Connect with us

LABARAI

Cikin Shekaru Biyu Nijeriya Ta Sami Zuba Jarin Dala Bilyan 24.1

Published

on

 

 

Babbar Sakatariyan hukumar bunKasa zuba jari ta Kasa, NIPC, Yewande Sadiku, ta ce, Nijeriya ta sami zuba jarin da ya kai dala Bilyan 24.1 daga waje a cikin shekaru biyu baya.

Malama Sidiku, ta bayyana hakan ne wajen wani taron manema labarai a Abuja, ranar Alhamis.

A cewar ta, babban aikin hukumar na ta shi ne ta bunKasa da janyo hankalin masu zuba jari a Kasarnan daga waje.

“Jarin da aka zuba a Kasarnan daga waje a shekarar 2016 ya kai dala bilyan 5.4, a shekarar 2017 kuwa an zuba jarin dala bilyan 12.5 daga wajen Kasarnan.

“A farkon zangon shekarar 2018, an zuba jarin dala bilyan 6.3 wanda hakan ya ma fi duk jarin da aka zuba a shekarar 2016, da kuma na zango na uku na shekarar 2017,” in ji ta.

Sidiku ta ce, “Mu na da cibiya musamman mai bayar da bayanan halin da tattalin arzikin na Nijeriya yake, da yanayin halin zuba jarin, da kuma dukkanin tsare-tsaren da suka shafi hakan gami ma da dukkanin bayanan sassan zuba jarin.

“Duk mun yi hakan domin kwaDaitar da masu sha’awan zuba jarin na su. A cewar ta kuma akwai bukatar Jihohi su ma su yi abin da zai janyo hankulan ma su zuba jarin.

Babbar Sakatariyar ta ce, hukumar na ta tana yin aiki tare da gwamnatocin Jihohi domin inganta hakan, ta ce, hukumar za ta iya kaiwa ga gaci ko ba tare da gwamnatocin Jihohin ba.

Ta ce, hukumar ta na shirin kafa wata cibiya a yanar gizo da za ta tattara bayanan duk wurare masu laushi a Jihohi da za su nu na wa masu sha’awa hanyoyin zuba jarin a cikin su.

A cewar ta, Nijeriya ta na da wurare masu yawa a zube da masu zuba jarin za su ci gajiyar su, manyan su ne kamar sassan Noma, Lantarki, Kere-Kere, albarkatun Kasa, manyan ayyuka da abin da ya shafi sana’anta bola.

Sidiku ta ce, hukumar na ta za ta gina tashar samar da bayanai a yanar gizo ta yadda daga ko’ina mutum zai iya duba sassan zuba jarin da ke cikin Kasarnan.

A nan sai ta ce, hukumar na ta za ta shirya wani taron faDakarwa, daga ranar 21 zuwa 23 na watan Mayu, domin ta janyo hankulan masu zuba jari a sassan Noma, Zirga-zirga, Lantarki, Iskar Gas, Kere-Kere, Sadarwa da Kimiyya da fasaha.

“ A wajen za a tattauna kan bukatar zuba jaruka da kuma manufar da za a cimmawa ba tare da sai mai son zuba jarin ya yi tattaki zuwa ko’ina a cikin Nijeriya domin ya duba ayyukan ba.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: