Mun Kammala Shirin Kwace Bauchi Daga Hannun APC, Inji PDP — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Mun Kammala Shirin Kwace Bauchi Daga Hannun APC, Inji PDP

Published

on


 

A wani gagarumin taron da jam’iyyar adawa ta PDP ta yi a jihar Bauchi a ranar Asabar din nan da ta gabata, masu ruwa da tsakani na jam’iyyar sun hallara a jihar domin taya mataimakin shugaban jam’iyyar PDP Alhaji Babayo Garba Gamawa murnar samun mukamin mataimakin shugaban da ya yi.

Taron an shiryi na musamman ne domin yin walima hade da taya murnar, inda aka gudanar a farfajin Multipurpose da ke Bauchi; sai dai jiga-jigan jam’iyyar sun yi amfani da wajen taron wajen fara bayyana shirinsu na amsar mulki daga hannun gwamnatin APC mai ci a jihar, suna masu cewa jam’iyyar APC ta kaza kasau wajen kawo wa jama’an jihar Bauchi ci gaban a zo a gani, don haka ne PDP ta dawo da karfinta domin ceto jama’an jihar da kasa daga ukubar da APC ta jefa su a ciki.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bauchi Hamza Akuyam a cikin jawabinsa a wajen taro ya bayyana cewar basu ga wani kalulen da ke cikin kwace mulki daga hannun APC a jihar ba, domin kuwa wasu marasa kishin jihar suna neman lalata ci gaban jihar ta fuskacin rashin walwala, rashin aikin yi, tsadar rayuwa da sauransu wacce gwamnatin APC a jihar ta jefa jama’a a ciki.

A don haka ne ya bayyana cewar PDP tana nan a jihar Bauchi kuma sun kammala dukkanin wata shiri domin koma gidan gwamnati kamar yadda ya ce daman mulkin nasu ne kuma sune suka kware, yana mai bayanin cewar tuni suka yi zaman karatun ta nutsu suka gano matsalolin hade da gyarawa, wanda ya ce a 2019 PDP ce za ta mulki jihar Bauchi.

Ta bakinsa, “Mu a jihar Bauchi PDP a hade take, kanmu daya muke. Ina mai tabbatar wa shugaban PDP na kasa cewar a zaben 2019 PDP za ta kafa mulki a jihar Bauchi, saboda hadin kanmu, yawanmu, yarda da talakawa da suka yi da mu. Muna tabbatar wa shugaba cewa za mu kawo jihar Bauchi ta kowace hali,” In ji Akuyam

Hamza Akuyam ya ci gaba da cewa “Babu wata barazanar da ke gabanmu, za mu kawo jihar Bauchi,” A cewar shi.

A tasa fannin kuma, Abdul Ningi wanda shi ma dan takarar gwamna ne a jihar Bauchi cewa yake “Wannan ranar ita ce ranar karshe da za mu yi taro a cikin daki. Saboda haka wannan taron ya nuna wa shugabanin PDP irin dumbin magoya bayan da kuke da shi. Ina son na sanar wa kowa, mu ‘yan PDP kanmu a hade yake, Ni Abdul Ningi bana adawa da wani dan PDP. Ba zan yi gaba da dan PDP ba, ba kuma zan yi adawa da dan PDP, duk abun da ka fada wa dan jam’iyyarka wa kanka ka fada. Ya zama tilas mu hade mu tunkuri abun da ke gabanmu,”

“A kowace karamar hukuma sama da bus-bus dari sun zo wannan taron, don haka wannan na nuni ne da cewar PDP ta dawo da karfinta, wadanda suka tsaya suka jajirce har muka dawo wa PDP da martabarta, da akwai bukatar mu sanni mu kuma gano cewar ga inda muka nufa ga kuma inda za mu je,” In ji Abdul Ningi.

Abdul Ningi ya gargadi jami’an tsaro da su daina biye wa gwamnati mai ci tana amfani da su wajen cin mutuncin ‘ya’yan jam’iyyar PDP, yana mai cewa PDP tana bin dokokin kasa, amma abun da ake musu na wuce gona da irin.

Sauran ‘yan takarar gwamna a jihar karkashin jam’iyyar PDP Adamu Gumba da Alhaji Bala Muhammad Kauran Bauchi sun nuna jinjinarsa da kuma taya Baba Gamawa murnar samun wannan kujerar, suna masu addu’ar Allah bashi ikon yin abun da aka daura masa. Kaura da Gumba sun sha alwashin cewar sun fito ne domin jama’an Bauchi ba don kawukansu ba, don haka ne suka nemi jama’an jihar su zabesu.

