Yadda Bikin Yaye Daliban 8,496  Jami’ar ATBU Ya Gudana — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Bikin Yaye Daliban 8,496  Jami’ar ATBU Ya Gudana

Published

on


 

A shekaran jiya Asabar ne jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi (ATBU) ta yi gagarumar bikin yaye daliban su dubu 8,496 wadanda aka yaye a karo na 23,24 da kuma 25 na tsankon karatu na shekara uku, hade da mika musu shaidar kammala jami’ar.

Taron wanda ya gudan cikin jami’ar ya samu halartar manyan kuma jiga-jigai, shugabani, sarakuna, malamai, dalibai, wadanda aka yayen da dai sauransu.

A lokacin da ke jawabi a wajen yayen daliban, shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ilimi ginshiki ne na ci gaban kowace al’umma, yana mai bayanin cewar da ilimi ne kowace al’umma za ta samu gagarumar nasarar ci gaban da take da bukata.

Buhari wanda ya samu wakilcin  Daraktan kula da jami’o’i ta kasar nan Dakta Gidado Bello Komo ya bayyana cewar da bukatar gwamnatocin da suke fadin kasar sun su rungumi jahohin da suke jahohinsu hanu biyu-biyu, ya bayyana cewar yin hakan zai kawo ci gaba wa sashin ilimi matuka gaya.

Shugaban ya bayyana cewar jami’ar ta ATBU ta himmatu wajen kenkeshe hazikan dalibai a fannonin kimiyya da kuma kere-kere, yana mai bayananin cewar jami’ar ta yi zarra wajen kawo ci gaba a kasar nan ta Nijeriya, inda ya bayyana cewar tarihi ba zai taba mance da jami’ar ba.

Da yake bayar da shawara ga daliban da suke kan karatu a jami’ar a halin yanzu kuwa, shugaban kasar Buhari cewa yake yi, “Ina shawartarku da ku ci gaba da kire al’adunku da mutunta juna, hade kuma da nuna halin kwarai wa malamanku domin samun ilimi kwarai, dukkanin wani ilimin da aka samu ta hanyar ladabi, ilimin na samun albarka kuma ana samun natija sosai a kansa,” In ji Shugaban kasa.

Haka kuma bai tsaya nan ba, ya kuma hori daliban da suka samu nasarar kammala jami’ar a wannan lokacin da cewar su fa sani yanzu ne kasa ke bukatar gudunmawarsu domin daukaka darajar Nijeriya zuwa mataki na gaba “Yanzu an yaye kuma, an sallameku za ku shiga cikin al’umma domin gudanar da rayuwa, na sani kun samu nagartaccen ilimi a wannan jami’ar, to ina kiranku da ku dauki wannan ilimin da kuka samu ku yi aiki da shi a cikin al’umma domin ci gabantar da kasar nan,” In ji Rufus.

Buharin ya kuma kirayi dukkanin jami’o’in da suke Nijeriya da suke zakulo hazikan daliban da suka yi zarra domin kasar ta amfana da su a fannonin kimiyya da kuma kere-kere, yana mai bayanin cewar fitar da masu basiri a wannan fannin zai taimaka wa kasar wajen samun ci gaban da ake bukata a halin yanzu, domin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.

Shugaban ya kuma yi amfani da wannan damar wajen nuna jinjinarsa da yabonsa wa hukumar gudanarwa ta jami’ar da kuma shugabanin jami’ar hade da sauran malaman jami’ar a bisa kyakkyawar sakamako da suke samar wa jami’ar ta hanyar yin aikinsu tsakani da Allah wanda hakan ya sanya jami’ar ta yi zarra a cikin kasar nan.

Shugaba Buhari ya kuma nemi dukkanin daliban da aka yayen da su da rungumi halaye na kwarai wajen tsayuwa domin yin aiki don gina kasa, yana mai bayanin cewar kowani dan kasa na da gudunmawar da zai iya bayarwa domin ci gaban kasar nan.

Shugaba Buhari ya taya su murna hade da kuma yi musu fatan dacewa a rayuwarsu ta gaba bayan kammala jami’ar.

Da yake jawabinsa, uba ga jami’ar wato shugaban jami’ar ta ATBU Oba (Dakata) Rufus Adeyemo Adejugbe Aladesanmi wanda kuma shine Sarkin Ado-Ekiti ya yaba kwarai da irin kokarin gwamnatin tarayya wajen tallafa wa jami’o’in da suke kasar nan a halin yanzu duk da matsatsin tattalin arziki da ake ciki.

Ya bayyana cewar wannan yayen karo na biyu kenan tun bayan da aka nadasa a matsayin shugaban jami’ar, yana mai bayanin cewar a shekara ta 2016 ne aka karramasa da lambar yabo ta Dakta wanda ya yi alkawarin zage damtse domin ci gaban jami’ar, yana mai bayanin cewar tun daga wannan lokacin kuma yake bayar da tasa gudunmawar.

Ya yi amfani da wannan damar wajen taya sabbin hukumar gudanarwa na jami’ar, yana mai nemansu da su ci gaba da aiki kafada-kafada domin fitar da sakamako mai kyau a kowani lokaci.

Shugaban ya yi godiya wa daliban da suka kammala jami’ar a bisa nuna halin dattako har zuwa ga kammala karatunsu tun daga farawa.

Shugaban hukuma gudanarwa ta jami’ar ATBU Ambasada Dakta Nimota N. Akanbi ta fara ne da yin tilawa kan sunan wanda aka sanya wa jami’ar wato Abubakar Tafawa Balewa, inda ta bukaci sauran jama’a da su yi koyi da halinsa wajen nuna wa jami’ar kauna, amana, gaskiya domin ci gaban kasar nan.

Dakta Nimota ta bayyana cewar tun bayan lokacin da aka nadata wannan kujerar, suna samun kyakkyawar fahinmta a tsakanin hukumar gudanarwa da kuma hukumar makarantar wacce a cewarta wannan kyakkyawar dangantakar ta iya haifar da gagarumin ci gaba wa jami’ar, jihar Bauchi da ma kasa baki daya.

Ta kuma yi amfani da damar wajen yin kira ga iyayen daliban da suka samu nasarar kammala jami’ar da cewar sun kuma himmatu wajen tabbatar da cewar ‘ya’yan nasu sun yi amfani da ababen da suka koya ba kawai domin amfanar kawuka ba, har ma da amfanar kasa baki daya, ta kuma yaba musu a bisa tsayuwar daka da suka yi har ‘ya’yan nasu suka samu nasarar kammala jami’ar a wannan lokacin.

Tun da fari a tasa jawabin, Mukaddashin shugaban jami’ar ta Abubakar Tafawa Balewa Farfesa Saminu Abdulrahman Ibrahim ya bayyana cewar  a wannan karon sun yaye dalibai da ya yawansu ya kai dubu 8,496 a zangon karatu karo na 23, 24 da kuma 25, wato yayen daliban na shekara ta 2015, 2016 da kuma shekara ta 2017 ne aka samu wannan adadin.

Ya bayyana cewar sun hada yayen na karo uku a waje guda wanda suka gudanar a wannan lokacin.

Saminu ya ci gaba da bayyana cewar daga cikin dalibai 8,496 da suka yaye, 480 sun kammala karatun Diploma ne, inda kuma adadin daliba mafi yawa na 5,637 ne suka samu shaidar kammala digiri a wannan shekaru uku, ya kuma ci gaba da bayyana cewar dalibai 1,518 suka kammala PGD, inda kuma adadin dalibai har 770 suka samu yin digiri na biyu, inda kuma 90 suka samu shaidar kammala jami’ar ta matakin karatu na Digirin-Digirgir.

Farfesa Saminu ya ci gaba da cewa, adadin dalibai 118 da suka kammala sun samu nasarar fita da lamba ta daya (first class), 1,618 su kuma suka fita da sakamako na biyu, inda kuma 2,609 suka fita da sakamako ta biyu amma marar dara, haka kuma 1,231 daga cikin daliban da aka yayen sun fita ne da sakamako ta uku, sai kuma wadanda suka fita daker masu cire wando ta ka wato basu tabukata kokari ba su ne kacal 61.

Mukaddashi shugaban jami’ar ya taya dukkanin daliban da suka yayen murna kammala jami’ar a karo na 23, 24 da kuma karo na 25, yana mai horonsu da kada su ji dadin jami’ar su mance da irin gudunmawar da ta basu a rayuwarsu, yana mai nemansu da su ci gaba da kawo wa jami’ar dauki a matsayinsu na tsoffin dalibai domin kai jami’ar mataki na gaba.

Farfesan ya yaba wa gwamnatin jihar Bauchi a bisa ginin titin da ta yi musu, yana mai bayanin wasu daga cikin nasarorin da ya iya cimmawa a cikin jami’ar kawo kama aikinsa a matsayin mukaddashin shugaba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai