Game Da Bikin Ranar ‘Yancin Manema Labarai Ta Duniya… — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RA'AYINMU

Game Da Bikin Ranar ‘Yancin Manema Labarai Ta Duniya…

Published

on


 

Ranar 3 ga watan Mayu, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin fadakarwa kan mahimmancin ‘yancin ayyukan manema labarai a duk duniya, ta yanda za a bar su, su gudanar da ayyukan na su, su kuma sauke nauyin sanar da al’umma halukan da ake ciki gami da tabbatar da bin diddigi ga ayyukan gwamnatoci ga al’ummun su.

Hakanan rana ce ta tunawa gwamnatocin nauyin da ya hau kansu na kiyaye ‘yancin fadin albarkacin baki kamar yadda yake a sashen na 19 na dokar kiyaye hakkin dan adam ta shekarar 1948. Wannan shekarar ita ce shekara ta 25 da fara gudanar da wannan bukin a duk fadin duniya. Sashen kula da ilimi da al’adu gami da kimiyya na Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) yakan gudanar da wannan bukin ne a duk shekara ta hanyar gayyato kwararru a sashen na yada labarai da kuma kungiyoyin kare hakkin ‘yan jaridun gami da sauran wasu hukumomi na Majalisar ta Dinkin Duniya domin su tattauna matsaloli da kuma hanyar shawo kansu.

A wannan shekarar, Hukumar ta UNESCO za ta jagoranci bukin cika shekaru 25 ne da fara bukukuwan a duk duniya. Ana sa ran daga cikin taken bukin akwai, Mahimman labarai a gidajen yada labarai, da kuma bayyanar da komai a fili a tsari irin na siyasa, ‘yancin kai ga sashen shari’a, da bin diddigin hukumomin gwamnati ga al’umma. Da kuma tattaunawa kan tabbatar da ‘yancin manema labaran a yanar gizo.

A duk duniya, masu mulki da masu dukiya suke jagorantar kisa da kuma illantar da manema labaran ta karkashin kasa, a duk sa’ilin da suka hangi suna neman tona masu asiri kan ayyukan su na cuwa-cuwa da sauran abubuwan da suke aikatawa wadanda ba su dace ba ga al’ummun su. A duk lokacin da aka kai ma manema labarai ire-iren wadannan farmakin, mawuyaci ne daga baya ka ga an kama tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban shari’a, wanda hakan shi ne daya daga cikin abin da ake ma ganin hadari babba ga ayyukan na manema labarai. Harin baya-bayan nan shi ne wanda aka kai kwanaki biyar da suka gabata a Kabul, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan ‘Yan Jaridu tara, baccin sauran da suka jikkata, wannan shi ne misalin irin hadurran da manema labaran kan shiga wajen gudanar da ayyukan na su, musamman a fagagen yakuka da kuma wuraren da ake rigingimu gami da kasashen da har yanzun ake gudanar da mulkin danniya.

A bara kadai, an kashe manema labarai har guda 81 a lokacin da suke kan bakin aikin su, baccin sama da 260 da suke tsare a gidajen yari, wannan a sakamakon binciken kungiyar ‘yan jaridu ta duniya, (IFJ) kenan. A Nijeriya, an kashe ‘yan jaridu biyu a bara. Su ne kuwa, Famous Giobaro, na gidan Rediyon Jihar Bayelsa, watau, Glory FM 97.1, wanda aka kashe ranar 16, ga watan Afrilu 2017, da Lawrence Okoji, na gidan talbijin tarayya da ke Benin, (Nigeria Telebision Authority (NTA), Benin). Wanda aka harbe shi har lahira sa’ilin da yake dawowa daga bakin aikin sa ranar 8 ga watan Yuli. Hakanan kuma, mutane 12 daga cikin manema labarai da kuma kungiyoyin sadarwa sun gamu da cin mutunci kala daban-daban musamman daga mahukunta a nan Nijeriya, kamar yadda cibiyar ‘yan jaridu ta, ‘International Press Centre (IPC), ta nu na.

A kasashe da yawa, mahukunta sukan kafa wasu dokokin tsuke bakin manema labaran, sai su yi amfani da hakan wajen tursasawa manema labaran, kan kar su fadi duk wani zalunci, cuwa-cuwa da bahalatsar da suka tabbatar mahukuntan na aikatawa. Kwanan nan a nan Nijeriya, al’umma sun mike tsaye suna kalubalantar dokar da gwamnati ta so kafawa ta hana fadin albarkacin baki, wacce gwamnati ta fake da cewa wai doka ce ta hana yin kalaman batunci, inda har dokar ta ce duk wanda aka kama da laifi zai iya fuskantar kisa kan yin magana kan wasu al’amurra masu hadari.

Sashe na 22 na tsarin mulkin 1999, ya bayyana ‘yancin ga ‘yan jaridu na gidajen Rediyo, Talabijin, Jaridu da Mujallu gami da dukkanin sassan yada labarai da su gudanar da ayyukan su, su ne kuma ke da alhakin bin diddigin ayyukan tafiyar da gwamnatoci domin bayyana su ga al’umma. Da haka ne, sashen na manema labarai ya zama tamkar wakili mai sanya ido kan ayyukan gwamnatoci kan kuma yadda suke tafiyar da ayyukan na su a bisa gaskiya da adalci. Su na kuma yin wannan aikin na su ne kamar yadda sura ta 4 sashe na 39 na tsarin mulkin ya ba su dama na ‘yancin fadin duk abin da suka shaida. Wannan aiki mai mahimmanci, ana kidanya shi a matsayin sashe na hudu na hukuma.

Duk da mashahurin mahimmancin wannan aikin, mafiya yawan ‘yan jaridu a Nijeriya su na gudanar da ayyukan na su ne a wani irin mawuyacin hali. Mafiya yawan lokuta su na aikin ne cikin haluka marasa dadi. da yawan su ma ba su da horon aikin da ya dace da aikin na su, ga tulin ayyuka ga ba albashi. Da yawan su sai su yi watanni ba tare da an biya su albashi ba. da yawan su ko sun ajiye aikin ba a biyan su kudaden Fenshon su. Da yawan su kuma ba su da inshoran lafiya da ta mutuwar su, duk da hadarin da ke cikin aikin na su. A lokacin da suke yi wa al’umma yakin neman ‘yancin su, su ba wanda ke nema ma su na su hakkin.

Ire-iren wadannan matsalolin ne suka dabaibaye ayyukan na su, ta yanda ma ba sa iya gudanar da ayyukan na su yadda ya dace. Amma dai duk da hakan su na bakin kokarin su wajen gudanar da ayyukan na su.

A yau da duniya ke gudanar da bukin ranar manema labarai, muna kira ga gwamnatoci da sauran mamallakan gidajen yada labaran gami da sauran masu kamfanonin yada labaran a duk duniya da su sauke hakkin manema labaran da ke kansu, su kuma kyautata ma su ta yanda za su sami damar gudanar da ayyukan na su kamar yadda tsarin mulki ya ayyana ma su.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!