Shi ma dai Malam Ibrahim Shekarau wanda dan takarar kujerar shugaban kasa a PDP ne cewa yaka yi, tilin jama’a ba zai haifar musu da komai ba, don haka dukkanin masoyin ga PDP ya hanzar neman mallakar katin zabe domin da hake ne kawai zai taimaki jam’iyyar idan lokacin zabe ya zo.

A ta bakin Shekarau, “Kuri’a a ranar zabe itace take tabbatar da cin zabe, kuma sai kowa ya tara daidai gabanin a ce an samu miliyoyin kuri’a, muna kira ga matasanmu da su tabbatar sun mallaki katin kuri’a. komai yawanmu idan yawan bai yi mana amfani a wajen zabe ba, to yawanmu bai yi amfani ba. Yanzu abun da ya dace idan kana son PDP shi ne ka fara mallakar katin zabe, haka kuma ka fadakar da sauran. Iyayenmu mata a cikin gida kuma ku bincika idan katinku ya bace ku sake nemowa domin fitowa a yi gangami a zabi PDP,”

“Mun tabbata idan an yi zaben na tsakani da Allah, PDP ita ce mai nasara a Nijeriya,” In ji shi.

Ibrahim Shekarau ya daura da cewa, “Daga dukkanin abubuwan da muka gani na tururuwar jama’a a jihar Bauch, alamu ya nuna mana PDP ta rigaya ta gama cin zabe a jihar Bauchi ma an gama. Abun da ya rage kawai shine ku baiwa jam’iyya hadin kai” kamar yadda ya shaida.

Da yake tasa jawabin, tsohon gwamnan Jigawa kuma mai neman kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Sule Lamido ya bayyana cewar Nijeriya ta shiga halin ha-ula-I a hannun Buhari, yana mai bayanin cewar gwamnatin APC ta gaza yin komai baya ga yunwa da kuma talauci hade da matsatsi da ta jefa jama’an kasar nan a ciki.

Ta bakin Sule Lamido, “Amma a yanzu an shiga wani yanayi, ‘yan dagaji marasa kishin Nijeriya sun hau mulki. Mulkin nan basu gudanar da komai sai karya. A 1984 an yi juyin mulki, Buhari ya hau mulki, yana zuwa abun da ya fara yi shine kama ‘yan siyasa da hukuntasu,”

Alhaji Sule Lamido ya kara da cewa, “Aiyukan ci gaba wa kasa kuwa an gagara yi. Yanzu ya sake dawo a yanzu, ya ce mu ‘yan PDP barayi ne, ya ce mu ‘yan PDP Boko Haram ne, ya ce mu ‘yan PDP ba mu da kirki, ya ce shekara 16 babu abun da muka yi. Kai yanzu wannan hall din da muke ciki suwa suka yi? Mafiya yawan aiyukan kasar nan PDP ta yi. Su wadanda suke mulki yanzu basu komai sai runto. Banda yunwa da talauci a fada mana abun da APC ta yi”

“Don haka ku farka PDP ta zo domin ceto kasar nan. Mulki PDP aiki, adalci, walwala, babu yunwa. Aka zo aka ce mune annoba a kasa, mumina ya zo ya hau, to a fada mana abun da muminin ya yi wa kasa baya ga yunwa da matsatsi da ya jefa kasar a ciki,” Kamar yadda ya shaida.

A jawabinsa na godiya, mataimakin shugaban PDP ta kasa, Garba Gamawa, wanda kuma aka shirya taron taya shi murnar, ya yi fatan Allah ya saka wa ‘yan uwa da abokan arziki da suka shirya taron taya shi murnar samun wannan kujerar day a yi.

Gamawa sai ya yi amfani da wannan damar wajen bayyana cewar PDP a yanzu ba PDP baya da jama’a suka sani ba ne, yana mai bayanin cewar yanzu haka sun dauki batun kama karya sun ajiye a gafe, yana mai bayanin cewar dukkanin wani dan takarar da jama’a suka nuna shi suke so la-shakka shine zai kasance dan takarar gwamna a jihar, don haka ne ya hori masu sha’awar tsayawa takarar gwamnan da su hada kansu waje guda domin samun gagarumar nasara a zaben da ke tafe.

Da yake tasa jawabin shugaban jam’iyyar ta kasa Prince Uche Secondus, ya bayyana cewar dukkanin alamun samun nasarar a zaben 2019 PDP ta gansu, domin APC ta kasa cika wa jama’an kasar alkawuran da ta dauka musu a lokacin yakin neman zabe.

Shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa na daya, ya bukaci dukkanin masu sha’awar tsayawa takara su gudanar yakin neman a tsaidasu bisa dokar jam’iyyar domin kauce wa yin wani abu da ka iya kawo baraka.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!