Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mummunan Hadarin Mota Ya Kashe Mutum Biyar A Ogun

Published

on

 

An samu bayanin mutum biyar sun mutu yayin da kuma wasu 14 suka samu raunuka a hadurra biyu, wadanda suka auku a wurare daban-daban a jihar Ogun  a makon da ya gabata.

Hadarin na farko ya auku ne a Alakara, Oke Odan akan hanyar Owode- Idiroko, wanda yayi sanadiyar mutwar mutane hudu.

Majiyarmu ta samo bayanan cewar hadarin ya shafi wata mota ce kirar Ford mai dauke da mutane 18 da kuma motar Cabster mai dauke da mutane biyu.

Direban mota Ford wadda take da namba KSF 01 DC  an ce yayi obatekin ne wanda bai kamata ba, kuma wurin da hanya ta juya.

Motocin dai sun yi taho mu gamu wato ita Ford da kuma Cabster wadda ke da namba LSD 491 DO wadda kan hanya daban.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda ta jihar Ogun mai kula da bin dokokin hanya Babatunde Akinbiyi, y ace, fasinjoji hudu sun mutu, da suka hacda da direba, yayin da kuma saurann fasinjan suka samu raunuka daban daban.

Ya ci gaba da bayanin cewar ‘’Wadanda suka mutu a hadarin kamar dai yadda jami’anmu da suka je wurin da aka yi hadarin, sun shaida mana mutum hudu ne, da suka hada da mata uku namiji daya.

‘’An kai gawarwakinsu babban asibitin Ilaro, a Karamar Hukumar Yewa ra kudu, wadanda kuma suka samu raunuka ana kulawa dasu a  asibiti, inda ake basu magunguna da sauran abubuwan da suka kamata.’’

Hadarin na biyu kamar yadda Akinbiyi ya bayyana ya faru ne a Olorunpodo akan hanyar Sagamu- Ijebu Ode zuwa Benin wannan kuma ya shafi mota kirar Hoda Cibic da kuma wata babbar mota.

Ita dai karamar motar tana da namba CW 23 ENU ita tana dauke da fasinjoji uku ne, zuwa wani wuri lokacin da babbar mota data taho da gudu ta buge ta, nan take ta kashe mutum daya wanda yake cikin motar.

Ya ce, direban babbar motr gudu yayi bayan da aka yi hadarin, su kuma sauranmutanen biyu da suka samu rainuka, an garzaya dasu asibitin kudi, a Olorunpodo saboda a kula da lafiyarsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: