Connect with us

LABARAI

’Yan Bindiga Sun Kashe Dan Kasuwa Don Ya Ki Sayar Musu Da Sigari

Published

on

 

Wasu ‘yan bindiga da suka kai biyar sun kashe wani dan tireda saboda ya ki ya sayar masu da fatikin sigari, anfi sanin shi da suna MM.

Majiyar labarin tamu ta bayyana cewar ranar Talata ce aka harbi dan tiredar bisa kan shi, a bakin shagon shi a Gaa Akanbi cikin Ilori jihar Kwara, daya daga cikin ‘yan bindigar wanda ake ganin ban kungiyar asiri ne shi yayi harbin.

Su dai’yan bindifar sun je shagon shi da niyyar su sayi sigari, sais hi MM ya fada masu cewar baya da sigari, duk kuwa da yake wani dafa cikinsu ya nuna mashi  fakitin sigarin,

Dan tiredar ya shaida masu cewar ajwai wani mutumin daya sayi fakitin sigarin

‘’Yan kungiyar asirin hankalinsu ya riga ya tashi, lokacin da ya fada masu cewar wani ya sayi sigarin, yana kuma kan hanyar shi ya karba.

‘’Daya daga cikinsu ya fito da bindigarshi ya harbi shi MM aka  kamar dai yadda majiyar ta bayyana.Lokacin da shi MM yake ta kakarin mutuwa ne suka shiga shagon suka dauki fakitin sigarin, suka ranta a na kare.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda ta jihar Kwara Mr Ajayi Akasanmi ya tabbatar da kisan, ya kuma kara da cewar ‘’Na ji labarin cewar an kashe wani mutum, a Gaa- Akanbi, amma har yanzu muna binciken akan al’amarin’’.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: