Connect with us

SIYASA

2019: Gwamnan Bauchi Ya Nemi Matan Kiristoci Da Su Zabi Shugabani Nagari

Published

on

 

Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya yi kira ga matan Kirista da su maida hankula wajen zaben ‘yan siyasar da suka taba yi musu wani aikin ci gaba, haDe kuma da zaban waDanda suka cancanta domin ci gabantan rayuwa.

Gwamnan ya bayar da wannan shawarar ce a lokacin da ke gabatar da wata maKala a wani taron da Kungiyar matan majami’ar cocin RCC suka gayya ce shi.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Kwamishiniya a ma’aikatar tsaftar muhalli ta jihar, Rifkatu Samsun Dana, gwamnan Abubakar ya kuma jawo hankalin matan kiristocin da su yi rijistan katin zabe wanda zai basu zarafin zaban wanda suke so a zaben da ke tafe na 2019.

Yana mai bayanin cewar zabe wata hanya ce ta samar wa kowani Dan Kasa amsar haKKinsa daga hanun shugabanin, yana mai nemansu da su yi KoKarin zaben waDanda suka tabbatar za su kawo wa rayukansu ci gaba mai ma’ana.

Muhammad ya kuma yaba kwarai a bisa zaman lafiyar da ake samu a tsakanin kiristoci da sauran addinan da suke jihar Bauchi.

Tun da fari shugaban cocin RCC da ke Bauchi Rabran Lawi wa gwamnan jihar Bauchi a bisa naDa wani mambansu a cikin makusantansa, wanda a cewarsa hakan zai ci gaba da kawo ci gaban zaman lafiya a jihar.

 

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: