Connect with us

LABARAI

Bankin Union Ya Ayyana Samun Ribar Naira Biliyan 5.3

Published

on

 

Rahoton yawan kuDaDen da aka samu a tare da wanda aka bincika na watanni uku na farkon shekara  2017 sun nuna cewar, an samu ci gaba duk kuwa da yake ba a bayyana ko nawa ne duk mai hannun jarin Bankin zai samu ba.

Bankin daiya bayyana cewar ya samu riba bayan an cire haraji na Naira bilyan 5.3 daga Naira bilytan 4.5, a irin shi lokacin na 2017 wannan ya nuna ke nan an samu Karin kashi 17 cikin Dari.

Riba kafin cire haraji ya tsaya Naira bilyan 5.4 daga Naira bilyan 4.7 abinda aka samu a watanni ukun farko na shekarar 2017, wannan kuma ya nuna an samu Karin kashi 16 cikin Dari.

Rahoton watanni uku ya nuna cewar an samu Naira bilyan 39.5, a watanni uku na 2018, idan aka gwada Naira bilyan 34.3 a farkon watanni uku na shekarar 2017.

Emeka Emuwa shine babban jami’in Bankin ya bayyana cewar bayanan watanni uku na farko abin ya nuna, wasu sababbin tsare tsare da shi Bankin ya Dauka, na yadda zai cimma burinsa, wajen samun ci gaba  musamman ta bangaren amfani da fasahar Dan Adam, don gano bakin tsaren.

‘’Duk da yake dain bamu daDe da faraway ba, amma kuma da akwai alamun cewar za a cimma manufa, idan aka yi la’akari da yadda abubu suka fara tafiya.’’

Ya Kara da cewar shi ci gaban da aka fara samu cikin KanKanen lokaci ya fara ne daga kashi 7.1 na cikin  kashi Dari zuwa kashi 8.7 cikin kashi Dari.

Mr Emuwa ya Kara jaddada cewar ita Karuwar cin ribar da aka samu ta kashi 18 na kuDin da babu ruwa,  abin ya kasance ne saboda, Karuwar kuDaDen  shigar da ake samu ta hanyar kasuwanci da kuma wasu harkoki na Bankuna, hakan ya bada gudunmawar da al’amuran suka kasance haka.

Yayin da kuma kuDin shigar da ake samu ta hanyar ruwa wato interest, abin ya Karu da kashi 14 aka samu Naira bilyan 31.7, a watanni ukun farko na shekarar 2018, idan kak gwada da Naira bilyan 27.7 na watanni ukun farko na 2017.

‘’Hakanan ma ribar da aka samu ta kuDin ruwa an samu Karuwar kashi 22 cikin kashi Dari na ko kuma Naira bilyan 17.8, idan aka gwada da Naira bilyan 14.6 a shekarar 2017, wanda hakan ya nuna ke nan, an samu Karuwar Naira bilyan 14.6 a shekarar 2017, watoan samu Karuwarb kashi 14 cikin kashi Dari, na ribar kuDin da ake samu ta ruwa, abin kuma ya yi Kasa,inda aka samu Karuwa kashi 6 cikin kashi Dari na ribar da aka samu na Karuwar kuDaDen da aka kashe daga cikin waDanda aka samu ta kuDin ruwa.

Akwai kuma Karin ci gaban da aka samu na kashi 18 cikin kashi Dari na daga Naira bilyan 6.6 zuwa Naira bilyan 7.8.

Da aka yi nazarin na  rahoton yadda tsarin kubaben Bankin yake na shekarar da ta Kare ranar 31 ga watan Disamba, abin ya nuna, cewar an samu Karuwar kashi 25 cikin kashi 100, zuwa Naira bilyan 168.8 daga Naira bilyan 126.6 na shekarar 2016.

Riba kafin a fitar da kuDaDen haraji abin ya tsaya akan Naira bilyan 15.5 a shekara 2017, idan aka haDa da Naira bilyan 15.7 na shekarar 2016.

Bugu da Kari Mr Emuwa ya nuna cewar ta hanyar bashi maabin an samu ci gaba da Naira bilyan 14.9 zuwa watan Maris na 2018 daga kashi 19.8 a farkon shekarar.ta 2018.

Ya Kara bayyana cewar Bankin ya ci gaba da tsayar da hankalin shi akan basussukan da ya bada, yana kuma sa ran Kara samun wani ci gaban, wanda kuma ke sa ran , Kara samun ci gaban da yafi na farko.

Bankin yana Kara Kaimi ta bangaren yadda karbo basussukan da ya bayar, abinda ya haDa da hanyar lalama ko kuma  atafi kotu, inda ya kasance dole.

‘’A farkon watanni shida na wannan shekarar zamu ci gaba da bullo wasu sababbin dabaru waDanda zasu bada gudunmawa ta  bangaren al’ummarmu yadda abin ko wanne sashe zai shaida an yi da shi ko kuma tafiya tare da shi.

‘’Hakanan ma ta bangaren fasaha da kuma fasahar zamani duk za ayi amfani dasu saboda  asamu damar cimma burin gamsar da abokan hulDarmu’’.

Shi ma babban jami’in harkar kuDi na Bankin Oyinkan Adewale ya bayyana cewar sakamakon watanni ukun farkon shekara, abin ya nuna amincewa da a fara amfani da wata hanyar  bada bayanai da suka shafi kuDaDe ta Kasa Kasa, ko kuma International Financial Reporting Standard, da aka fara amfani da ita a farkon wannan shekarar.

‘’Har yanzun dai muna nan akan (CAR) mizanin da ake amfani da shin a kashi 17.9 duk kuwa da yake akwai yadda IFRS 9 tayi matuKar tasiri akanmu.

‘’Sai kuma al’amarin da ya shafi dukiyar bankin wato kuDaDen shi da kuma basussukan da suke hannun mutane da kuma kamfanoni, abin ya tsaya akan yadda doka ta tanada, sai kuma al’amarin da ya shafi ruwan nkuDaDen shi Bankin, abin an samu ci gaba daga kashi 8.73  cikin kashi 100, na watanni ukun farko na shekarar 2018, daga inda aka tsaya na kashi 7.

Ta ce duk da yake kashi 19 cikin kashi 100 da kuma kashi 27 Karuwar yadda Hukumomin da suke kulawa Kaddarorin Bankin da kuma ta kula da kuDaDen jama’a da suke Bankuna,  yadda shi Bankin yake gabatar da hulDar shi, abin ya Karu da kashi 10 cikin kashi 100, wannan kuma kuma ya nuna yadda su shugabannin suka tsaya sai komai sun tafi yadda ya dace.

‘’Za kuma mu ci gaba yin al’amuranmu kamar yadda aka far, ko ma ya wuce yadda aka faro Diun wanda duk dama abin aka fiso ke nen’’.

 
Up Next

An Gurfanar Da Shaikh Zakzaky Kotu A Kaduna

Don't Miss

Hisba Ta Kai Samame Unguwar Danbare Da Dakatsalle A Kano Daga Na’ima Abubakar, Kan Rundunar Hisba ta Jihar Kano a KoKarin da ta ke na umarni da aikin alhairi da hani da mummuna aiki, ta kai wani samame unguwar Danbare dake Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, Jami’in da ya jagoranci tawagar da takai samamen Malam Sani Zailani ya bayyana cewa an samu nasarar damKe samari da ‘yan mata waDanda ke gudanar da harkokin baDala, Shaye Shaye da kuma masu yawon ta zubar a Unguwar Danbare. Alokacin Samamen rundunar ta Hisba tayi nasarar cika hannu da waDanca matasan da aka yi ittifaKin cewa suna wannan baKar ta’ada ne ba tare da sahalewar iyayensu ba, Hukumar wadda kullum aikinta shi ne ganin al’umma ta tsarkaka daga munanan ayyukan da ake fatan ganin an samu ingantacciyar al’umma. Haka zalika Rununduna ta Hisba ta sake kai irin wannan samame garin Dakatsalle dake Karamar Hukumar Bebeji inda anan ma hukumar tayi sa’ar damKe wasu masu yawon tazubar wandaacikinsu har akwai waDan ke Dauke da ciki, da aka tambayi mai Dauke da cikin ko ina waDanda yayi mata cikin sai tace ya gudu ya barta, amma dai da yawa na nuna cewa suna sana’ar sayar da abinci ne. Darakta Hukumar Hisbarna Jihar Kano Malam Abba Sa’idi Sufi da yake Karin haske kan wannan samame da hukumar takai y atabbatarwa da wakiliyarmu cewa wannan na cikin ayyukan Hukumar Hisba, saboda haka ya bayyana cewa za’a tantance waDanda wannan shi ne kamun farko da aka yi masu, inda za’a yi masu wa’azi tare da yin nasiha garesu, sauran kuma masu kunnen Kashi bayan kammala bincike za’a gurfanar dasu gaban kulliya domin girbar abinda suka shuka. A tattaunawar da aka gudanar da wasu waDanda aka kama sun bayyana nadamar su tare da roKon yi masu afuwa bisa alKawarin cewa ba zasu sake aikata irin wannan laifi ba

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: