Connect with us

RAHOTANNI

Ganduje Ya Gina Ofisoshin ’Yan Sanda Kan Naira Milyan 400 Don Magance Matsalar Tsaro

Published

on

 

Gwamnatin Jihar Kano za ta kashe kimanin Naira milyan 400 domin gina sabbin ofisoshin ‘yan sanda a duk faDin Jihar, in ji Gwamnan Jihar, Abdullahi  Ganduje.

Gwamna Ganduje, ya bayyana hakan ne jiya sa’ilin da yake kafa harsashin gina ofishin kwamandan shiyya da ke kan hanyar, ‘Court road’ a Tarauni.

Ganduje ya ce, ayyukan da gwamnatin za ta yi sun haDa da gina ofisoshin kwamandojin shiyya guda biyu a kan wannan titin a Kananan hukumomi biyu ta Tarauni da Tudun Wada, kan kuDi Naira milyan, N123, 364, 230, da kuma ofishin ‘yan sanda a Panshekara, da ke Karamar hukumar Kumbotso, kan kuDi Naira milyan, N59, 589, 240, sai kuma wasu ofisoshin ‘yan sandan guda biyu a Rijiyar Zaki da kuma Zango, duk a Karamar hukumar Ungoggo, kan Naira milyan, N 101,841, 438. 50.

Ya ce sauran sun haDa da, ofishin kashe gobara a Anguwan Dakata, da ke Karamar hukumar Ungoggo, kan Naira milyan, N71, 626, 643. 58.

Hakanan, gwamnatin ta bayar da ginin wani ofishin ‘yan sandan a garin Ganduje da ke Karamar hukumar Tofa, gami da gina gidajen kwanan ‘yan sanda a cikin garin na Kano.

Bikin kafa harsashin ginin ya sami halartar Shugaban ‘yan sanda na Kasa, Mista Ibrahim K. Idris, gwamnan ya ce, su na yin wannan aikin ne domin kare dukiyoyi da rayukan al’umma.

“A ‘yan watannin baya, mun baiwa hukumar ta ‘yan sanda da ke nan Kano sabbin motoci da kayan aiki domin taimaka masu fuskantar Kalubalen tsaron da ke fuskan tar mu a wannan Jiha.

A na shi jawabin, Shugaban ‘yan sanda, Ibrahim K. Idris, ya nu na farin cikin sa da yadda gwamnatin Jihar ta Kano ke Karfafa ma rundunar ‘yan sanda, ya yi nu ni da cewa a kwanakin baya ma ya zo Kano domin ya buDe wasu ayyukan da gwamnatin Jihar ta yi masu.

“Kano ta bayar da misali ga sauran Jihohi su yi koyi da ita wajen agaza wa rundunar ‘yan sandan,” in ji shugaban ‘yan sandan, ya Kara da cewa, ‘yan sandan ba za su yi Kasa a gwiwa ba wajen maganin duk wata barazana ta tsaro a duk Kasarnan.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: