Connect with us

LABARAI

An Gudanar Da Zaben Shugabannin Jam’iyyar APC ‘Kwankwasiyya’ A Karamar Hukumar Dala

Published

on

 

A jiya Litinin 14ga watan Mayu, 2018 ne aka gudanar da zaben jam’iyyar APC ‘Congress’ Kwankwasiyya a Karamar hukumar Dala.

An yi zaben a jiya ne sakamakon rashin da aka yi na Khadimul Kur’an, Khalifa Isyaka Rabiu. Wannan shi ne dalilin rashin yin gagarumin taron a ranar Asabar kamar yadda Uwar Jam’iyya ta Kasa ta umarta.

An yi zaben shugabancin jam’iyyar ne a gaban shugaban dattawa na Karamar hukumar ta Dala Alhaji Dayyabu Maiturare da Sakatarensa Honorabul Lawan Hussaini da kuma shugaban Kwankwasiyya na Kano Honorabul Barista Aminu Dala.

An sami maslaha da goyon bayan dubban ’Yan Kwankwasiyya na Karamar Hukumar Dala, a Inda aka samar da shugabanci kamar haka; Honorabul Kabiru Falaki a matsayin Shugaba (Chairman), sai Honorabul Usaini Agency a matsayin Mataimakin Shugaba (Assistant Chairman).

Honorabul Lawan Miko a ne ya lashe gurbin Sakatare (Secretary); sai Honorabul Abu Atiku Abba a matsayin Ma’aji (Treasurer), sannan Honorabul Nura Ayagi a matsayin mai bin diddigin kuDaDe ‘Auditor’

A Daya bangaren kuma Honorabul Hajiya Umma Kofar Ruwa ita ce ta zama Shugabar Mata (Woman Leader), sai Honorabul Auwalu AbdulKadir a matsayin mai bin diddigin kuDaDe na biyu (Auditor 2). Shi kuma Honorabul Labaran Shamba a matsayin ‘EDCO’ tare da Honorabul Garba Yakubu a matsayin Lauya (Legal Adbiser).

An yi wannan zaben da na sauran shugabanni ne kamar yadda uwar jam’iyyar APC ta Kasa ta umurta. Kowanne mutum a cikin waDannan shugabanni sai da ya cike fom Dinsa kamar yadda yake a doka daga uwar jam’iyyar ta

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: