Lebente Ta Taka Wa Barcelona Burki — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Lebente Ta Taka Wa Barcelona Burki

Published

on


Yunkurin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na kafa tarihin kammala wasanni a gasar La liga ba tare an doke ta ba ya gamu da cikas bayan da kungiyar Lebante  ta doke ta daci 5-4 a wasan da suka buga ranar Lahadi.

Tun da farko dai Lebante ta lallasa ta ne da ci 5-1 inda Emmanuel Boateng ya zura kwallaye uku yayin da Enis Bardhi ya zura kwallaye biyu.

Sai dai dan wasan Barcalona Philippe Coutinho ya zura kwallaye uku inda kuma Luis Suarez ya ci kwallo daya a bugun fenareti.

Barcelona dai ta buga wasanni 44 a gasar La Liga ba tare da an doke ta ba inda ta shafe tarihin da Real Sociedad ta kafa na buga wasanni 38 ba tare da an doke ta ba a kakar wasa ta 1979/80.

Sai dai duk da wannan rashin nasara kungiyar ta Barcelona ta lashe kofin na laliga inda ake saran za a bata kofin a mako mai zuwa idan kungiyar ta buga wasan tan a karshe da kungiyar Real Sociedad.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!