matuka, duk da cewar ta rasa dukkan kayan ta a can Kunduga bayan ita da mijin ta marigayi, sub shafe shekaru biyu suna a zamanma’aurata da aure.

A cewar ta, “lokacin da muna zaune a Konduga, mun dauka shine wurin da yafi dacewa da zaman mu tare da iyalan mu, amma bayan da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kawo mana hari, sai muka fahimci cewar ba wurin zama bane ganin babu kwanciyar hankali a kauyen.

“Ta ci gaba da cewa, abin da kawai yafi mani mahimmanci a yanzu shine, rayuwa ta data iyali na. Hamsatu ta ce,“babu komai a Konduga, mahaifata domin na rasa komai nawa har abin kauna ta miji na da harin ya rutsa dashi, domin ina ganin wannan shahadar kawai ta isa a Konduga.”

Ta amince da cewar, ada Konduga yana daya daga kauyukan da ‘yan kungiyar basu mamaye ba a jihar Borno, amma daga baya ‘yan kungiyar sun farma kauyen wadanda kuma suka gagari sojoji shiga.

A kauyen na Konduga ne  rundunar soji ta bayyana cewar, shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, an kashe shi a cikin watan Satumbar 2014, wanda ikirarin nasu  daga baya ya kasance ba haka bane, bayan da suka gano wanda suke cewar sun kashe ba Shekau bane mai kama dashi ne.

Ta kara da cewar, inda Konduga ya fada a hannun ‘yan kungiyar Boko Haram a lokacin da ake cikin tsananin gumurzun dasu, cikin sauki ‘yan kungiyar zasu mamaye Maiduguri ko kuma jami’ar Maiduguri wadda tana daya daga cikin manya wurare da gwamnatin jihar ta zuba jari dake bayan garin Maiduguri a kan titin Bama.

Hamsatu ta ce, amma bayan da Konduga ta fada a hannun ‘yan kungiyar, basu iya dannawa cikin Maiguriba saboda jami’an soji da aka girke a kan hanyar shiga Maiduri ba.

Ta bayyana cewar, a harin da suka kai na karshe, mafi yawancin mazauna kunyen sun yi fice daga kauyen, inda sakamakon harin, mijinta ya samumummunan raunuka, amma duk da hakan ya samu ya arce zuwa Maiduguri.

A cewar ta, ‘yan “Boko Haram sun kore mu daga kauyen, inda muka dawo nan Modusulumri dake wajen Maiduguri da zama. Hamsatu ta ce, ‘yan kungiyar sun kashe mutane da dama da kuma kona mana gidaje, mun rasa komai da zaiyi wuya mu sake mallaka, mun kuma shafe kwanuka uku a daji muna ragaita, kafin mu dawo nan da zama.

Ta bayyana cewar,”Bulama na kauyen Modusulumr ya san mjina, sai ya bamu wajen zama, inda muke zaune nida iyali na mu goma harda mijina.”

Rayu Ta A Matsayin Uwa Bazarawa:

Kamar sauran ‘yan gudun hijirar ita ce zata ci gaba da kula da dawainiyar iyalnta ganin cewar mijinta bai tallake harin ba saboda munanan raunukan da ya samu a lokacin da ya samu ya gudu lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai harin a Konduga.

A cewar ta, “mijina ya samu mummunan rauni saboda harbin sa da ‘yan kungiyar suka yi, inda ta ci gaba da jinyar sa kimanin shekaru uku daga karshe kuma ya rasu ya barni a zaman uwa kuma bazawara da ‘ya’yan mu takwas, ba zan iya bayyana irin wahalar dana ke ciki ba a yanzu. bayyana cewar, iyalanta sunga rayuwa, inda kaya sawa masu kyau da abinci yake gagarar mu, muna kawai dogaro ne akan makwabta da suke taimaka mana a koda wanne lokaci.

A cewar ta, “ina fita a kullum yi aikatau  don na ciyar da iyali na a zamana na uwa domin bana son ‘yaya na ‘yan mata su dinga fita nemo mana abin da zamuci domin wasu mazan suna yin amfani da damar hakan don bata ‘yan mata.

Ta ce, “Duk lokacin dana

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!